Showing posts with label Fadakarwa. Show all posts
Showing posts with label Fadakarwa. Show all posts

Thursday, 7 June 2018

Tashin Hankali Wannan Masifa A cikin Watan Ramadan : Malam Isah Ali Pantami Yayi Kuka Ya Zubar Da Hawaye

Tashin Hankali Wannan Masifa A cikin Watan Ramadan : Malam Isah Ali Pantami Yayi Kuka Ya Zubar Da HawayeDaga Datti Assalafiy

A tafsirin Al-Qur'ani Maigirma wanda Babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami yake gabatarwa a darasin jiya Talata 20 ga watan Ramadan, wani bawan Allah  ya rubuto takarda yake rokon Malam akan ya yiwa 'dan uwansa nasiha sakamakon bijirewa mahaifiyarsa da yayi har yace babu shi babu ita, kuma sunyi iya kokarin da zasuyi domin yaje ya baiwa mahaifiyarsa hakuri amma yaki

Da malam ya tashi gabatar masa da nasiha sai ya fara da cewa ashe har ana iya yin fada da iyaye a kaurace musu?
Babbar magana!, bil hakki ni dai tun da muka shiga Ramadan ban taba jin wata fitina da ta kai wannan girma ba ace mutum da iyayensa yayi fada har an rokeshi don ya basu hakuri amma yaki

Daga nan Malam ya kawo bayanan ayoyin Qur'ani da Hadisai na Annabi (saw) wanda suke nuni da falalar yiwa iyaye biyayya musamman mahaifiya, sannan ya kawo wata kissa wacce daga karshe sai da Malam ya fashe da kuka

Kissar itace kamar haka:
A zamanin sahabbai wani mutum ne yana neman budurwa sai ya kasheta saboda taki aurensa, sai yazo wajen Ibnu Abbas (ra) sai yace masa nayi zunubi maigirma, ban san me zanyi Allah ya gafarta min ba, ban san me zanyi ba a rayuwata na shiga damuwa

Sai Ibnu Abbas ya tambayeshi mai ya faru gareka? Sai yace wallahi budurwa nake nema taki aure na sai na kashe ta, Ibnu Abbas yace Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un haka ka aikata? yace eh!, yanzu don Allah yaya za'ayi Allah Ya yafe min?

Tambayar farko da Ibnu Abbas ya masa shine shin mahaifiyarka tana raye? sai mutumin yace masa a'a bata raye, sai Ibnu Abbas yayi shiru, bayan tsawon lokaci sai yace to kaje kayi ta tuba kayi ayyukan alheri.

Sai daliban Ibnu Abbas sukace masa me yasa ka tambayeshi ko mahaifiyarsa na raye kuma da yace bata raye sai kayi shiru?
Sai Ibnu Abbas yace Wallahi ban san wani aiki na nagarta da mutum zaiyi ya nemi gafarar Allah Ya yafe masa ba kamar BIYAYYA ZUWA GA MAHAIFIYA, yace ban san wani aikin dake kaffara na zunnubai a duniya ba kamar biyayyan da mutum yake yiwa Mahaifiyarsa.." daga nan wajen ne sai Malam Isah Ali Pantami ya fashe da kuka har ma ya kasa cigaba da bayanin kawai sai ya umarci Alarammansa Malam Abdullahi Abba Zaria ya karanto ayoyin Qur'ani.

Ni kuma nace Malam Ya tuna da tashi mahaifiyar wacce Allah Yayiwa rasuwa watannin baya shi yasa yake kuka, ga wani kuma tashi mahaifiyar tana raye amma yayi fushi da ita (Allah Ya sauwake)

Wanda yake da bukatar karatun ya nemi tafsirin Qur'ani na ranar 20 ga watan Ramadan wanda ya gabata jiya talata

Gaskiya duk wanda Mahaifiyarshi take raye ashe yana da wata babban alfarma wanda zai iya gyara lahirarsa da ita.
Mu kyautatawa iyayenmu da suke raye domin mu gama da duniya lafiya mu kuma hadu da Allah lafiya

Allah Ka shiryar damu ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu, wadanda suka rasa nasu iyayen Allah Ka jikansu Ka basu Aljannah don RahamarKa Amin

Saturday, 12 May 2018

Yadda Ake Gyaran Jiki A Gargajiyance —Muhibbat

Yadda Ake Gyaran Jiki A Gargajiyance —Muhibbat

Masu karin magana sukan ce, ‘ba a tauna taura biyu a lokaci guda’, ko kuma a ce ba a saka karfe biyu a wuta da nufin tada komadar kowanne kuma a lokaci guda. Sai dai za mu iya cewa a wannan zamanin ga dukkan alamu akwai wadanda suke da basira ta tauna taura biyu a lokaci daya. Bakuwarmu ta Adon Gari a wannan makon kwararriya ce wajen gyaran jiki ta ingantacciyar hanyar amfani da kayan gargajiya. Sannan jaruma ce da ta hada manyan ayyuka da take yi a rayuwarta. Baya ga kasancewarta matar aure wadda take hidimar kula da iyali, har ila yau darakta ce, furodusa (mai shirya) fim ce sannan ga wasu ayyuka na daban da ta hada da suka shafi harkokin kasuwanci. Domin jin yadda take aiwatar da wadannan ayyuka da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarta, a karanta tattaunawar da muka yi da ita tun daga farko har zuwa karshe:

Za mu so ki fada mana Sunanki da cikaken tarihin rayuwarki?

Sunana Muhibbat Abdulsalam, Mrs Giggs. An haife ni a garin Kaduna, kuma na yi karatuna a Kaduna na boko da na Addini.

Wace shekara kika fara fim kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga harkar?

Na fara fim a karshen 2000 da fim din Imani. Da farko dai sha’awar sana’ar fim ne ya shigo da ni, asali ma fim din Sangaya ne ya shiga raina sosai.

A matsayinki ta matar aure kuma jaruma kuma daracta kuma ’yar kasuwa, yaya kike iya tafiyar da harkarki da kuma kula da iyalinki?

Gaskiya, ba abu ne mai sauki ba amma dai ina bakin kokarina. Kusan in ce, sana’o’ina da dan yawa, Ina rubuta labari, Ina sarrafawa, Ina yin kwalliya ta amare, muna abincin biki, muna gyara jikin amare da sauransu, kawai ni ban yarda da zaman banza ba, kuma mafi yawancin ayyuka na a gida nake yin su, sai dai idan zanyi tafiya ne, amma ina da mai kulan min da yara. Alhamdu lillah muji na taimaka min ta ~angaren kasuwancina da kuma kula da yara idan bana nan.

Wane ci gaba kike ganin an samu yanzu a harkan fim?

An samu cigaba ta bangaren kayan aiki sosai.
Wanw kira za ki yi ga mata masu son su shiga harkar, kuma yaya kike ganin makomar rayuwar mace a harkar.
Shawarar ita ce ba a harkar fim kadai ba, a kowace irin sana’a ce, yana da kyau mace ta rike mutuncinta, dan kuwa ba ki san waye mujinki ba, ba ki san a ina mujinki yake ba. Makomar mace a harkar fim kuwa kamar yadda na fada ne, idan kika rike mutuncin kanki, inshaa Allah makomarki za ta zama mai kyau. Kuma kar mace ta tsaya a fim kadai, ta hada da karatu da kuma koyon sana’ar hannu.

Bari mu dan koma amsarki ta sama. Ko za ki fada mana yadda kike yin gyran jiki da abincin biki da kika ce?

Gyara jiki ina yin sa ne da kayan gargajiya, kamar su kurkur, dilka, garin alkama, madara, lemon tsami da sauransu.

Idan aiki ya same ki a wani gari daban ta yaya kike raba kanki, a matsayinki na mai sarrafawa kuma da ba da umurni. Za ki iya barin ’ya’yanki mata su fito a fim?

Ya danganta, gaskiya aikin da ya fi romo shi nake yi. A da idan na samu aikin gyaran jiki a wani gari ina zuwa, amma yanzu ba na zuwa, sai dai mutum ya sayi kayan gyaran jikin a wurina sai in yi masa bayanin yadda zai yi amfani da shi. Idan suna son yin zan bar su, amma gaskiya ina so su yi karatu sosai kamar yadda na samu ilimi. Kuma ni na dauki fim sana’a babba.

Yanzu Misali mace tana son shiga harkan fim ta hanunki ya za ta yi ta same ki?

Ayya! Ni ba a shiga fim ta hanyata. Za ta je dai ta yi rajista da kungiyar ‘yan fim, idan sun tantance kuma sun ba ta kati sheda, shi ke nan, to idan har akwai irin rawar da za ta taka a tsarin labarina sai a saka ta.

Ko akwai wani sako da kike son fada da ba mu tambaye ki ba?

Sakon shi ne, dan Allah masoya a dinga taimaka mana da addu’a, a daina jifar mu da munanan kalmomi.
Mun gode kwarai da hadin kan da kika ba mu.
Ni ma na gode, shukuran jazeela.


Sources:leadershipayau.com

Wednesday, 9 May 2018

Kwalliya Mata A Mahangar Musulunci Daga Sheikh Kabiru Haruna Muhammad Gombe

Kwalliya Mata A Mahangar Musulunci Daga Sheikh Kabiru Haruna Muhammad Gombe

SHEIKH MUHAMMADU KABIRU HARUNA GOMBE
KWALLIYAR MATA A MAHANGAR MUSULUNCI (female only)
Sakon da Annabi Muhd (S.A.W) ya zo da shi, bai takaitu kan alaka tsakanin bawa da ubangijinsa ba kawai, ya tsallaka har zuwa ga yadda bawa zai kula da gangar jikinsa da kuma yadda zai gudanar da zamantakewa da sauran halittun Duniya.
Mata sune Allah ya bada shaida a kansu cewa: An gina dabi’arsu kan son kawa an kuma tayar da su a cikinta, sannan kuma Musulunci ya karfafi mabiyansa kan cancada ado yayin zuwa masallaci, ya kuma tuhumci wanda yake tsammanin cewa ba dabi’ace ta mumunai ba. Allah yace: “ KA CE:
WANENE YA HARAMTA KAWAR(kwalliya) DA ALLAH YA FITARWA BAYINSA”
Manzon Allah kuma ya karfafi haka cikin Hadisansa yace: ‘’ Allah mai kyau ne, yana son Abu mai kyau”.

Abdullahi dan Abbas ya na cewa: “ Na kasance ina cancada ado wa matata kamar yadda take cancada min”.
Musulunci shine addinin da ya sanya wanka da kawar da kazanta daga jikin musulmi a matsayin ibada, kamar su; yanke kumba, tsige gashin hammata, aske gashin gaba, tsabtace hakora{Aswaki},balle sanya turare, shafa mai dss.

Amma musulunci bai bar wannan Ibada kara zube ba, sai da ya sanyawa ‘yan uwa Mata wassu ka’idoji a matsayin yanda ya kamata su gudanar da ita.
‘Yar uwata, Duk da cewa kwlliya addini ne amma sai a ringa kulawa da wadannan abubuwa:
• Kada kwalliyarki tai kama da na Matan Arna, don Manzon Allah yace:” wanda yai kama da wassu yana tare da su.”

• Kar kiyi kwalliyar da za mai da ke kamar Maza. Manzon Allah yace: “Allah ya tsinewa mai kama da Maza cikin Mata”.
• Kar Kwalliyar ta kunshi canja halittar Allah, kamar kulla gashinki da wani gashi, ko kuma canza fatar jikinki, ko kuma bankare tsakanin hakoranki don fitar da wushirya ko kuma yin zane a fuska ko a wani bangare na jikinki. Amma gyara halittar da Allah yai miki ba Laifi, kamar sa gashi ya yi santsi, ko mikar dashi, ko sa masa abinda zai kara tofar da shi.
• Kada ya zamanto cikinkin kwalliyar akwai barnatar da dukiya, Allah yace: “ ku ci ku sha, kar ku barnatar da dukiya, Allah ba ya son masu Ballagaza”

• Kar ya zamanto akwai bata lokaci, Ta yanda mafi yawan lokacinki zai tafi ne cikin kwalliya.
• Kada wannan kwalliyar ta zamanto tana kunshe da cutarwa wa jikinki, domin jikinki yana da hakki a kanki, wannan cutarwar yanzu yanzu ne ko kuma sai daga baya.
• Kar ya zama cikin kayan da aka kera wannan abin kwalliyar yana kunshe da najasa.
• Wanda kike fatar kwalliyar ta burgeshi ya zamanto mjinki, ba ki ringa rabawa Jama’a kirarki fi sabilil Shaidan ba.

Nana A’sha ta kasance tana da kayayyaki na musamman da take cabawa Manzon Allah ado dashi, kamar yadda Manzon Allah yace cikin ingantaccen hadisi: “ Duk wanda Allah ya bashi gashi ya kula dashi” Tirmizi cikin Shama’ilil Muhammadiyya.
Zan rufe da Hadisin da ke cewa:

“INA JAWO HANKALINKU DA SANYA TOZALIN ISMID LOKACIN BARCI, DOMIN YANA KARA GANI YANA KUMA TOFAR DA GASHI”

Sunday, 31 December 2017

Video : Kalli Bidiyon Yan Shi'a suna rera waka a coci lokacin kirsimati

Video : Kalli Bidiyon Yan Shi'a suna rera waka a coci lokacin kirsimati

Lallai yan shi'a sun nunawa duniya cewa su musulmuƙa ne saboda taya zaka raira waka a lokacin bukin sallar addinin da baka so a duniya ko baka tare da su. Waka ta nuna so da kauna ga mutum yana nuna kana sonsa dari bisa dari. 

Saboda daman a lokacin da shugabansu zazakky ya sha ruwan harsashe, shuganan can yaje na jajanta mishi da jama'arsa sai yake cewa daman su da su dan jumma ne da dan jummai to gashi abun ya fito a fili. 

Sai ku saukar da wannan video domin kallon suna rera wannam wakar a cikin coci ranar kirsimati. 


Download video here

Tuesday, 19 December 2017

NASIHOHI 35  Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

NASIHOHI 35 Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


1- ka fara yininka da sallar asubahi da azkar domin samun rabo da tsira.

2- ka zarce da istgfari har sai shaidan ya debe
tsammanin samun rabo a jikinka.

3-kar ka daina addu'a dumin itace igiyar tsira

4-ka tuna cewa mala'iku suna rubuta maganganunka.

5-kyawun yatsu shine ka rika qidaya TASBIH dasu.

6- idan ka shiga damuwa da qunci kace" la ila ha illallah".

7- ka sayi addu'ar talakawa da soyayyan marayu da kudadenka.

8-doguwar sujada 1 wanda aka yita saboda tsoron ALLAH yafi maka bene da aka gina na zinari.

9- ka tauna magana kafin kafadeta domin tana iya zama ajalinka.

10- ka guji addu'ar wanda aka zalunta da hawayen wanda aka hana.

11- kafin ka karanta jaridu da mujallu mai zai hana.kafara karanta alqur'ani.

12- ka zama dalilin gyaruwan iyalanka.

13- ka tilastawa ranka wurin bin dokokin Allah ,
domin ita rai tana umarni ne da sabon Allah.

14- kafin tsufar iyayanka ka daure ka samu yardarsu.

15-tsoffin tufafinka sababbi ne a wurin talakawa.

16- kar kayi fushi , domin rayuwa kadan ce ba kamar yadda kake tsammani ba.

17- tare dakai akwai wanda yafi kowa qarfi yafi kowa wadata, shine Allah.

18- kar ka rufe qofar tuba saboda sabon Allah.
19- sallah itace mafi alkhairin abun da zata taimakeka akan musibu da wahalhalu.

20- ka nisanci munanan zato, zaka huta kuma zaka hutar.

21- dalilin kowane damuwa juyawa Allah bayane, ka juyo zuwa gareshi mana.

22-kayi sallah irin wacce kakeso a shigar dakai qabari tare da ita.

23- idan kaji wanda yake gulma , kace dashi: yaji tsoron Allah.

24-ka dawwamar da kanka wurin karanta suratul MULK domin tana tseratarwa.

25- wanda aka hana( yayi hasara) shine wanda aka hanawa sallar dake cike da tsoron Allah , da idon dake zubar da hawaye.

26- kar ka cutar da bayin Allah nagari wadanda suka shagaltu da bautar Allah.

27- ka sanya soyayyar ka duka zuwa ga Allah da manzonsa.

28- ka yafewa wanda yayi gulmarka, domin ya baka kyautar kyakyawan aikinsa ne.

29- Sallah da ambaton Allah da karatun alqur'ani alqawurane masu nauyi akan qirjinka.

30- duk wanda ya tuna da zafin wuta zai iya hakuri akan sabon Allah .

31- indai ana dare gari yana wayewa, to watarana sai labari tsanani zai zama sauqi.

32- ka nisanci ANCE-KACE ( jita-jita) domin kai game da ayyuka kamar dutsene.

33- kayi sallah da tsoron Allah , domin duk abun da zakayi bayan sallar bai kai sallah ba.

34- ka sanya alqur'ani daf dakai , domin karanta aya daya acikinsa yafimaka duniya da abun dake cikinta.

35- rayuwa akwai dadi, mafi dadin rayuwa shine kaganka da iimaninka.
________________________________
ALLAH Yasa Mudace!
____________________________