Addini

SAƙO Ga Ƴar Luwadi !!! – Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Liwadi shine namijj yana neman danuwansa namiji, kamar yadda ake neman mace,
Shedan ya fitowa da mutane wannan halaka,  da bukatu da yawa,  domin tsafi, domin neman kudi,  domin neman daukaka, domin neman mulki, domin neman kwarjini da makamantansu,  KUMA duk karyace, babu wani abu da ake samu sai kaskanci da koma baya a duniya da lahira.

Babbar musifa babban bala’i, tashin hankali,tir, abin kaico, abin kunya abin takaici, namiji yana neman danuwansa namiji, abinda baa samu a cikin  dabbobi, amma a sami wasu matasa, wai har sun kafa kungiya ta masu neman maza, wannan kawai ya isa musifa da bala’i
da halaka, a sami wannan laifi yana yaduwa a cikin matasa, mu duba yadda Allah Ta’ala ya yiwa wannan kasa, ta Annabi Ludu as , da suke liwadi aka ruguza su, sama ta koma kasa,kasa ta koma sama, amma ace wannan abin ya zama, a cikin al’ummar Annabi saw,
Allah ya shiryar da masu yi da wadanda ake yiwa.
Luwadi yana jawowa mai yinsa bala’i 30
Na daya: karancin muwafaka
Na biyu : gurbatar raayi
Na uku : gurbatar zuciya
Na hudu : toshewar basira
Na biyar : Jefa kiyayya da kyamar mai yi a zuciyar bayin
Allah
Na shida: yana haifar da dimuwa
Na bakwai : rashin amsa addua
Na takwas : shafe albarka
Na tara : tabewa
Na goma : zarabta da kaskanci
Na sha daya : rinjayen makiya
Na sha biyu : kuncin kirji
Na sha uku : bacin zuriya
Na sha hudu : mugayen abokai
Na sha biyar : zama cikin tsoro da firgici
Na sha shida : kuncin rayuwa
Na sha bakwai : raunin jiki
Na sha takwas : mugun mafarki
Na sha tara : cututtuka marasa magani
Na ashirin : kin jin dadin sauraren Alkur’ani mai girma
Na ashirin da daya : gafala ga ambaton Allah
Na ashirin da daya: mummunar cikawa
Na ashirin da biyu : gushewar ni’imah
Na ashirin da biyu : tabuwar hankali
Na ashirin da uku : zubewar mutunci
Na ashirin da hudu : dabi’ar daud
Na ashrin da biyar : gushewar kunya
Na ashirin da shida : gushewar kishi
Na ashirin da bakwai : kaskanci
Na ashirin da takwas : rinjayar shedan
Na ashirin da tara : mala’iku zasu gujeshi
Na talatin : hukuncin kisa ya hau kansa idan an kama shi da shedu ko kuma yayi iitirafi a gaban kotu.
Magani:
1- Tuba da Nadama,
2- Hakuri daga sabon Allah
3-Canja abokai
4- Addua
5- Yawan Anbaton Allah
6- yawan karatun Alkur’ani mai girma
7- karanta tarihin magabata
8- tunanin wuta da Aljannah
9- tsoran Mummmunar cikawa
10 – Yin aure, da wadatuwa da iyali ta inda Allah ya
halatta
Allah ya shiryi wadanda suka fada wannan bala’i, ya
tsare wadanda basu fadaba. Amin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button