Labarai

An Kama Yan Tiktok Da Suka Hau Wakar Daidai Tanan

Hukumar Hisba Ta Kamo Saurayin Da Suka Hau Bidiyon Futsara Da Wata Mace Wanda Har Muka Jawo Hankalin Mahukunta shafin hausamini na ruwaito.

An Kama Yan Tiktok Da Suka Hau Wakar Daidai Tanan
An Kama Yan Tiktok Da Suka Hau Wakar Daidai Tanan

Yanzu haka hukumar Hisba ta kamo Saurayin nan mai suna Kamalu Bashir ɗan Hotoro da ke jihar Kano, Idan baku manta ba a Shekaranjiya mun wallafa wani Faifan bidiyo mai ƙunshe da nuna ISKANCI da FITSARA A FILI BA TSORON ALLAH wanda da yawan ku mabiyan mu kukai ta kiran mu kuna cewa mu cire wasu na zagin mu a cikin Comments duk a ƙarshe kiran da muka yi ga shi an samu nasara.

Kuma babban dalilin da yasa ba cire ba, A lokuta da dama hoto mai motsi yakan zama darasi da izina ga wasu amma yanzu mun janye wannan bidiyon da muka wallafa na sheɗancin da wannan saurayi suka yi da wata budurwa.

Kazalika, Muna godiya sosai da hukumar Hisba ta jihar Kano da duk ma’aikatan su ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina da duk waɗanda suka taya mu isar da wannan saƙon a wurare daban-daban, Kamar yadda Taskira – H Online Tv Ta Wallafa Tana kira da mahukunta da cewar ya kamata su nemo wanda ya yi waƙar da waɗanda suka hau kan waƙar domin a yi musu hukunci daidai da abun da suka yi.

Allah Ta’ala ya shirye mu ya shiryi zuri’ar mu, Allah ya tsare mana imanin mu ya kare mu da mugun ji da mugun gani, Amin Ya Allah.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button