Monday, 9 October 2017
Me yiwuwa Ronaldo da Messi ba za su je Rasha 2018 ba

Home Me yiwuwa Ronaldo da Messi ba za su je Rasha 2018 ba
Ku Tura A Social Media
Fitattun 'yan kwallon kafa na duniya Ronaldo da Messi da Sanchez na fuskantar barazanar rashin zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za a yi a Rasha.

A halin da ake ciki yanzu dai, ana daf da rufe shiga gasar, kuma wasu daga cikin manyan kasashen duniya na fuskantar barazanar samun shiga.


Yayin da kasashe kamar su Brazil, da Spaniya, da Ingila suka samu gurbi a Rasha, wasu kasashen da ake zaton za su taka leda a gasar ta duniya har yanzu na fafutuka.
Hakan na nuna cewa akwai yiyuwar manyan fitattun 'yan wasa na duniya da suka hada da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Alexis Sanchez ba za su halarci gasar ba.

Rahoto daga bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: