Sunday, 24 March 2019

Ya Datse Dan Yatsan Da Dangwalawa Buhari Kuri'a Dashi

Ya Datse Dan Yatsan Da Dangwalawa Buhari Kuri'a Dashi


Daga Jamilu Daya-malam Gama

wani bawan Allah da yasa gatari ya guntule babban dan yatsan sa na hannun dama, wanda yayi amfani dashi wajen zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

kuma wai har yana kiran mutane da su ma su datse nasu!
Labari Daga Sada bin suleiman usman.


Na Yi Kuskure Da Na Shiga Siyasa, Yanzu Na Tuba - Adam A Zango

Na Yi Kuskure Da Na Shiga Siyasa, Yanzu Na Tuba - Adam A Zango

 


Adam Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa, ya tuba daga shiga harkokin siyasa, domin ba karamin kuskure ya yi ba da ya shiga cikinta. Jarumin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga Maris, 2019, ta Instagram dinsa, inda ya ce, “shiga harkar siyasa a wurina ba karamin kuskure ba ne, sabosa hakan ya janyo wasu masoyan nawa sun zama makiyana. Don haka Ina so in yi amfani da wannan lokaci na bai wa duk wadanda na bata wa rai hakuri. “Daga yanzu kuma zan mayar da hankalina kan sana’ata. Zan cigaba da kawo mu ku finafinai da wakoki masu kayatarwa. Ina son ku masoyana, don idan babu ku, ni ma babu ni.” Jarumin dai ya yi wannan sanarwa ne jim kadan bayan da sakamakon zaben cike gurbi na jihar Kano ke nuni da cewa, dan takarar da bai yi wa yakin neman zabe ba, wato Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC, shi ne a kan gaba. 

Gabanin fara zaben dai jarumin ya bayyana a wani hoton bidiyo ya na murna tamkar dan takararsa na PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, zai lashe zaben, to amma sai labari ya nuna alamun shan bamban. Haka nan dan takararsa na kujerar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na PDP, shi ma ya sha kayi a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na APC kafin gudanar da zaben gwamnoni. Adam Zango dai jarumi wanda ya saba fitowa ya ce ya bar wani abu da ya ke kan yi, inda hatta shi kansa fitowa a finafinai ya kan ce ya daina a wasu lokutan baya, ballantana kuma ita siyasar kasa. 


 
NaƘi Auruwa - Zainab Indomie

NaƘi Auruwa - Zainab IndomieSharar Fage
Cikin Muryar takaici ta dube ni, duba me son samun mafita tace, “Kawata meye mafita?, aure nake so wurjan Jan kamar na kai kaina dakin miji wallahi, kowa ya zo rimi rimi kwana kadan sai ya gudu, Abin ya ishe ni “,Kawata Zarah tayi shiru daidai inda ta fashe da kuka cikin tashin hankali. Na bi ta da kallo cikin tausayi ,ya yin da na shiga tunano irin rayuwar da muka yi da Zarah tun daga kuruciya har girman mu ,a inda yanzu ni ina cikin shekara ta Bakwai da aure, yayin da Zarah ke zaune a matsayin Budurwa har yanzu. Tsugunawa nayi daidai kafar zarah, na dafa kafadun ta, cikin yanayin Rarrashi na fara yi wa Zarah magana cikin sanyin murya nace, “Kiyi hakuri Zarah, komai yana da wa’adi a rayuwa, aure lokaci ne, sanin kan ki ne baki da wata makusar halitta da za’a ce an gaza auren ki, sannan kina da ilmi, Asali da kyak….. “ “Dakata “,a fusace Zarah ta dakatar da ni, wanda har sai dana tsorata. Ta cigaba da cewa, “Tabbas ina da kyau, Asali, Nasaba, Ilmi, amma sanin kan ki ne cewa Kubra duk wannan abubuwan dana mallaka shirme ne domin nayi asarar Babban abinda ya dace na mallaka, wato tarbiyya.” Ta yi shiru daidai inda ta sake fashewa da Kuka mai dauke da Gumjin takaici da Danasani. A wannan lokacin kasa cewa komai nayi, jikina yayi sanyi kwarai, sannan kuma na shiga tunanin irin zaman da muka sha yi da Zarah akan dacewa da yayi ta gyara tarbiyyar ta yadda ya kamata sabanin yadda take rayuwa kara zube babu tsari. Ginshiki Tabbas haka ne cikin rayuwa komai yana da lokacin sa, yayin da komai yana wanzuwa ne cikin tsarin Allah subahanahu wata’ala.Hakika Aure na da lokaci tabbas, amma duk da haka akwai wasu abubuwa da mata ya kamata su dinga dubawa kafin furta cewa sun ki auruwa, ko Mazan da suke son nasu sun ki fitowa su aure su, duk kuwa da soyayyar da ke wanzuwa a junan su.Akwai wani abu da Mata ya dace lallai su dinga lura da shi kafin koka cewa namiji ya ki auran su, ko bayan duk doguwar soyayyar da suka yi ya gudu ya auri wata.,Abin kuwa shine…. *Yaya Ku Ka Hadu Ko A Ina Ku Ka Hadu Da Shi Kansa Namijin? Abin nufi anan a ina kuka hadu da mutum, ma’ana waje ne nagartacce ko wajen Banza?, sannan kuma kuma a cikin wanne yanayi ya gan ki ganin farko, ma’ana a nutse cikin tarbiyya ya gan ki ko a yanayin rashin tarbiyyah??. Gurin haduwar farko da yanayin da namiji ya gan ki a farko yana da matukar tasiri da amfani cikin neman aure, Hakan ya sa mata ya dace lallai su kula da wasu abubuwa kamar haka… *Kamun Kai Mace ta zama mai kamun kai da mutumta kan ta tare da nuna kyakkyawar tarbiyyah a ko’ina take ,Domin maza kaso 90% cikin 100% abinda suke bukata a macen aure shine tarbiyya da kamun kai ba kyau ba.

*Surutu Lallai ya dace ga mace ta zama in har zata bude bakin ta, to ya zama maganar da zata yi ta zama maikyau ta tarbiyya. Sannan maganganun su zama takaitattu, ba mace ta zauna tayi ta surutu babu kai babu tsari ba, babu nutsuwa da nuna kunyar ‘ya mace. Sutturar mace ma wata jigo ce babba a rayuwar ta, wanda mace ya dace ta dinga sanin irin sutturar da zata sa don suturta jikin ta. Domin yadda mace ke sa suttura ma na bata damar samun miji. Wani shirme da mata ke yi wajen tallata jikin su, wai a tunanin hakan ne zai sa maza su kwadaitu da su, su aure su, tabbas shirme suke tafkawa domin lallai Macen da take suturta jikin ta maza sun fi sha’awar ta da daukar musu hankali, saboda kullum tunanin su wace irin kira ce dauke cikin sutturar nan?, sabanin macen data gama fallasa surar ta kowa ya gama gani. *Ciye-Ciye Lallai mace ta sani ba ko’ina mace ya dace tayi ta ciye ciye ba a gaban maza, Ka ga mace tsakiyar maza tana ta ciye, babu kamun kai. Tauna da ciye ciyen rashin tsari kan zubar da mutumci da kimar mace.

 *Yanar Gizo Kafar sada zumunci ba illah ba ce ga mace matukar zata tsare darajar ta, sabanin wasu matan da suka mayar da abin dandalin su na shaidana da rashin kamun kai. Ka ga mace na turo wasu sakonni da kana gani ka san rashin tarbiyya ya gama keta jikin ta.

*Instagram Ita ma wata kafar sada abota ce, wadda y’an mata da dama ke amfani da ita ta hanya maras kyau, inda mata ke turo hotuna marasa tsari ciki, ka ga wata ta turo kirji, Baki, Mazaunan ta, kai dadai sauran sassan jiki na rashin kamun kai.

 *Jami’a Karatu yana da mahimmanci kwarai ga maza da mata, wanda yanzu kai ya gama wayewa wajen Bazama neman ilmi, wanda hakan tabbas yana dakyau. Amma abin mamaki wasu matan sun mayar da jami’ar wajen kashe Ahu da zubar da tarbiyya da al’ada. Ka ga mace ta fito daga gidan iyayen ta da shigar mutumci, amma tana isa Jami’a zata cire, ta shiga nuna kirar jikin ta, da hulda da maza da wasa da su, tare da wasu halaye marasa tsari. Kafin na karkare filin zan yi kira ga mata akan lallai suyi duba ga wannan abubuwa dana lissafo a sama wanda akasari su ke janyo musu rashin kima gun maza, Ballantana ma su aure su. Za su ga mazan na soyayya da su, amma in aka zo kan maganar aure sai su ki auran su, su je su auri y’ar mutumci mai tarbiyya. Manzon Allah (SAW) da kan sa cewa ya yi namiji na iya auren mace, don abu uku
*Kyau *Asali *Addini Amma daga karshe ya hore su da auren mafi alkhairi daga cikin su, wato mai Addini. Ashe kenan mata dacewa ya yi su jajirce wajen kwatanta kyakkyawar tarbiyya sabanin kaucewa hanya, wadda babu inda zata kai su sai tashar danasani. Mu sani Kyau komai girman sa wataran yana gushewa… Kudi duk yawan su wataran suna iya zama tarihi… Amma Addini baya gushewa har Abada, sannan wanda ya rike shi ba ya tabewa. Mu hadu mako mai zuwa Insha Allahu.


© Leadershipayau

Rashin Jituwar Kannywood Da Afakallahu Ta Sa ’Yan Fim Juyawa Ganduje Baya

Rashin Jituwar Kannywood Da Afakallahu Ta Sa ’Yan Fim Juyawa Ganduje BayaTsamarin da rashin jituwar da ke tsakanin masana’antar Kannywood da shugaban hukumar tace finafinai, Isma’il Afakallahu, ya sanya masu sana’ar shirin fim din Hausa a jihar Kano juya wa gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje baya.
Lamarin ya fito fili bayan gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar, inda rana-tsaka a ka wayi gari ’yan Kannywood da dama sun daina tafiyar gwamnatin Ganduje, wanda kafin zuwan wannan lokaci su ne kan gaba wajen tallata gwamnatin, inda a ka fara ganin su su na yi ma sa wakokin zambo; lamarin da ya ke daure wa da dama kai har a ke zargin ’yan fim da yin butulci.
To, amma binciken da LEADERSHIP A YAU ta gudanar ta hanyar jin ta bakin yawancin masu sana’ar ya nuna cewa, ba haka siddan su ka juya bayan ba; sun yi haka ne saboda jikakkiyar da ke tsakaninsu da Afakallahu.
Wasu wadanda su ka nemi a sakaya sunansu sun nuna cewa, shugaban hukumar tace finafinan ya babbake komai ya hana su su bayyana wa gwamna hakikanin matsalolin da ke damun su, inda kullum a ke yiwa gwamnan ’yar burun-burun.

Hatta horar da su da a ka yi, har kawo yanzu gwamnati ta kasa ba su takardar shaida ko kuma jari kamar yadda a ka yiwa dukkan masu sana’ao’in da a ka horar a jihar. Haka nan alkawarin da gwamna ya dauka na ba wa kundiyarsu mota, ita ma shiru ka ke ji, wai malam ya ci shirya, wato batunta ya sha ruwa kenan.
Sun kara da cewa, wani abu da ya ke addabar su shi ne, tun lokacin da a ka nada Afaka a matsayin shugaban hukumar ya dawo da salon kama su ya na kai su kotu a na cin tarar su, wasu kuma a na daure su. Sun bayar da misali da yadda Afaka ya sa a ka daure Alhaji Salisu Chali da kuma yadda ya sa addabi Marigayi Rabiu Arrahuz har ta kai ga ya koma yin farauci, inda ya kwantsama hatsarin mota ya rasa ransa, baya ga yadda ya kori Alhaji Sani Rainbow, wanda ya na cikin manyan ’yan kasuwar fim da furodusoshi da dama su ka dogara da shi, wanda hakan rashin irinsu ya sa ’yan fim da dama su ka karye.
Bugu da kari, sun yi korafi kan yadda su ka ce Afaka ya yaudare su kan batun bude ofisoshin kananan hukumomi na hukumar da sunan za a bunkasa mu su sana’a, amma har kawo yanzu babu amo babu labari.
Sannan kuma batun ba su rancen kudi da a ka dade a na yi mu su romon baka, shi ma ya sha ruwa, baya ga azabar gaba da su ka ce shugaban hukumar ya na yi da mafi yawan masu sana’ar da ke da tasiri a kasuwar shirin fim a jihar.
Bayanai sun nuna cewa, fitaccen Jarumi Ali Nuhu ya yi iyaka bakin kokarinsa wajen ganin ya shawo kan masu abokan sana’ar tasa, don ganin sun dawo sun cigaba da tafiyar Ganduje, amma da yawansu sun yanke kauna da cewa, matukar Afaka ne ke fada a ji, to za a cigaba da yaudarar su ne kawai.
Haka nan binciken ya cigaba da nuna cewa, hatta fitaccen mawakin nan, Aminu Ala, ya fice daga tafiyar Gwamna Ganduje ne sakamakon zargin da ya ke yi na cewa, bangaren Afakallahu ya yi ma sa yankan baya a tafiyar.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin shugaban hukumar tace finafinan, don ya kare kansa kan wadannan zarge-zarge, amma abin ya ci tura. Saidai idan hali ya yi, shi ma za mu zo da nasa bangaren.
A yanzu dai an ce, irinsu mashahurin Mawaki Ibrahim Ibrahim da fitacciyar Jaruma Rashida Maisa’a su na can su na ta fama da fafutukar hado kan ’yan Kannywood, don su dawo su cigaba da mara wa gwamnan baya a zaben cike gurbi da za a gudanar a jihar ranar Asabar 23 ga Maris, 2019.
Malam Shekarau Ya Bayyana A Fim Din ‘Al’ummarmu’ Don Hadin Kan Musulmi Da Kirista

Malam Shekarau Ya Bayyana A Fim Din ‘Al’ummarmu’ Don Hadin Kan Musulmi Da Kirista
Daga Nasir S. Gwangwazo
Sabon zababben sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi wata fitowa ta musamman a farkon faifen bidiyon fim din ‘Al’ummarmu’ da karshensa, inda ya yi kira ga ma’abota kallon finafinan Hausa da su rungumi kallon finafinai irin Al’ummarmu, domin samar da hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista.
Irin wannan bayyana a faifen finafinan Hausa ita ce irinta ta farko da a ka taba ganin wani fitaccen dan siyasa ya yi, domin karfafa gwiwar hadin kan kasa a Najeriya; kasar da ta ke da rinjayen mabiya addinan biyu, wato Musulmi da Kirista.
Shi dai wannan fim na Al’ummarmu an shirya shi ne da nufin kawo hadin kai tsakanin mabiya wadannan addinai, inda fitattun jarumai irin su Ibrahim Maishunku, Al’amin Buhari, Shehu Hassan Kano, Ladidi Tubeless, Ishaq Sidi Ishaq da sauransu su ka jagoranci wakilcin bangarorin biyu.

Bayanai sun nuna cewa, sakon da ke cikin fim din Al’ummarmu ne ya yi matukar birge zababben sanatan bayan da a ka nuna ma sa kafin ya fito kasuwa. Don haka ya amince a dauke shi da kyamara, saboda ya yi jan hankali da tunatarwa kan wannan sako mai matukar muhimmanci ga jama’ar kasar.
Amma rahotanni sun nuna cewa, Al’ummarmu ya sha tarnaki a hukumar tace finafinai ta jihar Kano a karkashin jagorancin Babban Sakatarenta, Isma’il Afakallahu, kafin ya samu sahalewar fita kasuwa, saboda sabanin da a ke zargin akwai tsakaninsa da masu shirin fim.
Majiyar mai tushe daga hukumar tace finafinai ta tabbar wa da wakilinmu cewa, da fari an saka wa fim din sunan ‘Arewa’ ne, saboda karfafi gwiwar hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristan arewacin kasar, to amma shugaban hukumar ya dakile yin amfani da wannan suna, inda tilas ta sanya a ka sauya sunan fim din zuwa ‘Al’ummarmu’, duk da cewa a na ganin zai fi karbu wa da fa’ida da sunan ‘Arewa’ din.
Sai dai kodayake a yanzu haka fim din ya samu nasarar fitowa kasuwa bayan tsallake wadancan shingaye har a na ma sayar da shi a ko’ina a fadin kasar da makota, inda ya ke samun tagomashi.

Friday, 22 March 2019