Monday, 19 December 2016
FATAWAR RABON GADO(81) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Home FATAWAR RABON GADO(81) | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Ku Tura A Social Media
*FATAWAR RABON GADO (81)*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, malam  Tambaya ce dani dan Allah,, mahaifinmu  ne yarasu ya bar mata biyu kuma da ya'ya' guda 32, maza16 mata 16.yaya rabon gadon zai kasance?
*Amsa*
  Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida takwas, a bawa matansa kashi daya, ragowar kashi bakwan sai a bawa 'ya'yansa su raba, duk namiji ya dau RABON mata biyu.      
Allah ne mafi sani
12/11/2016
Amsawa
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*

Share this


Author: verified_user

0 Comments: