Showing posts with label SPORT:::::::::::::. Show all posts
Showing posts with label SPORT:::::::::::::. Show all posts

Friday, 14 September 2018

Shehu Abdullahi Yace Zai Yi Ma Kungiyar  Mahaifarsa Sa Goma Ta Arziki idan sunka zura kwallo a ragar kano pillars

Shehu Abdullahi Yace Zai Yi Ma Kungiyar Mahaifarsa Sa Goma Ta Arziki idan sunka zura kwallo a ragar kano pillars
Dan wasan Super eagles zaiyi ma kungiyar mahaifar sa goma ta arziki idan suka zura kwallo a ragar Kano pillars

Yace a ko wani kwallo da tawagar ta zura a ragar abokan adawar su kuma suka yi nasara a wasan kungiyar zata samu naira dubu dari daya.


Mai tsaron bayan ragar tawagar super eagles ta Nijeriya Shehu Abdullahi yace a shirye yake domin yi ma kungiyar mahaifar sa wato Sokoto united goma ta arziki na ko wani kwallo da suka zura a ragar Kano Pillars wasan tare na gasar Aiteo Cup.

A sakon faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Tuwita dan wasan yana mara ma kungiyar Sokoto United baya kuma yana karfafa gwiwar su wajen samun galaba.

Yace a ko wani kwallo da tawagar ta zura a ragar abokan adawar su kuma suka yi nasara a wasan kungiyar zata samu naira dubu dari daya.

Dan wasan ya fara wasa a kungiyar Sokoto United da Kano Pillars gabanin zuwan sa kungiyar kasar waje.

Tsohon kungiyoyin sa zasu fafata a rukuni na biyu na gasar kofin Nijeriya ranar lahadi 16 ga watan Satumba.

Ga yadda sauran wasannin rukuni na biyu na gasar zata kaya;

Mighty jets vs Kwara utd

Osun utd vs Katsina utd

Ifeanyi ubah vs J. Atete

Elkanemi Warr vs Katsina utd feeders

Wikki Tourists vs Bayelsa utd

Cofine FC vs Sunshine stars

Crown FC vs Abia Warriors

Kogi utd vs Niger Tornadoes

Nasarawa utd vs Standard FC

Remo stars jnr vs Rivers utd

Yobe stars Plateau utd

Go round vs supreme court

Kebbi Utd vs Enugu Rangers

Monday, 3 September 2018

Ronaldo,  Modric Da Mo Salah na Takarar zama dan wasan 2018

Ronaldo, Modric Da Mo Salah na Takarar zama dan wasan 2018

Hukumar Kwallon kafa ta duniya Fifa ta bayyana Cristiano Ronaldo da Mohammed Salah da kuma Luka Modric a matsayin wadanda ke takarar zama dan wasan da yafi fice na wannan shekara ta 2018.

Ronaldo ne yafi zira kwallo a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, abinda ya baiwa kungiyar Real Madrid nasarar lashe kofin sau uku a jere.

Shima Luka Modric ya taka rawa wajen nasarar kungiyar Madrid, kana kuma ya lashe kwallon zinare saboda ficen da yayi da kasar sa ta Croatia gasar cin kofin duniya.

Mohammed Salah kuwa ya taka rawa ne wajen nasarar kungiyar Liverpool inda ya zirara kwallaye 44, wanda ya taimakawa kungiyar zuwa wasan karshe, kafin Real Madrid ta doke su, bayan ya samu rauni a kafadar sa.

Friday, 10 August 2018

Kalli Bidiyon Dandazon Jama'a Da Suka Tarbi Shahararren Dan Wasan Nijeriya Ahmed Musa a kasar Saudiya

Kalli Bidiyon Dandazon Jama'a Da Suka Tarbi Shahararren Dan Wasan Nijeriya Ahmed Musa a kasar Saudiya


Ahmed Musa ya sauka filin jirgin saman King Khaled dake nan birnin Riyadh ranar alhamis inda ya samu kyakkyawar tarba daga dinbim masoya dake jiran sa.

Dan wasa mai tauraro Ahmed Musa ya samu tarba daga dinbim masoyan sa yayin da ya sauka daga jirgi a kasar Saudia Arabia.

Dandazon masoyan fitaccen dan wasan Nijeriya suka garzaya filin jirgin sama domin yi ma
sabon dan wasan kungiyar Al-nassr maraba.

Ahmed Musa ya sauka filin jirgin saman King Khaled dake nan birnin Riyadh ranar alhamis inda ya samu kyakkyawar tarba daga dinbim masoya dake jiran sa.
A cikin wata faifan bidiyo da sabon kungiyar dan wasa ta fitar a shafin ta an kafafen sada zumunta, an gan inda magoya bayan kungiyar ke murna tare da yi masa waka.
Tsohon dan wasan Kano Pillars zai nemi ya kafa tarihi a sabon kungiyar shi cikin shekaru hudu kamar yadda kwantiragi cinikin shi ta bayyanar.

Dan wasa mai tauraro ya koma kasar larabawa da taka leda bayan yarjejeniyar da kungiyar tayi da tsohon kungiyar shi na kasar Ingila na siyan shi a kan farashi wanda ba'a bayyanar. Sai dai ana hasashe miliyoyin kudi ne.
Ya bar kungiyar Leicester bayan shekara biyu da murza musu leda. Sai dai cikin shekaru biyun da yayi ya koma tsohon kungiyar shi ta CSKA Moscow bisa matakin aro gabanin kammala kakar 2017/2018.

Kungiyar Al-nassr ita ce ta zo na uku a gasar kakar da ta shude, ana kyautata zaton zata taka rawar gani a gasar bana bisa ga taimakon dan Nijeriya wajen saka kwallaye a ragar abokan adawar su.

Friday, 3 August 2018

Ahmed Musa Zai Koma Kasar Saudiya  Da Taka Leda

Ahmed Musa Zai Koma Kasar Saudiya Da Taka LedaDan wasan gefe na Najeriya, Ahmed Musa na shirye-shiryen yin kaura zuwa kungiyar Al Nassr da ke kasar Saudi Arabia daga kungiyar Leicester City ta Ingila.

Dan wasan Najeriya Ahmed Musa da ke taka leda a kungiyar kafa ta Leicester City a Ingila zai koma kasar Saudiya da buga kwallo.

Kafofin yadan labaran cikin gida a Najeriya sun ruwaito cewa Musa zai koma kungiyar Al Nassr akan kudi fam miliyan 25 na Ingila.

Rahotanni sun ce Musa zai isa kasar ta Saudiyya a gobe Asabar domin karkare shirye-shiryen komawa kungiyar ta Al Nassr.

Idan har aka kammala cinikin dan wasan, Musa zai zamanto dan wasa mafi tsada cikin 'yan wasan Najeriya da ke buga kwallo a kasashen waje.

Kungiyar ta Al Nassr, na daya daga cikin manyan-manyan kungiyoyin kwallon kafa a Saudiyya.

Ta lashe kofuna 24 a gasa daban-daban da aka yi a kasar da sauran yankunanta.

Musa shi ne dan wasan da ya fara zirawa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha a wasanta da Iceland, inda ya ci duka kwallaye biyu a wasan da aka tashi 2-0.

Ya taba bugawa kungiyar CSKA Moscow kwallo a Rasha inda daga bisani ya koma Leiscester City, ko da yake, ya taba komawa CSKA Moscown a matsayin dan wasan aro daga kungiyar ta Leicester.

Monday, 30 July 2018

An yanke wa Ronaldo daurin shekara biyu da tarar dala miliyan 3.7

An yanke wa Ronaldo daurin shekara biyu da tarar dala miliyan 3.7

Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7, bayan daurin shekaru biyu da kotu ta yi masa. Sai dai kuma ba zai zauna gidan kurkuku ba.

Wannan ya zo karshen kiki-kakar da ake da shi a kotu na tsawon lokaci inda mahukuntan kasar Spain suka zarge shi da kin biyan haraji a lokacin da ya ke wasa a Real Madrid.
Ronaldo dai ya musanta zargin da ake masa. An yanke masa wannan hukunci ne ranar Juma’a.

An zargi Ronaldo da kin biyan haraji har na Yuro milyan 5.7
Ronaldo mai shekara 3 a duniya, ba zai je gidan kurkuku ba, saboda dokar kasar Spain ta ce ko da an yanke wa mai laifi irin wannan hukuncin dauri, matsawar a karon farko ne, to ba zai je gidan yari ba, sai dai ya biya tarar kawai.

Amma kuma maimakon dauri, zai rika biyan wani sabon haraji na Yuro 250 a kowace rana har tsawon shekaru biyun da aka yanke masa, a madadin zaman gidan kurkuku.

Bayan wanna, Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7 da kuwa zunzurutun Yuro milyan 5.7 wadanda tun da farko ya ki biya a matsayin tarar da ta sa aka maka shi kotu.
Akwai kuwa tarar wata Yuro milyan daya da zai biya, a matsayin kudin ruwan da suka taru a hannun sa, a tsawon lokacin da ya ki biyan harajin.

Gaba daya dai Ronaldo zai biya tarar Yuro miliyan 19, wadanda idan aka auna su a sikelin naira, bilyoyin nairori ne masu yawa.

Friday, 27 July 2018

Shahararren Dan Wasan Super Eagles Ahmed Musa Da Matarsa Juliet Sun Samu Karuwa

Shahararren Dan Wasan Super Eagles Ahmed Musa Da Matarsa Juliet Sun Samu Karuwa

Wannan shine na uku da zai samu kuma na farko da zai samu aurensa da Juliet Ejue wanda aka daura cikin shekarar 2017.Kwana daya bayan yin nasara zama dan wasa na 8 da kwallon sa yafi birgewa a gasar kofin duniya na wannan shekaru, Ahmed Musa da Matar sa Juliet Ejue sun samu karuwar da.
Dan wasan wanda tauraron sa ke haskawa ya sanar da wannan abun farin ciki a yammacin ranar alhamis a shafin sa na Instagram.

Ya rubuta "Ina mai sanar daku cewa cikin dan kanakanin lokaci da ya wuce a baya Allah ya albarkace ni da samun karuwar yaro. Kalamai baza su iya bayyana irin farin ciki dake tattare dani ba!

Ya rubuta hakan ne tare wallafa hoton jaririn da suka samu.
Wannan shine da na uku da dan wasan super eagles zai samu kuma na farko auren sa da amarya Juliet Ejue .
Dan wasan ya haifi yara biyu Ahmed Musa Junior da Halima Musa auren sa da tsohuwar uwardakin sa Jamila .

Kwallon sa shine na uku a cikin jerin kwallaye da aka ci a gasar kofin duniya na FIFA
Wannan abun farin ciki ya biyo bayan wanda ya samu na zama dan wasa mai kwallo mafi birgewa na 8 a gasar kofin duniya na wannan shekarar.
Kwallon shi na biyu wasan Nijeriya da Iceland a gasar ya fito takarar jerin kwallaye mafi birgewa sai dai amma bata yi nasarar zama na daya ba.
Dan wasan kasar Faransa wacce tayi nasarar zama zakarun gasar Benjamin Pavard shine ya lashe kyautar gasar.

Ahmed Musa shine dan wasan mafi kwallo a tarihin yan wasan tawagar Nijeriya » a gasar kofin duniya. Ya samu wannan matsayin ne samakon kwallaye biyu da zura a raga a gasar bana wanda ya daga yawan kwallayen shi daga biyu zuwa hudu.

Auren sa da Juliet Ejue
Dan wasan kungiyar Leicester ya auri amaryar shi Juliet cikin shakarar 2017 bayan rabuwar sa da Jamila. Bikin auren su ya samu halarci manyan jarumai a dandalin wasan kwallon kafa da harkar nishadi.
Anyi bikin a garin mahaifan amaryar sa dake nan Ogoja dake jihar Kuros Riba.

Sources:pulsehausa.com

Tuesday, 24 July 2018

Bamu Yarda Mu Bayarda Dembele Ba Don A Bamu Hazard - Inji Barcelona

Bamu Yarda Mu Bayarda Dembele Ba Don A Bamu Hazard - Inji Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bayyana cewa ba zata bayar da dan wasanta Ousmane Dembele ba a kan a bata Edin Hazard domin a cewar kungiyar Dembele matashin dan wasa ne kuma zai iya fin Hazard iya kwallo nan gaba.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai ta nuna sha’awarta ta neman dan wasa Edin Hazard bayan da dan wasan ya bayyana cewa yana tunanin barin kungiyarsa ta Chelsea domin samun sabuwar kungiya.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce take zawarcin dan wasan bayan da ta siyar da dan wasanta Cristiano Ronaldo zuwa ga kungiyar Jubentus kuma take ganin Hazard ne zai iya maye mata gurbinsa.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta nuna sha’awarta na neman dan wasan inda akayi zargin zata bayar da Dembele a matsayin aro ko kuma ta siyar dashi ga ungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Sai dai kungiyar ta bayyana cewa bazata yarda ta rabu da matashin dan wasan ba wanda ta siya fam miliyan 97 a kakar wasan data gabata daga kungiyar Borussia Dortmund domin yam aye mata gurbin Neymar wanda yabar kungiyar zuwa PSG.
Dembele dai bai fara kakar wasan data gabata cikin nasara ba bayan da a wasansa na biyu a kungiyar yatafi jinya ta kusan wata hudu kuma bayan yadawo yaci gaba da samun matsaloli akai-akai.
Sai dai yana daya daga cikin ‘yan wasan Faransa da suka lashe gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Rasha a tsakiyar wannan watan.
Majiyarmu leadershipayau.

Sunday, 22 July 2018

Chelsea Da Real Madrid Sun Cim Ma Yarjejeniya A Kan Hazard

Chelsea Da Real Madrid Sun Cim Ma Yarjejeniya A Kan Hazard

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyoyin Real Madrid da Chelsea sun amince da cinikin dan wasa Edin Hazard dan kasar Belgium wanda Real Madrid ta dade tana nema domin maye mata gurbin Cristiano Ronaldo.

Hazard dai ya bayyana aniyarsa ta barin Chelsea domin komawa Real Madrid bayan da ‘yan jaridu sukayi masa tambayar ko yanadasha’awar komawa Real Madrid.
Tuni dai Neymar da Mbappe suka bayyana cewa bazasu koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ba bayan da rahotanni suka bayyana cewa kungiyar tana zawarcin ‘yan wasannin na kungiyar kwallon kafa ta PSG.

Tuni rahotanni suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wadda itace zakara a nahiyar turai ta amince zata biya fam miliyan 170 domin siyan Hazard wanda tauraruwarsa ta haska a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Rasha.
Sai dai wasu rahotannin sun bayyana cewa fam miliyan 170 din da Real Madrid ta amince zata biya har da kudin da zata biya domin siyan mai tsaron raga Thibaut Courtois wanda shima dan kungiyar Chelsea ne..


Hazard dai ya amince da komawa Real Madrid bayan daya amince da albashin da kungiyar tace zata dinga bashi duk da cewa sabon kociyan kungiyar, Mauricio Sarri ya bayyana cewa yanason ganin yashawo kan Hazard domin yaci gaba da zama a kungiyar.

Tuesday, 17 July 2018

Ni Zan Lashe Kyautar Ballon D'or - Cristiano Ronaldo

Ni Zan Lashe Kyautar Ballon D'or - Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce wata kila shi ne zai lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya wato Ballon d'Or.
Dan kwallon ya bayyana hakan ne lokacin gabatar da shi ga magoya bayan kungiyar Juventus a ranar Litinin.

Hakazalika dan kwallon ya ce yana godiya game da damar da kungiyar ta ba shi saboda 'yan wasa masu irin shekarunsa a wannan zamani "suna koma kasashen Qatar da China ne".
A makon jiya ne dan wasan, mai shekara 33, ya koma kungiyar Juventus ne a kan fan 99.2 bayan ya yi shekara tara a Real Madrid.
"Na koma wannan kungiyar a wannan lokaci. Ina matukar farin ciki," a cewarsa.
Har ila yau ya ce yana fatan kasancewa "mai sa'a" yayin da kungiyar take fafutikar lashe Gasar Zakarun Turai.

Albashin Ronaldo a Juventus

Naira biliyan 50 aka sayo shi

N12.5b

A shekara Naira

       1b

A duk wata


N258m A duk mako

N36m A duk rana

N1.5m A duk awa daya

N12m A awanni takwas na baccinsa


Ronaldo, wanda sau biyar yana lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya, ya ci wa Madrid kwallaye 450 ne - kuma sau hudu yana lashe Kofin Zakarun Turai da kuma La Liga biyu.
"Ina so na yi nasara, ina so na zama fitacce. Wa ya sani watakila kila na kara lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya, amma haka rayuwa za ta ci gaba da tafiya da kanta," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Samun hakan yana da wuya a Manchester da Real Madrid, amma watakila na sake samu a nan, za mu gani."
Dan wasan kasar Portugal din ya ce akwai abubuwa da dama da suka sanya ya shi ya amince ya koma Juventus.

Bajintar Ronaldo

Ronaldo ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Madrid

Ya ci kwallaye 105 a gasar Zakarun Turai

Kwallaye 311 a gasar La Liga

Kofi 16 a Real Madrid da suka hada da La liga biyu da Zakarun Turai hudu da gasar duniya ta kungiyoyi.

Ya ci kwallaye uku-uku (hat-tricks) shi kadai sau 44, kuma sau 34 a La Liga
Sau takwas yana cin kwallaye fiye da hudu a Real Madrid
Ya taba cin kwallaye 61 a kakar 2015-16 a dukkanin wasanin da ya buga
Hakan ya hada da kwallaye 48 a La Liga
Kwallaye 659 ya ci a rayuwarsa - biyar a Sporting Lisbon, da 118 a Manchester United da 451 a Real Madrid da 85 a Portugal
Sau biyar yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or

Monday, 16 July 2018

Kylian Mbappe zai Lashe Kyautar Dan kwallo Duniya

Kylian Mbappe zai Lashe Kyautar Dan kwallo Duniya

Tsohon dan wasan Ingila Rio Ferdinand ya ce, zaratan ‘yan kwallon duniya wato Christiano Ronaldo da Lionel Messi za su sallama kambinsu ga matashin dan wasan gaba na Faransa, Kylian Mbappe da ya taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Ferdinand ya ce, nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa, Mbappe zai tsaya akan dandamali don karbar lambar yabo ta Ballon d’Or da ake bai wa dan wasa mafi kwarewa a duniya, kuma Ronaldo da Messi sun shafe tsawon shekaru suna lashe wannan kyauta a tsakanininsu.

Mbappe mai shekaru 19 ya zama matashin dan wasa na biyu a tarihi da ya ci kwallo a wasan karshe a gasar cin kofin duniya bayan Pele wanda ya fara nuna wannan bajintar a shekarar 1958.

Mbappe ya jefa kwallo ta hudu a ragar Croatia a minti na 65 a wasan na karshe a Rasha, yayin da ya lahe kyautar gwarzon matashin dan wasa a gasar cin kofin duniya a bana.

Sunday, 15 July 2018

Russia 2018 World Cup: Wadanda suka sami kyautuka daga FIFA bayan kammala wasan a yau a Kasar Russia

Russia 2018 World Cup: Wadanda suka sami kyautuka daga FIFA bayan kammala wasan a yau a Kasar Russia

'Russia 2018 World Cup: Wadanda suka sami kyautuka daga FIFA bayan kammala wasan a yau a Kasar Russia.

1. Luka Modrić Daga Kasar Croatia Shine Ya Samu Kwallon Zinare Golden Ball Wato Gwarzon Dan Kwallo (Best Player)

2. Harry Kane Daga Kasar England Shine Mafi Yawan Zura Kwallo A Raga, Don Haka Ya Samu Kyautar Takalmin Zinare (Golden Boot).

3. Kylian Mbappé Dan Kasar Faransa Shine Ya Zama Tauraron Dan Wasa Mai Tasowa (Young Player of the Tournament)

4. Maitsaron Raga Thibaut Courtois Daga Kasar Belgium Shine Ya Samu Kyautar  Safar Hannun Zinare (Golden Glove) Wanda hakan ke Nufin Ya Zama Mai Tsaron Raga Mafi Tasiri A Gasar (Best Goalkeeper).

Wednesday, 11 July 2018

Dan wasan Nijeriya Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa Rangers

Dan wasan Nijeriya Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa Rangers
Tun ba yau ba sabon kocin kungiyar Rangers ya nuna sha'awar da yake ma dan Nijeriya kuma ya sha alwashin kawo matashin kungiyar.

Gwarzon matashin dan kwallon super eagles, Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa kungiyar Rangers da taka leda.
Kamar yadda jaridu suka bayyana, dan wasan zai koma kungiyar ne bisa yarjejeniyar aro daga kungiyar Roma na tsawon shekara daya.Tun ba yau ba sabon kocin kungiyar Rangers ya nuna sha'awar da yake ma dan Nijeriya kuma ya sha alwashin kawo matashin dan kwallon kungiyar.

Tsohon gwarzon dan wasan kungiyar Liverpool  yace hazikin matashin yana daya daga cikin dinbim yan wasa da suke birge shi. Ya yaba gwaninta da dan Nijeriyan ke nunawa a filin kwallo.

Dan wasan ya sauka filin jirgin sama ta Edinbugh daidai karfe 10 na safiyar ranar Litinin 9 ga wata domin daukar matakai na karshe kan kwantiragin sa da kungiyar.

A rahoton da jaridar Daily Mail ta fitar, tauraron dan kwallon yana jiran takardar aiki na kasar gabanin sa hannu ga takardar kwantiragi.Sadiq Umar wanda ke taka ma kungiyar As Roma na kasar Italiya wasa zai shiga cikin jerin sabbin yan wasan da sabon kocin Rangers ya kawo.

Kai ga yanzu kungiyar Rangers ta siyo yan wasa bakwai. ga sunayen su kamar haka: Scott Arfield, Allan McGregor, Jamie Murphy, Nikola Katic, Connor Goldson, Ovie Ejaria da Jon Flanagan.

Akwai yiuwar bayan Sadiq Umar shima dan wasan tsakiyar kasar Mali, Lassana Coulibaly, zai dawo kungiyar da taka leda bisa yarjejeniyar aro daga kungiyar Angers na kasar Faransa.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga naijhausa.com.

Tuesday, 10 July 2018

Cristiano Ronaldo ya amince ya koma Juventus

Cristiano Ronaldo ya amince ya koma Juventus

Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya amince ya koma Juventus, abin da ya kawo karshen shekara tara da ya shafe a Spain.
Kungiyoyin biyu sun amince kan dan kwallon mai shekara 33 ya koma Italiya kan fan miliyan 105.

Hakan na nufin zai zamo daya daga cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.
Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid.

Juventus ta bayyana cewa dan kwallo zai sanya hannu kan kwantiragin shekara hudu, sannan ta wallafa zanen dan wasan a sanfurin irin murnar da yake yi idan ya ci kwallo:
"Lokaci ya yi da zan bude wani sabon shafi a rayuwata, a don haka na nemi kulob din ya sayar da ni", kamar yadda ya fada a wata sanarwa da aka fitar .

Paris St-Germain ne suka sayi 'yan wasa biyu mafiya tsada a duniya - fan miliyan 200 ga Barcelona domin sayen Neyrmar, da kuma miliyan 166 don sayen dan Faransa Kylian Mbappe a watan Yuli bayan ya shafe shekara daya a matsayin aro.

Barcelona ma ta biya Liverpool fan miliyan 142 lokacin da ta sayi Philippe Coutinho a watan Janairu.

Rahoto:- bbchausa

Thursday, 5 July 2018

Ahmed Musa Da Abdullahi Shehu Sun Yi Wa Marayu Goma Ta Arziki A Sokoto  Kalli hotuna

Ahmed Musa Da Abdullahi Shehu Sun Yi Wa Marayu Goma Ta Arziki A Sokoto Kalli hotuna

Ahmed ya ba su milyan daya, yayin da Abdullahi ya ba su buhunan shinkafa guda 100 da kayan masarufi

DAGA MUKHTAR HALIRU TAMBUWAL SOKOTO

'Yan wasan kwallon kafar Nijeriya Ahmad Musa da Abdullahi Shehu sun kai ziyara a makarantar UK Jarma Academic (akasarin yaran daga jahohin maiduguri da Yobe wadanda suka rasa iyayen su  sanadiyyar rikicin Boko Haram) inda Abdullahi ya ba su tallafin kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa guda dari, kwalin indomi hamsin da katon ashirin na lemun kwalba.

A bangaren wasanni kuma, Abdullahi Shehu ya b su kala biyu na kayan wasa da kwallo biyu domin su motsa jikinsu.

Dan kwallon na Nijeriya, Abdullahi Shehu dan asalin jihar Sokoto ne.

Abokinsa Ahmad Musa shi ma ya bayar da naira milyan da rabi domin cigaba da hidimar wadannan bayin Allah.

Shugaban hukumar zakka da wakafi na jiha kuma shugaban dauko yaran ne Malam Muhammad Lawal Maidoki  ya karbe su a madadin Jarman Sokoto, Dr. Ummarun Kwabo.

A. A Kwamishinan Matasa da Wasanni ne ya jagoranci tafiyar matasan tare da goyon bayan dimbin matasa masu goyon bayan 'yan wasan.

Tuesday, 3 July 2018

Akwai Yiyuwar Cristanio Ronaldo Ya koma Kungiyar Juventus

Akwai Yiyuwar Cristanio Ronaldo Ya koma Kungiyar Juventus

Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya sauya sheka daga kungiyar zuwa Juventus cikin wannan kaka, bayanda shugaban Real Madrid Florentino Perez ya gaza cimma muradin na wasan na biyan yuro miliyan 30 a kowacce kakar wasa, maimakon haka Club din ya bukaci ya biya shi yuro miliyan 25 a kowacce kakar wasa.

Ronaldo wanda ke hutu a yanzu haka bayan koro kasarsa daga gasar cin kofin duniya, yaki rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Real Madrid amma kuma kawo yanzu babu Club din da ya miko bukatar sayenshi.

Kusan dai hakan ne ya faru da dan wasa a kakar da ta gabata, inda har aka kulle kasuwar cinikayyar ‘yan wasa ba a samu Club din da ya nuna bukatar sayenshi ba, duk kuwa da kwarewarsa a fannin na Tamaula, ko da dai akwai tarin kungiyoyi da ke fatan ganin dan wasan ya taka musu leda ciki kuwa har da ita Yuventus din.

Yanzu haka dai dillalin dan was am Jorge Mendes ya yi wata ganawa da shugabancin na Yuventus game da makomar dan wasan, matakin da ake ganin zai yiwa magoya bayan Juventus din dadi la’akari da lokacin da suka shafe suna fatan sayen dan wasan.

A bangaren Juventus din dai biyan adadin kudaden da Ronaldon ke bukata baa bin damuwa ba ne domin kuwa tuni suka ware yuro miliyan dubu guda don cinikayyar ‘yan wasa a wannan karon, ko da dai ana ganin ba lallai Madrid din ta amince ba, la’akari da cewa yana da sauran kwantiraginsa da Real din zuwa nan da 2021.
Moh Salah Ya kafa Tarihi  A kungiyar Liverpool

Moh Salah Ya kafa Tarihi A kungiyar Liverpool

Fitaccen dan wasan kasar Masar, Mohamed Salah, ya kafa tarihi a kungiyar Liverpool na Ingila inda yake taka leda.
Zakaran yan wasa a kakar bana, shine dan wasa mai karban albashi mafi yawa a tarihin kungiyar.
Hakan ya faru ne bayan sabonta yarjejeniyae sa na cigaba da taka ma kungiyar leda har tsawon shekara biyar.
Dan wasan ya rattaba hannu ga takardar kwantiragin sa da kungiyar. Sabon yarjejniyar zai sa ya amshi albashin pam dubu dari biyu ( 200,000 ) a ko wani karshen mako.
Dan kwallon mai shekaru 26 ya koma liverpool daga kungiyar Roma na kasar Italiya a cikin shekarar 2017. Dan wasan yana karban pam 100,000 a kakar bara gabanin sabon yarjejeniya da ya saka hannu.
Mohamed Salah, ya samu yabo da jinjina bisa rawar da ya taka a kakar bara. Hakan ma yasa kungiyoyi da dama ke neman sa da ya dawo gare su da taka leda ciki har da Real Madrid da Barcelona.

Monday, 2 July 2018

Shi Ko Ahmad Musa Zai Koma Bugun Kofin Duniya (world cup) ?

Shi Ko Ahmad Musa Zai Koma Bugun Kofin Duniya (world cup) ?

Yayin da wasu 'yan wasan Super Eagles ke cewa za su haki gaba, wasu daga cikin 'yan wasan kuma damarsu ta karshe ke nan na wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya.
Hukumar Fifa ta ce tawagar ta Najeriya ce mafi kankantar shekaru da suka tafi gasar cin kofin duniya a Rasha.
Mafi yawancin 'yan wasan da suka wakilci kasar suna tsakanin shekara 19 zuwa 26.
Mai tsaron ragar Najeriya Ozoho ne dan wasa mafi kankantar shekaru a tawagar Super Eagles inda ya ke da shekara 19.

Sai dai kuma akwai wadanda ko shakka babu ba za su sake zuwa gasar cin kofin duniya ba saboda wasu dalilai da suka hada da yawan shekaru.
Akwai kuma wasu daga cikin matasan da ake ganin ba za su yi karkon da za su samu damar sake wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar 2022 ba.
Mun yi nazari game da makomar wasu 'yan wasan na Najeriya.
Matasan da ba su da tabbas
Daga cikin wadanda ake ganin ba za su yi karkon sake wakiltar Najeriya ba a gasar cin kofin duniya, sun hada da Victor Moses da Ahmed Musa da Abdullahi Shehu da Nwankwo.
Dan wasan Chelsea Victor Moses wanda ya tafi Rasha yana da shekara 27, zai kasance kafin Qatar 2022 yana da shekara 31.
Makomarsa za ta dogara ne da rawar da zai taka nan gaba a wasannin kulub dinsa da kuma Najeriya.
Ahmed Musa da Abdullahi Shehu da Onazi dukkaninsu suna da shekara 25 a bana da suka wakilci Najeriya a Rasha amma kafin gasar cin kofin duniya a 2022, zai kasance 'yan wasan suna hararar 30.
Musa wanda ya zura kwallaye biyu da Najeriya ta doke Iceland, shi ne dan kwallon da ya fi ci wa kasar kwallaye a gasar kofin duniya.
Damar sake zuwa gasar cin kofin duniya ga Ahmed Musa da Abdullahi Shehu za ta dogara ne da rawar da suke taka wa a matakin kulub.
Wadanda shekarunsu ya ja
Babu shakka akwai wadanda shekarunsu suka ja, kuma daga dukkan alamu azama da kyan wasansu ma ya fara ja baya.
A don haka zai yi wuya a sake ganinsu a gasar kofin duniya a matsayin 'yan wasa.

John Mikel Obi

Kaftin din Super Eagles John Mikel Obi mai shekara 31 shi ne na biyu mafi tsufa a tawagar 'yan wasan da suka wakilci Najeriya a Rasha.
Mikel ya buga wa Najeriya wasa 85 tare da cin kwallaye 6. Ya lashe wa Najeriya kofin Afirka da tagulla a wasannin Olympic a Rio 2016.
Ana ganin nan da dan lokaci tsohon dan wasan na Chelsea zai sanar da yin ritaya daga buga wa Najeriya wasa.

Odion Ighalo

Ighalo da ke taka leda a kulub din Changchun Yatai na China zai yi wahala ya sake zuwa gasar cin kofin duniya.
Dan wasan na gaba yana shekara 29, ya wakilci Najeriya a Rasha, kuma kafin 2022 dan wasan ya haura 33.
Tsohon dan wasan na Watford ta Ingila ya ci wa Najeriya kwallaye 4 a wasanni 22 da ya bugawa kasar.

Leon Balogun

Karo na biyu ke nan da Balogon ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya.
Dan wasan na baya da ke taka leda a kungilar Mainz ta Jamus ya wakilci kasar a Rasha yana da shekara 30.
Balogun wanda aka haifa a Jamus, ya buga wa Najeriya wasa 22 amma ba tare da ya ci kwallo a raga ba.
Damarsa ta sake wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya za ta dogara ne da rawar da zai ci gaba da taka wa a wasannin Najeriya da kuma kulub dinsa.

Ikechukwu Ezenwa

Zai yi wahala mai tsaron raga Ezenwa mai shekara 29 ya sake wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya.
Ezenwa wanda ya taimakawa Najeriya a wasannin samun gurbi a Rasha, ya fara ganin makomarsa tun kafin fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya.
Ezenwa da ke tsaron ragar Ifeanyi Ubah ta Najeriya an ajiye shi ne a benci a dukkanin wasannin da Najeriya ta buga a Rasha.
Golan Deportivo La Coruna, Francis Ozoho mai shekara 19 ne aka ba dama a maimakon Ezenwa da Akpeyi.

Daniel Akpeyi

Mai tsaron ragar kungiyar Chippa United ta Afirka ta kudu Daniel Akpeyi mai shekara 32 shi ne mafi tsufa a tawagar Super Eagles a Rasha.
Duk da cewa Akpeyi ya samu damar zuwa Rasha amma har aka fitar da Najeriya yana benci.
Akpeyi wanda ya taba wakiltar Najeriya a matsayin mai tsaron raga a wasannin Olympics a 2016 yana da wahala ya sake zuwa gasar cin kofin duniya.

Tuesday, 26 June 2018

Abubuwa Biyar Da Nigeria Ke Bugata Domin Doke Argentina

Abubuwa Biyar Da Nigeria Ke Bugata Domin Doke Argentina

Najeriya da Argentina za su fafata a wasansu na karshe na rukunin D na gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018.
Wasan shi ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar, kuma hankalin masu kaunar kwallon kafa a duniya ya karkata a kansu.

Sai Argentina ta doke Najeriya, san nan Croatia ta ci Iceland ko kuma sun tashi canjaras, san nan Argentina za ta samu zuwa zagaye na gaba.

Najeriya kuma na bukatar ta doke Argentina ko kuma ta tashi canjaras da ita, sannan ta yi fatan kada Iceland ta yi nasara a kan Croatia domin zuwa zagaye na gaba.
Ga abubuwan da nake ganin ya kamata 'yan Super Eagles su yi domin samun nasara:1. Kai hare-hare


Najeriya na bukatar fara wasan da kai hare-hare saboda 'yan magana kan ce mafi kyawun tsaro shi ne kai hari.
Idan suka zauna a gida ba sa kai hari, 'yan Argentina za su samu damar kame tsakiyar fili kuma wannan zai ba su damar rike kwallo fiye da Najeriya, duk da cewa ana hasashen dama za su rike fiye da su din.
Idan hakan ta faru, to Argentina za ta samu damar kai hare-hare da wahalar da Najeriya sosai.
Amma idan Super Eagles ta sa kaimi, ta fito aka fafata, amma tare da yin taka-tsan-tsan, to za ta iya cin kwallo ta hannun 'yan wasanta irinsu Ahmed Musa da Victor Moses da sauransu.

2. Rashin sake

Croatia ta yi amfani da dabaru ciki har da killace madugun Argentina, Lionel Messi, a wasan da ta doke su da ci 3-0.
Najeriya na bukatar irin wannan dabarar saboda tawagar Argentina an gina ta ne a kan Messi.
Sai dai kocin Argentina, Jorge Sampaoli, zai iya sauya salon wasa, a don haka dole ne Super Eagles su kula da dukkan 'yan wasan Argentina musamman na gaba da kuma tsakiya (masu shirya kwallo).
Yin hakan zai taimaka musu wurin dakile kaifin Messi ko da kuwa ba su iya rufe shi kwata-kwata ba, wanda dama abu ne mai matukar wahala.

3. Da'a

Ya kamata 'yan wasan Najeriya su mayar da hankali wurin bin dokokin wasa musamman wadanda suka jibinci keta.
Argentina na da 'yan wasa da suka iya yanka kamar su Lionel Messi da sauransu.
Yi wa irin wadannan 'yan wasan keta ka iya janyo wa Najeriya fenareti ko kuma jan kati, abin da zai iya jawo tawagar koma baya.
A don haka 'yan wasan baya irinsu Leon Balogun da Ndidi na bukatar su yi taka-tsan-tsan kan yadda za su tunkuri wasan, ganin cewa sun jawo wa kansu fanareti a duka wasa biyun da suka yi a baya.

4. Mayar da hankali har zuwa karshen wasa

A gasar cin kofin duniya ta bana wasu kasashen da suka yi kokari tun daga farkon wasa sun sha kaye domin sakacin da suka yi a karshe.
Daya daga cikin irin wadannan kasashen ita ce Sweden wadda ta rike Jamus ana kunnen doki har zuwa minti na 95, inda Jamus ta samu ta zura mata kwallo daya a raga abin da ya sa ta sha kaye a wasan.

Irin wannan ci a kurarren lokaci ka iya saka Najeriya a wani mawuyacin hali, kamar yadda Italiya ta fitar da kasar a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.
A don haka wajibi su nutsu, kada su karar da kuzarinsu a farko-farkon wasa, kuma kada su bari Argentina ta gajiyar da su.

5. Cin kwallo


Babu yadda za a yi nasara a wasa ba tare da zura kwallo a raga ba. Ya kamata 'yan wasan gaban Najeriya Ahmed Musa da Kelechi Iheanacho da Kuma Victor Moses su nemi ci ido rufe.
Babu shakka idan suka matsa kaimi, za su iya samun damar zura kwallo domin 'yan bayan Argentina suna da rauni kamar yadda wasanninsu na baya suka nuna.
Idan Super Eagles ta yi nasara, wannan zai sa ta samu zuwa zagaye na biyu a gasar.
Hakazalika, zai sa Najeriya ta rama kadan daga cikin shan kayen da ta sha a hannun Argentina a baya.

Sau hudu Najeriya na shan kaye a hannun Argentina a gasar kofin duniya- ko a wannan karon Super Eagles za su taka mata burki?

Monday, 25 June 2018

Magoya Bayan Club Din Chelsea Suna Son kungiyar ta Sayo  Ahmed Musa

Magoya Bayan Club Din Chelsea Suna Son kungiyar ta Sayo Ahmed Musa

Magoya bayan Chelsea da suka kalli wasan da Najeriya ta lallasa kasar Iceland daci 2-0 ta hannun dan wasa Ahmad Musa sun bayyana burinsu na ganin kungiyar ta siyi dan wasan daga kungiyarsa ta Leceister City.

Magoya bayan kungiyar sun bayyana hakane a shafukansu na sada zumunta na tiwita inda suka dinga yabon dan wasan suna bayyana cewa kungiyar ta siyar da Morata ta siyo Musa domin zai taimakawa kungiyar sosai.

Ahmad Musa dai wanda a yanzu haka yake zaman aro a kungiyar kwallon kafa CSKA Moscow daga kungiyar Leceister City ya zura kwallayen ne a wasa na biyu da kasar Najeriya ta fafata a gasar cin kofin duniya.

Duk da cewa dan wasan yakasa buga abin azo agani a kungiyar ta Leceister City bayan kudin da ta kashe fam miliyan 15 wajen siyansa daga kungiyar CSKA Moscow din a shekara ta 2016 amma mai koyar da tawagar yan wasan Super Eagles ta Najeriya yafara buga wasan dashi a wasan da aka fafata a ranar Juma’a.

Musa dai yayi amfani da kwarewa da gogewa a kwallayen daya zura a wasan musamman a kwallon farko da yayi amfani da kwarewa yayinda kwallo ta biyu kuma yayi amfani da gudu da koma iya wuce yan kwallo.

Ya taba bugawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da kuma BBB Benlo dake kasar Holland sannan kuma ya taba buga gasar ta cin kofin duniya a shekara ta 2014 inda anan ma ya zura kwallaye biyu a wasan Najeriya da kasar Argentina.
Akwai Yiyuwar Mikel Obi Ya buga wasa Da Argentina Saboda Rauni

Akwai Yiyuwar Mikel Obi Ya buga wasa Da Argentina Saboda Rauni

Tawagar Likitocin Super Eagles da ke wakiltan Najeriya a gasar cin kofin duniya a Rasha na aiki ba-dare-ba-rana donin ganin Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar buga wasan da Najeriya za ta yi da Argentina a gobe Talata.
Binciken likitocin ya nuna cewa, dan wasan ya samu rauni a wuyar hannunsa a dai dai lokacin da ake dab da tashi wasan da Najeriya ta casa Iceland da ci 2-0 a ranar jumm’ar da ta gabata.

Koda dai Kocin Super Eagles, Gernot Rohr na kallon runin a matsayin karami wanda kuma ba zai hana Obi buga wasan da Argentina ba.
Rohr ya kuma bukaci ‘yan wasan nasa da su rika dukan kwallo da zaran sun hangi wata kafa a dab da ragar Argentina.

Rohr ya ce, wasan na gobe ba zai kasance mai sauki ba, kuma za su yi fafatawar ce da burin samun nasara amma ba canjaras ba kamar yadda wasu ke akalla fata.
Masharhanta kan harkokin wasanni na kallon wasan a matsayin mai zafi kwarai, lura da cewa Argentina na neman nasara ruwa a jallo don tsallakawa matakin gaba, yayin da ita ma Najeriya za ta yi kokarin samun karin maki.