Labarai

Da duminsa: Buhari ya sa hannu kan wata sabuwar doka da za tayi maganin barayin gwamnati

Shugaba Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar hadin taimakawa juna wurin yakar masu laifi – Wannan dokar za tayi aiki ne kan masu aikata laifuka a kasa Najeriya da kasashen ketare musamman laifukan rashawa

 – Sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Yunin 2019 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar hadin gwiwa wurin yakar masu laifi wato ‘Mutual Assistance in Criminal Matters Act, 2019’ domin inganta yaki da rashawa a Najeriya da kasashen ketare. Ita Enang, babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan ayyukan Majalisar Tarayya ne ya bayar da sanarwar a ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, an kafa sabuwar dokar ne domin Najeriya da kasahen duniya su rika taimakawa juna wurin kama masu laifi kamar gano idan suka boye, neman shaidu da wasu takardun da za su taimaka wurin gano masu laifin. Ya ce wasu daga cikin dalilan da yasa aka kafa dokar sun hada da:

Binciko kayayaki da kadarorin da masu laifi suka sace, kwato kayayakin sata da wasu laifukan. “Gano sakonni da masu laifi ke aikawa junansu da sa ido kan su.”

 “Karbo kadarorin da aka kwace da kuma neman taimako daga kasashen ketare muddin bai saba dokar kasashen ba.

 “Attorney-Janar na kasa shine ke da wuka da nama wurin karbar bayyanai daga wasu kasashe da kuma neman alfarma wurin kasashen kan duk wani abu da ya shafi wannan dokar.” 

Hadimin shugaban kasar ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar 20 ga watan Yunin 2019.

®Legit

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button