Kannywood

Hukumar tace fina finai ta dakatar da daukar ko wane irin fim a jihar kano – Abba elmustapha

Hukumar tace fina finai da dab’i ta jihar Kano ta bada umarnin dakatar da daukar ko wane irin fim a fadin jihar.

Shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne ya tabbatarwa da Kanawa Radio hakan, inda yace hukumar ta dauki matakin hakan ne domin bawa duk kanin ya’yan masana’antar damar zuwa su sabunta rijistar su.

” Taro ne munka tashi hadakar kungiyoyin mu moppan arewa film makers da kuma dattawan masana’atar
cikinmu mai albarka ta Kannywood wadda munka kai ga yarjejeniyar cewa kwanankin baya anji ko mun dakatar da lasisi da duk wani stateholder suke da shi to yanzu har munkai matsaya shirye shiryen mu sunyi nisa to yanzu mun kusa fara sabanta rigista na kowa ɓangarori to a yau mun tattauna da su da cewa duk wani aiki da yake faruwa a cikin kannywood har kasuwa sun tsaya chak har zuwa sati biyu.

“Wannan shine ya bada damar kowa yazo ya sabanta nashi lasisi ko rigista sa ko sabo domin yabi matakan domin shima ya zamo dan kungiya wanda anka yadda yazo yayi wannan sana’a duk ɓangarori.

Wannan bangarori kaga daga yanzu daukar fim “shortin fim” sun “musica’ studio” gidajen wakoki da masu editin “art and editors” da masu downloading a kasuwa da masu maganin gargajiya da masu harka kida “D’js” kenan da kuma “cafe business centre” da masu daukar hoto da wankewa “photo labs” dukkansu suna cikin wannan tsari na sati biyu a tsaya chak.

Kowa zai zo ya sabunta lasisinsa ya cigaba da sana’a sa a cikin tsari aminci da shari da kuma bin doka da oda da kuma inda ake kallace kallace “views center” kenan muna da inda ake kallon kwallo duk zasu zo suyi rigista domin mun bada nan da sati biyu duk wanda baiyi ba yasani sana’a sa na cikin barazana zamu iya kulle shi”.inji abba elmustapha.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button