Showing posts with label Addini. Show all posts
Showing posts with label Addini. Show all posts

Monday, 24 September 2018

Hadarin zama Da Mace Daya -  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hadarin zama Da Mace Daya - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.

ILLOLI GA MAGIDANCI.
1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida.
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.

ILLOLI GA SU MATAN.
1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida,  yaran gida da ita ma kanta.
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya.
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa.
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.

ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu.
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma.
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.
WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA,
DA FATAN MAGIDANTA ZASU GANE,
SU KUMA MATA ZA SU TAIMAKAWA JUNANSU WAJEN TUNAWA MAI GIDA YA QARA AURE.

Wednesday, 12 September 2018

Fadakarwa Ga Masu Shiga Facebook -Mal.Aminu Ibrahim Daurawa

Fadakarwa Ga Masu Shiga Facebook -Mal.Aminu Ibrahim Daurawa


Face book wata hanya ce ta gani, da saurare, da karantawa, da
rubutawa, da yadawa.
ka tabbatar, da jinka da ganinka, da rubutunka, da
karantawarka, da
abinda ka yada, Allah zai tambayeka ranar Alkiyama, Wasu suna ganin tunda su kadai,
suke kamar babu, mai ganin su sai suyi abinda suka ga dama, alhalin Allah yana ganin su.

ga shawarwari domin amfanuwa:
(1) mu kiyaye
idanuwanmu daga kallon batsa.
(2)  Umarni da kyawawan aiyuka da hani da munana.
(3) duk abin zamu rubuta mu tabbatar da muna da cikkakiyar hujja ta ilmi.
(4) mu daina yawan bayar da labarin abinda ya shafemu, na yau da kullum, kamar yanzu na tashi,
yanzu ina cin abinci yanzu kaza da kaza, duk wannan bai dace ba.
(5) 'kulla abota da
mutumin da bakasan ko waye ba.
(6) yada jita jita, da
kanzan kurege, da 'kage da sharri, da
wani ko wasu.
(7)  kiyaye isgili da yiwa  wata kabila ko wani yare, domin
bakasan yadda wannan mutunen
sukeji ba.
(8) kula da lokaci,
domin wasu suna wace gona da iri
amfani da face book
(9)  masu kawo wani
labari mara kan gado, kuma su zagi, ko
tsinewa wanda yaki taya su abin, kamar duk wanda baice kaza ba Allah ya yi masa kaza.
(10) Yada kalaman batsa, da hotunan batsa, da maza masu
shigowa da hotunan mata, da kuma mata masu shigowa da
hotunan mata, da masu daukan haton mace batare da sanin ta ba su yada a face book Duk wadannan abubuwa suna faruwa da fatan zamu kiyaye,

Dama Mata Zasu Karanta Wannan Gajeren Tarihin Na Nana Fatima (RA)

Dama Mata Zasu Karanta Wannan Gajeren Tarihin Na Nana Fatima (RA)Manzon Allah (Saww) ya ce, Fatima Shugabar mataye ce baki daya. Sai aka tambaye shi, Ya Manzon Allah (Saww) ita Kuma Nana Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” Shin ko kun san dalilin da yasa ta samu irin wannan babban matsayi da girma?

An ruwaito hadisi daga Jabir bin Abdullahi Al’ansari (RA) ya ce; Mun yi Sallar Asar tare da Manzon Allah (Saww), bayan Mun idar da Sallah muna zaune tare da Manzon Allah (Saww), sai ga wani Dattijo ya zo Kai tsaye sai ya je wajen Manzon Allah (Saww) tare da yi masa bayanin halin da yake ciki na kuncin rayuwa na rashin abinci da tufafi da kuma kudi.

Sai Manzon Allah (saww) ya ce masa; “Ga shi kuwa ba ni da wani abu da zan ba ka” Sai ya ce masa; “Amma Ka tafi gidan Fatima”. 

Wannan Dattijo sai ya kama hanya zuwa gidan Sayyida Fatima (RA) da ya je gidan ya yi sallama.

Bayan haka ya shida wa Sayyida Fatima (RA) ga halin da yake ciki na rashin abinci da tufafi da kuma kuddi.

A lokacin da ya zo Nana Fatima ita ma ba ta da shi, saboda haka sai ta je ta dauko shimfidar 'ya'yanta (Wato Hasan da Husain), ta ce ga shi ya je ya sayar domin ya biya bukatarsa.

Sai Dattijon ya ce shi ba zai amsa ba, domin shi a tunaninsa wannan shinfidar ba zatayi kima ba. Kasancewae ya raina wannan abin da aka ba shi, sai Nana Fatima ta shiga gida ta debe abin wuyanta, wato sarka, ta kawo masa.

Sai ya amsa, bai tsaya ko’ina ba sai wajen Manzon Allah (Saww), ya same shi yana zaune tare da Sahabbai, ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) Fatima ta ba ni
wannan sarkar a kan in sayar domin in biya bukatuna”.

Nan da nan Sai Manzon Allah (Saww) ya fashe da kuka, ya ce yaya ko ba za ka samu biyan bukata ba, alhali Fatima ’yar Muhammad Shugabar mataye ta ba ka.

Sai Ammar bin Yasir (RA) ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) ka ba ni izinin sayen wannan abin wuyan”. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa yana iya saye.

Sai Ammar ya tambayi wannan Dattijon a kan nawa zai sayar masa da sakar? Sai ya ce masa; “Ni dai abin da nake bukata kayan abinci da tufa ko da kuwa daya ne, da kuma Dinare, shi ma ko da daya ne da zai kai ni garinmu”.

Sai Ammar ya hada masa kayayyakin abinci da kuma tufafi da kuma dabbar da zai hau zuwa garinsu, ya kuma ba shi kudi Dinare 20.

Bayan haka sai shi Dattijon ya zo wajen Manzon Allah (Saww), sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa; “Ka samu abinci da tufan?” Sai Dattijon ya ce; “Ya
Manzon Allah (Saww) ai ni yanzu na zama mawadaci”.

Saboda farin ciki da jin dadi, kafin ya bar wajen zuwa kauyensu, sai da ya yi addu’a, ya ce; “Ya Allah! Wanda babu wani abin bauta in ba shi ba, ka ba Fatima abin da ido bai ta'ba gani ba, kuma kunne bai ta'ba ji ba”.

Bayan haka, Ammar bin Yasir daya sayi wannan sarka, ya sa mata turare na Almiski ya nade ta a wani kyalle mai kyau ya ba Bawansa ya kai wa Manzon Allah (Saww). sarkar da Bawan, duk ya ba shi.

Daya isa wajen Manzon Allah (Saww) ya fada masa sakon. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce je ka kai wa Fatima sarkar da  wannan Bawa. Ya je wajen nana Fatima ta amshi sarkar, shi kuma Bawan, ta ’yanta shi.

Lokacin da Manzon Allah (Saww) ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce; “Wannan sarka mai albarka ta biya bukatar mabukaci (wato Dattijo) ta kuma ‘yanta bawa, ta kuma koma hannun mai ita.

Bayan duk irin wannan kyauta da Nana fatima keyi Kuma bayan kasancewarta 'yar Shugaban halitta (saww), amma gidan Mijinta Sayyidina Aliyu (RA) Sai da hannunta yayi kanta akan aikin da take yi.

Nana fatima ta kasance me biyayyah Sau da kafa a gurin mijinta kuma ta kasance mai kyauta.

A rayuwar Sayyidina Aliyu (RA) yayi aure-aure amma bayan rasuwarta, ba komai ya bata wannan matsayin ba face ayukkan da take na alkheri tare da kyautatawa mijinta.

Babu shakkah ko kinada 'yar aiki yana da kyau ki ware wa kanki wani girki wanda zaki rika dafawa mijinki da kan ki domin kara daukaka darajarki a wajensa da kuma wajen Allah (swt).

Ya Allah ka karawa Nana Fatima daraja kuma ka yi jinkai ga sauran matan da suka kaikwayi halayenta.

Wednesday, 5 September 2018

Ya Zama Wajibi Shugaba Muhammadu Buhari Ya Wadata 'Yan Nijeriya Da Abinci, Domin Ba A Hakurin Zama Da Yunwa" - Inji Dr Ahmad Ibrahim Buk

Ya Zama Wajibi Shugaba Muhammadu Buhari Ya Wadata 'Yan Nijeriya Da Abinci, Domin Ba A Hakurin Zama Da Yunwa" - Inji Dr Ahmad Ibrahim Buk


Daga Abdurrahman Abubakar Sada

Wannan kira ya fito ne daga bakin Babban Malamin Addinin Musulunci, Sheikh  Dr. Ahmad B.U.K Kano

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa: "Lallai a samarwa al'umma abinci, kar a bar ta cikin yunwa, matukar aka bar al'umma cikin yunwa, kafin lokacin da za a zo a samu dama a gyara idan an samu damar, wadansu sun tagayyara, wadansu sun tozarta, wadansu rayuwa ta halaka su, kuma duk sai Allah ya tambayi mutum, sai Allah ya tambaye ka wadannan mutane duk da ke karkashin ka, kasancewar ka kana siyasa, ko kasancewar ka kana mulki, ba abinda aka dauke ma cikin hakkoki na shari'ar Musulunci. Shi ya sa halin da al'umma suka kai yanzu na yunwa, ya kai na mutane fa suna tagayyara, wadansu dukiyar su sun karye".
.
"Wadanda ake maganar cewa sune suka kawo tabarbarewar tattalin arziki, wadansu da suke wahala yanzu suke halaka ba su da hannu a cikin wannan, to mene ne laifin su. Mutane sun kai yanzu, duk sa'adda aka yi barazana aka kori yara Makaranta, lokacin Jarabawa, sai kaga duk inda za a nemo kudi a biya su za a nemo a biya su, yanzu haka, jarabawar da ta wuce, yara in an kore su, da yaro ya je gida sai uban shi ya ce zauna yanzu ta ciki ake ba ta Makaranta ba, ba ta Kudin Makaranta ba, wani daga nan karatun ya tafi kenan ba shi ba daman Karatu".
.
"Shi ya sa abin da ake nema wajen masu mulki, wajen Shugaban Kasa Mai cikakken iko, nan zuwa sati (mako guda) duk inda Allah ya ba ka Mulki ka wadata su da abinci, duk karkashin mulkin ka inda Allah ya dora ka a kansu a ga ka wadata su da abinci, abinci ba ya daukan jinkiri a jira zuwa Lokaci kaza.
Shi ya sa Allah (Madaukakin Sarki) ya ce: "Allazi Ad'amahum Min Ju'in Wa Amana Hum Min Khauf", kashin bayan rayuwa abubuwa guda biyu ne; Aminci da Abin ci, Abin ci da Aminci, da'iman abubuwa guda biyu su ke tafiya".
.
"Shi ya sa mu na kyautata zato, muna fata kan nan zuwa sati insha Allahu, duk Nijeriya za ta cika da abinci, Shinkafa ta kara kudi, Masara ta kai inda ba ta kaiwa ba sai wannan Lokaci, kuma wadannan duk matsaloli ne Allah ya na kallon bayin sa".

"Zantuttukan da ke hana ruwa gudu su ne maganganun 'yan Siyasa, magana ce gaskiya, maimakon a fada wa Shugaba ya maida hankali ya yi, sai a maida shi Siyasa, ana suka ana zagi, wannan ba shi zai fishshe mu ba, wannan sai ya hana ma su son su fadi gaskiya ma ba za su iya fada ba, idan sun fada sai wadancan su ja zare, wannan ya fadi kaza wannan ya fadi kaza, shi kuma wanda ake son ya yi gyara din, ya san wadancan maganar banza ce su ke",
Sako Za Ta Isa Insha Allahu - Inji Dr. B.U.K.

Sunday, 19 August 2018

CANJA RANAR BABBAR SALLAH  Musulman Nijeriya Za Su Rana Azumi Daya Idan..., Cewar Sheikh Dahiru Bauchi

CANJA RANAR BABBAR SALLAH Musulman Nijeriya Za Su Rana Azumi Daya Idan..., Cewar Sheikh Dahiru Bauchi


Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce idan ya tabbata an ga watan Ramadan da ya wuce a yammacin Talata amma aka ki bayyana labarin ga Musulmin Nijeriya don a yi daidai da Saudiyya wajen daukar azumi to Musulmin Nijeriya za su biya azumi daya na ranar Laraba.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana haka ne lokacin da majiyarmu ta Aminiya ta tuntubi Shehin Malamin game da takaddamar da ta taso kan jikirta ranar Babbar Sallar bana, inda watan Zul-kida yana da kwana 28 Kwamitin Ganin Wata ya bayyana washegari 1 ga Zul-Hajji, don komawa aiki da ganin watan Saudiyya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, saboda wadanda alhakin sanar da ganin wata ke hannunsu a Najeriya ba addini suka karanta ba shi ya sa suke ganin saukin hadarin abin. “Da a ce sun karanta addini ne da sun san akwai Yaumi Shakki a lokacin da duniya ba ta hadu wajen kafofin watsa labarai ba. Na biyu da a ce an karanta addini da an san madala’in ganin watan ’yan Najeriya ba daya ne da na Saudiyya ba, saboda haka akan iya yin azumi daya zuwa biyu wani sa’in, kafin Saudiyya ta dauki azumi,” inji shi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, abin da ya kamata a gane filin samaniya na ko’ina daban ne, “Mukan dauki azumi a Najeriya in mun je Kaulaha sai mu cika azumi 30 su ba su ga wata ba, sai mu fada wa Shehu Ibrahim (Radiyallahu anhu) mu ce masa yaya za a yi mu mun cika azumi 30 kuma a nan kasar Senegal ba a ga wata ba? Sai Shehu ya ce mana, Shehu ya ce a Najeriya ku sai da kuka ga wata kuka dauka muka ce masa ce.

Sai ya ce to gobe ku kada ku yi azumi kuma kada ku sha ruwa, wato sai a ajiye niyyar azumin kuma ba za ku ci abinci ba. Wato ya zama kamar kamun baki, wato kamar a garinku kai ba ka ga wata ba gari ya waye aka tashi da azumi ka ga kai da ba ka ga wata ba, ba za ka sha ruwa ba don ana azumi kai kuma ba ka yi niyyar azumi ba, sai ka kama baki.

Haka in azuminka ya cika amma inda kake ba a ga wata ba sai ka kama baki ba azumi ba cin abinci. Allah ne Yake da kowane filin sama da ake ganin wata kuma kowane filin sama na kowace kasa da lokacin ganin watansa da Allah Ya sa.”

Shehin ya ce sai a ji wadansu suna cewa a dauki na Makka, alhali saman ganin watan Makka daban da na ganin watan Najeriya. “Idan lokacin ganin watanku ba daya ba ne dole ku saba da su a samu bambanci. Amma na Idin Layya nan ne ake bin kasar Makka don ba inda ake da Arfa sai Makka din don haka ba za mu yi Layya ba, ba za mu yi Idin Layya ba sai bayan sun yi Arfa,” inji shi.

Ya ce addini nassi ne a farko sannan imani ya biyo baya, sai hankali ya biyo bayan imani. “Amma a ilimin zamani hankali ne a gaba a cikin duk sha’anonin rayuwa. Idan aka dawo kan abin da ya shafi Najeriya da Saudiyya a kan watan Zul-Hajji a nan ana amfani da lissafin ganin watan Saudiyya ne don ita take da Arfa a duk duniya. Saboda haka kowa zai bar lissafinsa ya bi na Saudiyya saboda su suke da filin Arfa domin ranar 8 ga lissafinsu ake fita filin Muna don fara aikin Hajji.

Idan alhazai suka kwana ranar 9 su tafi filin Arfa idan sun dawo Muzdalifa suka kwana wayewar garin 10, sai duk duniya a tashi da Sallar Layya. Saboda haka lissafinsu ne ake amfani da shi a watan Zul-Hajji, saboda su suke da filin Arfa, sabanin watan Ramadan wanda ba sai an jira ganin Saudiyya kafin a dauka ba,” inji Shehin.

Sheikh dahiru Bauchi don haka idan aka yi Arfa ran 9 watan Zul-Hajji, ya zamo ke nan washegari dukan Musulmi su karrafa bakin Allah da suka yi Hajji suka hau Arfa, a yi yanka ranar goma ga watan Zul-Hajji, wannan yanka ana yin sa ne duk duniya don a karrama bakin Allah da suka yi Hajji sunan yankan Layya amma bakin Allah ake karramawa a yi Idi a gode wa Allah, ranar goma ga Zul-Hajji ranar Babbar Sallah.

Saturday, 11 August 2018

Ya Hallata Matar Aure Tayi Facebook- Sheikh Isah Ali Pantami

Ya Hallata Matar Aure Tayi Facebook- Sheikh Isah Ali Pantami

Shugaban hukumar kula da ci gaban fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Dokta Isa Ali Pantami ya ce ya halatta miji ya bar matarsa ta shiga shafukan sada zumunta, idan ba za ta saba wa dokokin addini ba
.
Ya shaida wa BBC haka ne a wata tattaunawa ta musamman ranar Talata, inda ya ce miji na iya hana matarsa shiga shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter da Instagram da Whatsapp da makamantansu "idan har za ta saba wasu hakkokin addinin musulunci."
Hakazalika ya kuma ce idan har a ka bi hanyoyin da suka dace, amfani da shafukan sada zumunta na iya shigar da mutum aljanna.


"Idan dai a manufofi na alheri ne, bai dace miji ya hana matarsa shiga shafukan sada zumunta ba," in ji shi.
Har ila yau ya ce bai kamata matar aure ta rika abokanta da mutanen da ba su dace ba a shafukan sada zumunta.
"Ta rika abokanta da kawayenta da suka yi karatu tare, ta tarbi abokanta da yayyanta da kannenta da kuma sauran 'yan uwanta na jini," kamar yadda ya ce

Tuesday, 31 July 2018

Tijjaniyya Ta Yi Hanun Riga Da ‘Yan Hakika, Inji Shaikh Dahiru Bauchi

Tijjaniyya Ta Yi Hanun Riga Da ‘Yan Hakika, Inji Shaikh Dahiru Bauchi

Shaikh Dahiru Usman Bauchi, Shararren Malamin addinin Islama ne a fadin Nijeriya dama Afrika baki daya, a gefe guda kuma shugaban darikar Tijjaniyya ne, a hirarsa da ‘yan jarida dangane da ‘yan hakika da ake cewa ‘yan darika ne, Shehin ya bayyana cewa, babu abun da ya hada ‘yan hakika da darika, domin ita dari babu wani haram da ta halasta, ya dai yi hanun riga da ‘yan hakika. KHALID IDRIS DOYA ya kasancewa a wajen ganawar ga kuma yadda hira ta kasance.

Akramallahu mene ne alakar Darika da ‘yan Hakika?

Ai ban sansu ba! amma an ce akwai wadansu mutane wadanda suke wasa da sallah suna wasa da matan mutane an ce koda Tijjaniyya suka soma ne, daga baya suka zarce suka kai wannan hakika din na raina musulunci, ba ruwanmu dasu, ba ruwansu damu. Su irin wadannan mutane, mutane wadanda shedan ya riga ya janyesu daga cikin yan Tijjaniyya daga cikin musulunci gabaki daya. wadannan mutane suna wasa da Sallah suna wasa da matan mutane wai ba komi, mu ‘yan Tijjaniyya dai muna gaya wa mutane a fili cewa Shehu Tijjani da ya kawo Darika abin da ya ce, idan ka ji labari an jingina wata magana ko wani abu daga gareni yake to ka aunashi da shari’a idan ya yi daidai ni na fada, in bai yi daidai ba ni ban fada ba’, Shehu Ibrahim Radiyallahu Anhu da ya gajesa ya ce to wannan fa Shehu Tijjani ya ce, mu yi ta karatu kenan, don in baka yi karatu ba yaya zaka yi ka gane gaskiya da rashin gaskiya cikin shari’a, Shehu Ibrahim yana cewa. “Na gode wa Allah cikin manyan alherorin da ya yi mini ya kiyaye mini zuciyata, ba za a ganni na karkata wurin abin da bai halatta cikin musulunci ba. Shin zina halal ne cikin Musulunci? Haramun ne babbar kaba’ira, wasa da sallah halal ne cikin Musulunci? Shi ma haramunne cikin Musulunci, saboda haka duk wanda ya ce shi almajirin Shehu ne to zamu duba mu gani yana bin hanyar Shehun, in suna sabawa shari’ar musulunci su ba almajiran Shehu bane don Shehu ba ya halatta haramun, don ita darikar Tijjaniyya ba wani abu sabo da ta kawo cikin shari’ar Musulunci, kuma ayyukan da Tijjaniyya ta kawo guda hudu ne daya sunan sa lazimi da ake yi safe da yamma, daya sunansa wazifa, daya kuma shi ne zikirin jumma’a sai kuma sharuddan da sai an fada maka ka yarda kafin a baka darikar, amma duk maganan daya shafi halal da haram Tijjaniyya nan ta samesu nan take binsu duk wanda ya canja haramun ya ce halal ne ya yi ridda ya karyata alkur’ani, ya karyata Manzon Allah (S) ba maganan darika ake masa ba wannan maganan ridda ake masa Allah ya ce, “Ko kusa da zina kar ku yi” kai kuma ka ce ba komi wannan riddance, haka kuma masu kamanta Shehu Ibrahim da Allah shi ma Ridda kun taba ganin Allah da Uwa da Uba? Shehu Ibrahim sunan mahaifinsa Abdullahi sunan mahaifiyarsa Aishatu, kuma ya rasu duk mutumin da yake da uwa da uba shi ba Allah bane.
 Kuma Allah yana mutuwa ne ? Allah rayayyene baya mutuwa, Ire-iren wadannan mutane a yi nesa dasu sun ridda su wadannan irin mutane ba ruwanmu da su, idan nace basa cikin musulunci ma na fadi gaskiya don sun karyata ayoyin alkur’ani da hadisan Manzon Allah (S).
Don ita Darika fa bayan mutum ya bi Malamansa sun koya masa alkur’ani, ya bi Malamai sun koya masa Ilimi sai kuma ya nemi Malamai masu gyaran zuciya, shi ya sa muka bi Shehu Ibrahim din kuma ya fi kowa kokari wajen bin shari’a da halalta halal da haramta haramun kamar yadda Allah da Annabi suka yi umurni.

Sojoji sun nusar da cewar ‘yan hakika sun bayyana a wasu sassa kuma ana dai cewa su ‘yan darika ne?

Sai su nemesu ta can domin suba ‘yan Tijjaniyya ba ne kamar yadda na fada muku tun farko, Dukkan wanda ya ke wasa da sallah ya ke wasa da azumi ya ke wasa da farillai ai baya kusa ma da Tijjaniyya domin ya yi ridda, mu kuwa ‘yan Tijjaniyya kowa ya sanmu mun fi kowa kokari wajen kulawa da sallah da yinta a cikin jama’a. Ba ma wasa da dukkan rukunan Musulunci, kuma muna nisantan dukkan abin da Allah ya haramta, wadanda suke wasa da sallah da matan mutane sun ridda domin sun karyata alkur’ani, sai su neme su can amma su ba ‘yan Tijjaniyya bane.

Shehi idan muka juya kan yawaitar kashe-kashen da ake samu a wasu sassan kasar nan me za ka ce ne kam?

Wannan tambaya na da muhimmancin gaske don amfanin gwamnati kiyaye rayukan ‘yan kasa, da gabobinsu da dukiyansu da mutuncinsu, da iyalansu in aka samu gwamnati ba ta kare rayukan mutane, ba ta kare mutuncinsu, ba ta kare iyalansu ba ta kare gabobinsu to hakika da saura, saboda haka muke kira ga duk wadanda abin ya shafa wato Allah ya dora muku amanar al’umma wato amanar ‘yan kasa, da rayukansu da dukiyansu da dukiyar da gabbansu wato jininsu da iyalansu da mutuncinsu wajibi ne a kare musu shi ne ma’anar gwamnati din. Su kuma ‘yan kasa su taimaka, cikin jin maganar gwamnati da biyayya wa gwamnati, idan an samu haka za a samu zama lafiya.

Annabi (S) wanda duk maganarsa a Ilimince ya ce, wajen neman zama lafiya dole ne manya su ji tausayin kanana dole ne kanana su girmama manya, kuma a girmama Malamai wadanda suka zama magada Annabawa, kuma ya ce duk babban da bai ji tausayin kanana ba duk kananan da basu girmama manya ba to ba sa tare da Annabi Sallalahu alaihi Wa sallama, ba wai an koresu daga Musulunci bane, a’a an koresu ne daga majalisar Annabi, inda mutane suke zama tare da Manzon Allah, saboda haka muna kiran manya su ji tausayin kanana, kanana kuma su girmama manya, su kuma Malamai a basu hakkinsu na magada Annabawa. In an yi haka za samu zama lafiya mai daurewa.

Amma kara zube kamar yadda ake yanzun nan wannan ya kashe wannan wancan ya kashe wancan kamar ba gwamnati, wannan ba shi da kyau.
Amma wassu na jingina wannan kashe-kashen ga addinin ko siyasa akwai kanshin gaskiya a wannan mahangar?

A’a kashe-kashen mutane a danganashi da addinin kuskure ne, shi addinin ya fi kowace jama’a kiyaye rayukan jama’a, da dukiyoyin jama’a da iyalan jama’a da gabobin su jama’an, to yaya kuma addinin ne zai bada umurni ana karkashe mutane ana tarwatsa musu dukiyarsu da iyalansu da mutuncinsu da jininsu? Ai addinin ba zai ce haka ba kuma bai taba yarda da haka ba, kuma kowani addini, addinin musulunci shi ne a gaba, sai addinin kirista shi ne mai biyo wa to duk wadannan addinai basu yarda da a kashe rayukan musulmi a kashe rayukan mutane, a zubar da jinin mutane, a wawashe dukiyar mutane ko’a kona ko a tarwatsa iyalansu, ko a hana musu ‘yancinsu na zama lafiya wannan ba daidai bane.

Kashe-Kashe nan ma ana akanta na Jos, Zamfara da Binuwai ga Fulani ina gaskiyar hakan?

Fulani ai ba baki bane a kasar nan shekara da shekaru Fulani suna nan a kasar nan da suna yin wannan kisan ai da ba yanzu ne za su yi ba da tun tuni suna yi, akwai dai wadanda suke yin haka suna fakewa da sunan wata kabila don su bata sunan wannan kabilar, an ce wadannan kasha-kashen da ake yi an ce da bindigogi ake yi, Fulani waya basu bindiga abin da suke da shi shine sanda da kwari da baka, amma basu da bindiga su Fulani,
Ko akwai shawara da Shehi zai bai wa a’lumma a kan wadannan mutane ‘yan Hakika?
Shawarar ita ce, koda an ji wani mutum ya danganta ‘yan Hakika da ‘yan Tijjaniyya a ce masa ba haka bane, mu ‘yan Tijjaniyya ba ruwanmu da ‘yan Hakika, don ‘yan hakika suna halatta haramun suna wasa da matan mutane suna wasa da Sallah, mu kuwa ‘yan Tijjaniyya mun fi kowa kulawa da Sallah mun fi kowa kulawa da abin da Allah ya halatta, mu mun barranta da su ba ruwanmu dasu.

Wednesday, 25 July 2018

Idan An Karbo Dukiyar Al'umma Daga Barayin Gwamnati A Rika Tunawa Da TALAKA -  Nasihar Dr Ahmad Ibrahim BUK

Idan An Karbo Dukiyar Al'umma Daga Barayin Gwamnati A Rika Tunawa Da TALAKA - Nasihar Dr Ahmad Ibrahim BUK


A cikin karatun Hadisi da gidan Rediyon Dala FM Kano suke sanyawa da karfe 6:00 kowacce safiya, wanda Dakta Ahmad Ibrahim BUK ya ke gabatarwa, yau Laraba ya shawarci gwamnatin tarayya da, kada kacokam ta tattara dukkan manufofinta wajen kwato dukiyar sata dake wajen barayin gwamnati, a kuma manta da sauran manyan bukatun Talaka.

"Idan an kwato dukiyar sai a yi wa al'umma wani abu da zai dauke musu radadin rayuwa, a duba batun man fetur, abinci da lantarki. Domin kwato dukiyar sata ba aiki ne na lokaci guda ba, sai an dauki lokaci, wanda idan ba a duba sauran bukatun talaka sai lokaci ya kure ba a yi masa komai ba".

"Su wadanda ake fadan da su sun mallaki dukiya gida da waje ba ruwansu da tsadar rayuwa, ba su san matsalar abinci ba, ba su san matsalar man fetur ba, ba su san matsalar rashin magani a asibiti ba. Don haka yana da kyau shima Talaka ya rika amfanar romon Dimokradiyya.

Shehin Malamin ya kirayi shugaban Kasa da Gwamnonin jihohi da su rika kiyaye albashin ma'aikata, wanda ko ba a rika ba su duk 25 ga wata ba a rika ba su 30 ga wata domin samun damar biyan bashin da ke kansu da kuma hidimtawa iyalansu.

A karshe Malamin ya yi Addu'o'in samun sauki da kuma yalwar arziki ga Najeriya.

Friday, 29 June 2018

WATA SABUWA.   Zamu yi wa Dr. Ahamed Gumi raddi, kuma zamu zakulo karerayin da ya ke wa al'umma-Musa Yusuf Asadussunah.

WATA SABUWA. Zamu yi wa Dr. Ahamed Gumi raddi, kuma zamu zakulo karerayin da ya ke wa al'umma-Musa Yusuf Asadussunah.Daga Datti Assalafy 

Muna anfani da wannan damar wajen sanar da 'yan uwa musulmin duniya cewa Bijimin matashin malamin sunnah Ash-sheikh Musa Yusuf Asadussunnah Kaduna (H) zai gabatar da mashahuriyar Lecture mai taken MUFTI KO MUFSIDI, MAI FATAWA NA 'KASA KO MAI 'BARNA NA 'KASA wannan lecture raddi ne ga Dr. Ahmad Gummi.

Kuma lecture ne da za'a warwarewa musulmin Nigeria da duniya gabaki daya dukkan wasu miyagun akidu da 'karya da gubar da Likitan Kaduna Dr. Ahmad Gummi yake fesawa a tsakanin al'ummar musulmin Nigeria

Insha Allahu Malam zai gabatar da karatun ranar Asabar 15 ga watan Shauwal Hijirar Annabi (saw) 1439 wanda yayi daidai 29/6/2018, za'a gabatar da Karatun a Masallacin Ahlul Baiti Wassahaba dake Hausawa Road Tudun Wada Kaduna State Nigeria daga misalin karfe 8:00pm na dare zuwa 10:00pm

Wadanda suke da zama a garin Kaduna don Allah kada ku bari a baku labarin wannan mashahuriyar Lecture, kuyi cincirindo kuje ku saurara, domin Malam ya shirya ma Lecture din! Allah Ya baku ikon zuwa Amin.
Wadanda suke tare damu a group whatsapp ku shirya insha Allah zan daura karatun da zaran Malam Ya kammala.

Malam Musa Yusuf Asadussunnah ya kirani a waya yace insha Allahu daga yanzu Malam Datti mun shirya zamubi mataki daki daki wajen mayar da martani ga Dr. Ahmad Gumi, kuma Malam yace min kafin ya gabatar da karatun zai kira ya sanar dani domin mu yiwa al'ummar musulmi albishir

Muna rokon Allah Ya tsare al'ummar musulmi daga sharrin da Dr. Ahmad Gumi yake yadawa, muna masa fatan shiriya da dawowa kan tafarki na gaskiya
Allah Ka zama jagora ga Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah Ka kara masa hazaka da zalaka da ilmi mai albarka

Wednesday, 20 June 2018

Audio :- ​SAKON DR.ABDALLAH GADON KAYA ZUWA GA GOMNAN KANO​

Audio :- ​SAKON DR.ABDALLAH GADON KAYA ZUWA GA GOMNAN KANO​


MAUKACI DAN BILKI COMONDA YA FARA YIWA MALAMAI RASHIN KUNYA AKAN MAGANAR NAN

Ga Dukkanun Alamu Wannan Sakon Yaje Kunnan Gomnan Kano Ganduje

Saboda Munji Labarin Cewa Wani Shasha Dan Jagaliyar Siyasa Mai Suna Dan Bilki Comonda Ya Fito Gidan Radio Yana Yiwa Dr. Abdallah Raddi

Akan Wannan Sakon Daya Turawa Gomnan

To Wallahi Dan Bilki Comonda Ka Sani Idan Kai Wawa Ne To Muma Muna Da Wawaye Irinka Wadan Da Zasu Mana Maganinka  Banza Dan Jagaliyar Siyasa

Duk Haukar Da Zakayi To Ka Dinga Tsayawa A Iya Rigimarku Ta Siyasa Wallahi Bakin Rijiya Ba Wajan Wasan Makaho Bane

Dan Bilki Comonda Idan Jahilci Ne Yake Damunka Mumafa Muna Da Jahilai Irinka Wadan Da Suke Dai-Dai Da Kai

Dan Bilki Comonda Ka Sani Wallahi Dukkanin Ahlussunnah Na Kano Muna Goyon Bayan Wannan Lafazin Na Dr.Abdallah Baja Da Baya


​DAGA​
​ADBULLAHI​
​NAGEGIME​


AYI SAURARO LAFIYA
👇👇👇👂👂👂

Download Audio Now

Wednesday, 30 May 2018

Sheik Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 67 Da Soma Tafsiri

Sheik Dahiru Bauchi Ya Cika Shekaru 67 Da Soma Tafsiri... ya kuma cika shekaru 54 yana tafsirn Kur'ani da ka ba tare da duba Kur'ani ba

Daga Ismat Suleja

A bana Maulana Sheikh Dahir Usman Bauchi ya cika shekaru 67 yana gabatar da Tafsirin Kur'ani. Ya fara Tafsirin Kur'ani a watan Ramadan na  Shekarar 1951. Sannan kuma a bana Sheihin Malamin ya cika shekaru 54 yana gabatar da Tafsirin kur'ani da ka ba tare da duba takarda ba.

Kana kuma a bana ya cika shekaru 39 yana Tafsiri a Birnin Kaduna tare da yin sauka uku a mashahurin Tafsirin da duniyar Ilimin Tafsiri ta Sallama masa akai wato fassara Kur'ani da Kur'ani, fassara Kur'ani da Hadisin Manzon Allaah SallalLaHu AlaiHi Wa AliHi Was Sallam, fassara Kur'ani da maganganun Sahabai da Tabi'ai da magabatan Bayi na kwarai.

Alhamdulillahi, cikin yardar Allah a ranar 25 ga watan Ramadan, Maulana Sheikh Dahir Usman Bauchi zai maimaita saukar Kur'ani a tafsirin watan Ramadan karo na uku, bayan shekaru 12 da sauka da aka gabatar a shekarar 2006 a filin taro na Murtala Square dake birnin Kaduna.

Muna addu'a Allah Subhanahu Wa Ta'Allaah Ya sanya mu daga cikin wadanda za su halarci wannan taro na bana da za a yi a ranar 10 ga watan Yuni, 2018 a filin taro na Murtala Square dake Kaduna.

Muna Rokon Allaah Subhanahu Wa Ta'Allaah Ya ja mana kwanan Shehu, Allaah Ya kara masa, lafiya. Amin.

Saturday, 19 May 2018

Wednesday, 16 May 2018

LABARI DUMIDUMINSA : Anga Wata Ramadan - Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar III

LABARI DUMIDUMINSA : Anga Wata Ramadan - Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar IIIMai alfarma sarkin musulmi sultan muhammadu sa'ad Abubakar Na ukku yayi jawabin ganin watan ramadan a yau misalin karfen 8:25pm inda yayi bayanin anga wata da kuma tabbacin manya manya malamai na kasar Inda ya bayyana jahohi da anka ga wata kamar haka:

1- sokoto

2 - Maiduguri

3- Yobe

4 - jos

5 - zamfara

6- Bauchi da sauran jahohi

Wanda ya bayyana 17/05/2018 shine yayi dai dai da 1/09/1439

Mai alfarma sarkin musulmi yayi jan hankali da mutane mu maida hankali wajen ayukan ibada da kuma nisantar abubuwan asha.
Allah ya bamu alkhairi da ke cikin wannan wata amen.

Daga: Abubakar Rabiu Yari

Tuesday, 15 May 2018

Idan Gwamnati Bata Saki El Zakzaky Ba Allah Zaiyi Fushi Da Kasar Nan. --Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Idan Gwamnati Bata Saki El Zakzaky Ba Allah Zaiyi Fushi Da Kasar Nan. --Sheikh Dahiru Usman Bauchi.


Babban malamin addinin musulunci A Najeriya kuma malamine masani a fannin kur'ani Sheikh dahiru usman Bauch yayi kira ga gwamnatin buhari da'azaunaa tattauna game da Al-zakzaky A Samar da mafita don asakeshi yanema lafiya, idan har gwamnati tayi haka to lallai babu shakka za'a kara samun zaman lafiya A Najeriya.

Shehin malamin yaci gaba da cewa kin sakin malamin wato Al-zakzaky wata jarabawace da Allah zai jarabci wannan kasar da ita ta! Domin Al-zakzaky malamine Na Addinin musulunci tsareshi batare da wata hujja Na nuna alaman yana da laifiba to lallai Allah zaiyi fishi da wannan kasar.

Sheikh dahiru usman bauci a inda ya karkare da bayanansa inda yake cewa malamai dai sune magada annabawa idan aka muzguna masu to babu shakka za'a fuskanci fushin Allah, kuma ita fushin Allah babu Dan baruwana kowa da kowa zata shafa inda yakare da ba gwamnati shawara data saki Al-zakzaky a nema masa lafiya a kasar waje.

Ayayin zantawarsa da wadansu malamai Na kusa dashi a wurin zaman karban gaisuwar marigayi khalifa isiyaka rabi'u Kano.

Allah Ya karama Shehu Lafiya.

Daga : Madubi 

Monday, 14 May 2018

Wata Kungiya ta Ɗalibbai mai suna GAMJI STUDENTS ASSOCIATION ta karrama Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe A cikin Hotunan

Wata Kungiya ta Ɗalibbai mai suna GAMJI STUDENTS ASSOCIATION ta karrama Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe A cikin Hotunan

Wata Kungiya ta Ɗalibbai mai suna GAMJI STUDENTS ASSOCIATION ta karrama Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe a bisa namijin kokarin da yake wajen ganin an tabbatar da Sunnah a wannan nahiya.
  Da yake nasa jawabin shugaba Kungiyar na reshen Al-Hikima Ustaz Basheer Mainasara yake cewa
Sheikh Kabiru Gombe mutun ne mai kokari da jajircewa wanda baya damuwa da haushin masu haushi wajen fadin gaskiya da kuma ganin an tabbatar da Sunnah da kuma aiki da ita.

Kungiyar ta kara yabawa malam irin yadda ya samarwa Mata incinsu a wannan nahiya, koda yaushe malam yana kokarin fahimtar da mata a binda ya shafi zaman Aure yadda zasu zauna mazajensu da yadda zasu bada tarbiya ga ƴaƴan su domin asamu nagartaciyar Al-ummah.

Daga karshe Shugaban yayi kira ga malam ya kara kokarin da yakeyi wajen kira ga matsa su daina shaye-Shaye domin yana gurbata Al-ummah da kuma rayuwar ɗan Adam gabaɗaya.

Mustapha Ambursa.Wednesday, 9 May 2018

Karamomin Shehu Nyass Ne Silar Arziki Da Ilimin Sheikh Isiyaka Rabi'u -Sheikh Dahiru Bauchi

Karamomin Shehu Nyass Ne Silar Arziki Da Ilimin Sheikh Isiyaka Rabi'u -Sheikh Dahiru Bauchi

 

Malam Isyaka Rabi'u Shi Kadai Allah Ya Yi Wa Wata Kyauta A Almajiran Sheik Ibrahim Nyass Da Babu Kamarsa A Nijeriya.

Sheik Dahiru Bauchi ya ce "Ka bada darrusan karatun Kur'ani, sannan ka tafi ka bude kanti (kasuwanci), Sannan ka dawo ka bude wazifa a Zawiyyarka. Sannan ka hidimtawa 'ya 'yan Shehunmu Shehu Ibrahim RTA.

"Mu mahaddata mun yi rashin dan uwanmu mahaddaci, mun 'yan Tijjaniya mun yi rashin dan uwanmu dan Tijjaniyya, masu kudi sun yi rashin dan uwansu mai kudi.

"Ina yi wa gwamnatin Kano da masarautar Kano ta'aziyya. Allah ya gafarta masa".
Abin Kunya Ne Soke Amirul Hajji Da Aka Yi A Najeriya – Dr. Bashir Aliyu Umar

Abin Kunya Ne Soke Amirul Hajji Da Aka Yi A Najeriya – Dr. Bashir Aliyu Umar


Babban limamin juma’a na Masallacin Alfurqan, kuma Shugaban cibiyar Alfurqan Charitable Foundation, Dr. Bashir Aliyu Umar, ya bayyana cewar abin kunya ne a ce an soke tsarin Amirul Hajji a lokacin aikin Hajji a Najeriya.

Malamin yayi wannan bayani ne a ranar Lahadi lokacin da yake gabatar da Tafsirin Alkurani mai girma a Masallacin Alfurqan Kano. 

A cewarsa “Amirul Hajji tun zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam al’ummar Musulmi take da Amirul Hajji”

“A yayin aikin Hajji na farko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ya wakilta Sayyaduna Abubakar ya kasance Amirul Hajji ga dukkan Musulmi, kuma ya jibanci al’amuran aikin Hajji ga al’ummar Musulmi”

“A yayin da yayi aikin Hajjinsa na farko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shine da kansa ya kasance Amirul Hajji, 
dogara da wannan ya zama koyi da Sunnarsa SAW, sanyawa al’ummar Musulmi Amirul Hajji”

“Amma abinda wannan Gwamnatin ta yi na soke tsarin tura Amirul Hajji abin kunnya ne, domin shi Amirul Hajji shi ne wakilin dukkan Musulmin Najeriya, 

Wadanda duk suke da hannu wajen cire tsarin Amirul Hajji a Najeriya sun ji kunya kuma ba su kyautawa al’ummar Musulmin Najeriya ba” 
A cewar Dr. Bashir Aliyu Umar.

Tuesday, 8 May 2018

Sunayen Malamai Da Alarammomin Da Jibwis Ta Kasa Ta Tura Tafsirin Ramadan Na 1439H/2018 A Jahohin Najeriya

Sunayen Malamai Da Alarammomin Da Jibwis Ta Kasa Ta Tura Tafsirin Ramadan Na 1439H/2018 A Jahohin Najeriya1. Sheikh Abdullahi Bala Lau da Alrm Nasiru salih Gwandu Adamawa Jimeta

2. Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo da Alarm Mustapha jalingo Taraba Jalingo

3. Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi da Alrm Muhammad Auwal Kaduna Sultan Bello

4. Sheikh Usman Isa Taliyawa da Alrm Abubakar Muh’d Bolari Gombe, Gombe Gombe

5. Sheikh Ibrahim Sabi’u Jibiya da Alrm Aminu Salisu Jibiya Katsina Jibiya Mas Hamz

6. Sheikh Yakubu Musa Hassan da Alrm Usman Birnin Kebbi Katsina Katsina

7. Sheikh Abbas Jega da Alaramma Ridwan Kaduna Kebbi Birnin Kebbi

8. ShK Dr. Abdullahi Saleh Paskitan da Alrm Abubakar Adam Sokoto Sokoto

9. Sheikh Muh’d Kabir Haruna Gombe da Alaramma Ahmad Sulaiman Kaduna T/Wada / Malali

10. Sheikh Abubakar Giro Argungun da Alarm Fadlulahi Musa Makera Niger Bargu

11. Profesor Umar Labdo da Alrm Yunusa Abubakar Jigawa Hadejia

12. Sheikh Usman Baban Tine da Alaramma Kaduna NNPC Kaduna

13. Dr. Abdulmajid Umar, Kaduna Rimi College

14 Skh Khalid Usman Khalid da Alarma Salisu Ung Kanawa Zamfara Gumi

15. Sheikh Dr Ali Mustapha da Alaramma Yunus ismail Yobe Potiskum

16. Sheikh Aliyu Abdullahi Telex Kaduna, Masjid Haruna Dan ja

17 Sheikh Ahmad Muhammad Boyi da Alarm Mustapha Jalingo Taraba Masjid bin Fodio

18. Dr Ibrahim Abdullahi Sani R/lemo da Alaramma yusuf suru Abuja Area 11 Masjid

19 Mall. Aliyu Ladan da Alarm Nasiru Dan malam Abuja Life Camp

20 Mal Hussaini Zakariya,  Abuja Bernex Plaza

21. Mal. Abdullahi umar zaria da Alaramma Salihu Gumi Abuja Garki Village

22. Mal. Auwal Mai Gaskiya da Alaramma Aliyu Ibrahim Abuja Fed. Min. of Works

23. Mal. Abdullahi Karshi,  Abuja Villa

24. Mal. Sahibul Kuwa, Abuja Dakkwa

25. Mal Muhammad Fatihu Hassan da Alaramma Ibrahim Adam Abuja Apo Legislative Quarters

26 Mal Abdulrahman Alzamfari da Alaramma Saifullahi Kira Abuja Berger Masjid

27. Dr Ahmad Atiku Auwal, Abuja Gwarimpa masjid

28 Mal Nura Khalid da Alr Abdullahi Adam Bature, Abuja Apo Legislative Quarters

29. Mal. Tajuddeen Imam da Alrm Murtala Muhammad Abuja Prince & Princes

30 Mal. AbdulRahman Sani Yakubu da Alr Sulaiman Abdullahi Azare, Abuja Juwa Emirate council

31 Mal Hamza Dr Alhassan Saeed da Alaramma Khalid Lawal, Abuja Sani Zangon Daura Estate, Kado

32. Dr. Bashir Imam,  Masjid Amb. Adamawa Yola

33. Dr. Sadau Salihu Adamawa Yola

34. Dr. Abdulqadir Salih Kazaure da Alaramma idris Gashuwa Adamawa Jimeta

35. Mal. Isa Shehu Ruga da Alm Abubakar Unguwar Madi Adamawa Ganye

36 Mal Abubakar Mukhtar Yola,  Adamawa Masallacin Nepa Jimeta

37 Mall Yahya Gidadawa da Alrm Mustapha Hamza Jarmai Anambra Onitsha/Delta

38. Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo da Alm Abubakar Muh’d Rariya, Bauchi Masjid Gwallaga

39 Mal. Alkali Sulaiman Yusuf da Alrm Dauda Muh’d Zukku Bauchi Masll Adamu Jumba

40. Mal. Aliyu Saeed Gamawa da Alaramma Saeed Adamu Bauchi Peoples Bank Masjid, Gamawa

41. Dr. Ibrahim Adam Umar Disina da Alaramma Ukasha A. Umar Bauchi Masjid Rahama

42. Mall Abdul aziz Dan lami da Alaramma Nafiu A A saeed Bauchi Tilden Fulani

43. Mal. Muhammad Kabir Azare da Alaramma Bala Bako Bauchi Azare

44. Dr. Zubairu Madaki da Alaramma Kabir Abdullahi Bauchi Masjid Umar bn Al-khattab, Kofar Wambai

45. Shk Ahmad Tijjani Yusuf Guruntun da Alaramma Muhammad Zahruddeen Bauchi Masjid S19 Dutsen Tenshe, Bauchi

46 Mall Muhammad Kabir Collage Bauchi Ningi

47 Mall Abubakar Mala Bauchi Alkaleri

48. Dr Abubakar Usman Riba da Alrm Farouq Jada Tambuwal Benue Makurdi

49. Mal.Isa Shk Ibrahim Bawa mai shinoafa da Alarm Abdulkarim Akwanga Benue Gboko

50 Mal Abubakar usman Bolari da Alaramma Adam Mahmud Borno Kwaya kusar

51 Mal. Abba Musa da Alaramma Aminu Ibrahim9, Potiskum Borno Maiduguri

52. Shk Muhd Abubakar Kachalla da Alaramma Ahmad Jiha Ismail Borno Maiduguri

53. Mal Husaini Yusuf Mabera da Alrm Mustapha Argungu Delta Wari

54 Mal. Dr Umar Garba Dokaji, Delta Sapele

55 Mal Abubakar Musa Azi da Alaramma Ahmad Qiyamuddeen Ebonyi Hosana Masjid Abakaliki

56. Mal. Nazifi Hashimu Samaru da Alrm Aliyu Ismaila Gummi, Edo Benin City

57 Mal Ibrahim Abdullahi Bauchi da Alaramma Sidi Ali Ibrahim Ekiti Ado Ekiti

58. Mal. Adam Muhammad Adam da Alarm Abubakar Jibril Bula Gombe Gombe

59 Dr Abdallah Umar Gadon Kaya da Alaramma Baba Lawal Kan bariki,(Water Board)
Kumo Gombe

60 Dr Sani Ashir Kano da Alrm Auwal Ung Mai kawo Gombe Gombe

61 Mall Adaurrahman Dr Alhassan Said Jigawa Gumel

62. Mall Usman Bello San Turakin Kumo da Alaramm Abubakar Kaura Jigawa Kazaure

63. Mal. Sulaiman Abubakar Birnin Kudu Jigawa Yalwan Damai

64. Mall Isa Abdullahi da Alaramma Hamza Isa Abdullahi, Jigawa Hadeja

65. Mal. Sani Yakubu Kaduna Zaria

66. Dr Abdurrahman Idris zakariyya da Alaramma Auwal Iliyasu Kaduna Saminaka

67. Shk Abduihadi Aliyu Daura da Alarm Yunusa Abubakar Kaduna Dan Fodio Masjid

68. Mal. Murtala Nasir Almisry da Alaramma Aliyu Dahir Kaduna ASD Motors

69. Mall Abdulrahman Maiduguri da Alrm Shamsuddeen Haruna Kaduna Rigachikun

70 Mal. Sani Sulaiman Funtua da Alaramma Abubakar Kaura Kaduna Kafancan

71. Mall Shuaibu Salihu Zaria da Alaramma Aliyu Umar Kaduna Tudun Wada Zaria

72 Imam Khidir Bello Manufa da Alrm Sidi Aliyu Ibrahim Kaduna Tafa

73 Mall Shuaibu Salihu Zaria da Alaramma Aliyu Umar Kaduna T/Wada zaria

74 Mal. Muhammad Sani Alhamidy da Alaramma Kano Bebeji

75. Mal. Abdul mudallib Ahmad Tijjani da Alrm Salihu Muhd Usman Kano Masjid Triump

76. Mall Abdul mudallib Gusau da Alaramma Umar Ramadan Kano State Univ.Wudil

77. Mall Saifullahi Adam Shuaib da Alaramma Tasiu Sabiu Kano Huguma Takai Kano

78. Dr Ibrahim Sani Jibiya,  Kano Kura

79 Mall Abdul mudalib Gusau da Alrm Umar Ramadan Kano State University, Wudil

80. Mall Aminu Numan Almr Muhammad kabir Yawuri Kano Tudun Murtala Kano

81. Mall Ibrahim Idris Zakariya da Alr Sulaiman Adam Tudun wada Kano Tudun Wadan Dankade

82. Mall Nuruddeen Numan da Alaramma Bashir Gombe Katsina Babban Masjid Funtua

83 Mal. Aminu Liman Mustapha Funtua

84. Mal. Aminu Yammawa Katsina Masjid. G.R.A.

85 Mal. Muktar Usman Jibiya da Alaramma Auwal Umar Katsina Government House KT

86.

87. Mal. Hassan Yusuf da  Alaramma Haruna Salisu Katsina Masjid Senator (Madawaki)Daura

88 Dr Jamilu Zarewa, Katsina Masj Bilal ibn Rabah

89. Mall Safiyu Alqasim,  Katsina Masallaci jumaa Bakori

90 Mal Ahmad Ahmad Kura,  Katsina Dutsen-ma

91. Mall Kabiru Chiadawa da Alrm Muhd Aliyu Kamba Katsina Malumfashi

92 Mal. Usman Zaga da Alaramma Adam Muhammad Fana Kebbi Bena

93 Mal Husaini Isa Abubakar da Alm Hassan Sani Tambuwal Kebbi Yawuri

94. Mal. Ishaq M Alqali da Alaramma Safiyanu Abdullahi, Makera Kebbi Danko Wasago

95 Mal. Imam Aliyu Bunza da Alaramma Amiru Ibrahim Argungun, Kebbi Argungun

96 Mall Aliyu S Mafara da Alaramma Usman Tagule Kebbi Kamba

97. Mal. Umar Jega da Alaramma Nafiu Bena Kebbi Koko

98 Mal. Tasiu Funtuwa da Alaramma Muhammad Bunza Kebbi Argungu

99. Mal. Imam Dahiru Lokoja da Alaramma Ishaq Kogi Lokoja

100. Mal. Imam Yahaya Iddah da Alaramma Auwal Muhammad Kogi Iddah

101. Mal. Yusuf Umar da Alaramma Rabi’u Ibrahim Kogi Obajana

102. Mal. Salihu Mukhtar da Alarm Ahmad Muhammad Kwara Ilorin

103. Mal. Attahiru Kaiama da Alaramma Ibrahim Kaima Kwara Kaima

104 Mall Mas'ud Ibrahim Offa da Alr Abdulwahid Abdulhamid Kwara Offa

105 Mal. Abubakar Abdulsalam da Alaramma Tukur Jakada Lagos Sabon masallaci Agege Lagos

106 Mall Aminu Khalilu Ung Barau,  Lagos Masj Ahlussunah IKorodu

107 Barrista Ishaq Adam Lagos

108 Mall. Bukhari yakubu da Alaramma Muhammad fari Lagos Agege Lagos

109 Mall Anas Assalafee Kano da Alaramma Abubakar Rano Lagos Obalande / Ikoyi

110 Sheikh Imam Sulaiman Lagos Masjid 1000 & 4

111. Mal . Jamilu Albani da Alaramma Abubarkar Umar Balarabe, Nassarawa Lafia

112. Mall Adam Ibrahim Ishaq Al-madani da Alaramma Harith umar Abubakar Nassarawa Karu, Masjid Jibwis

113 Mal Abubakar Usman Pakistan da Alaramma Ibrahim Abubakar Nasarawa Keffi

114. Mall Musa Mujaddadi da Alaramma Sulaiman Hussaini Doma Nasarawa Doma

115 Mal. Muh’d Sani Ahmad Almuhadis da Alaramma Abubakar Bawa Niger Wawa

116 Mal. Lawal Shuaibu Abubakar da Alaramma Abdulrashid Jega Niger Minna

117 Mal Abdulrahim Sabiu Rafin Dadi da Alaramma Danwarai Niger Kontagora

118 Umar Jega da Alrm Iliyasu Birnin Gwari Niger Suleja

119 Mall.Muhammad Auwal da Alaramma Dahir Musa Niger Mariga

120 Mall. Usman Arabi da Alarm Safiyanu Abdullahi Niger Rijau

121. Dr Umar Gumi,  Niger Lafai

122 Mal. Bukhari Ibn Ishaq Albayani da Alm Anas Abdullah Yalwan Shandam Niger Shiroro

123 Mal Abba Abdullahi Gwale da Alaramma Idris Saminaka Niger Lapai

124. Mal Hashimu Nataala Yawuri da Alrm Saidu Yusuf Mista Ali Plateau Yalwan Shendam

125 Dr Ismail Kumo da Alrm Usman Barikin Ladi Plateau JOS

126 Mall Muhammad Aminu Muhammad da Alrm Yusuf Dabai Mai Sittin Plateau Bukuru

127. Mal Shuaibu Adam Makoli da Almr ismail Abullahi Mangu Plateau Dengi Kanem

128 Mall Mustapha Yusuf Hadejia da Alam Muhd Auwal Jalingo Rivers Port-Harcourt

129. Mal. Yunus Saeed Abdul-Hamid, Rivers Refinery Depot

130. Mal. Abdulbasir Ung Mai Kawo da Alarmma Sani Mulumfashi Sokoto Illela

131 Mal. Aliyu Aliyu Muhammad jos da Alaramma Bala Abubakar,  Tambuwal Sokoto Tambuwal

132 Mal. Umar Mai Damma da Alaramma Auwal Adam Sokoto, Sokoto Masj shk Ab Gumi Sokoto

133 Mal Musa Asadus Sunnah  Sokoto Sokoto

134 Mal. Abubakar Ladan Mai Idigami da Alaramma Muhammad Auwal Sokoto Masj Lokoja Road Sokoto

135 Mall Sani Abubakar Tambuwal da Alaramma Sokoto Sultan Ibrahim Dasuki Mosque

136. Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da Alaramma Abubakar Ghani Sokoto Masjid Abu Huraira

137. Mal. Muhammad Barkindo Jungudo da Alaramma Abdullahi Badejo Taraba Masjid Ummah

138. Shk Salihu Muhammad Barau da Alrm Abdurrashid Lamido Gora Taraba Masjid Nana Aisha RD Jalingo

139. Mal. Gambo Kyari Maiduguri, Taraba Wukari

140 Mal Abubakar Salihu Dengi da Alm Abubakar Muhd Dal Oyo Ibadan

141 Mal Isah Aliyu Jen da Alaramma Oyo Ojo Exp,Tudun Sunnah.

142 Mall Hassan Bako da Alaramma Abubakar Kaura Ogun Shagamu

143 Mall Mujtaba Yakubu Musa da Alrm Jamilu ISA Danlaje Osun Oshogbo

144 Mall shafiu Salihu Kazaure da Alrm Sani Ibrahim mai Niyya Osun Unguwar Sabo

145 Mal. Attahiru Muhammad Tilde da Alarm Hashim Sani Hashim Yobe Jaji Maji

146 Mal Abdulaziz Muhammad Bauchi da Alrm Suleiman Funtua Yobe Gaidam

147 Mal.Ibrahim Damaturu da Alaramma Sani Nguru Yobe Damaturu

148 Dr Umar Musa Kano da Alaramma Bello Argungu Zamfara Anka

149 Mal. Surajo Muhammad Gusa,  Gusau Zamfara

150 Mal. Usman Abdulrashid Almadani da Alaramma Garba Bayawa Zamfara Bukuyum

Sanarwan ta fito ne daga ofishin shugaban kwamitin Tafsir, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, ta ofishin shugaban Kwamitin Jibwis Social Media ta kasa, Ibrahim Baba Suleiman. Tare da sa hannun sakataren kwamitin Tafseer Ustaz Jameelu Kankara.

Jibwis Nigeria
21-Sha'aban-1439
08-May-2018.

Monday, 30 April 2018

Wallahi Gwamma  Mazinaci ko  Dan Luwadi ko kuma Mashayi akan Dan Bidi'ah,  -- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe

Wallahi Gwamma Mazinaci ko Dan Luwadi ko kuma Mashayi akan Dan Bidi'ah, -- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe

Domin Mazinaci ko Dan Luwadi ya sani karara cewa sabon Allah ya keyi, idan ma har akayi mishi magana ko nasiha sai yace a kara sanya shi a Addu'a Insha Allah zai bari.

Amma shi Dan Bidi'ah yana kallon ihun da yake yi da tsalle tsalle a matsayin shine addini kuma son Manzon Allah, saboda haka baka isa ya saurare ka ba da wata nasiha, da wannan ne nake kara tabbatar muku da cewar, Bidi'ah Musiba ce kuma Bala'i ce  Allah muna roko a gareka ka karemu Daga fitinar Bidi'ah karama ko babba.

Sources :arewadaily trust

Thursday, 26 April 2018

'Yan Hakika Ba 'Yan Tijjaniyya Ba Ne Yan Shedaniyya Ne, Inji Sheik Dahiru Bauchi

'Yan Hakika Ba 'Yan Tijjaniyya Ba Ne Yan Shedaniyya Ne, Inji Sheik Dahiru Bauchi


...kaf Nijeriya babu wanda ya kai mabiya Tijjaniyya yawan mahaddata Kur'ani, cewarsa

Daga Babangida A. Maina

Sheik Dahiru Bauchi ya ce

"Akwai Musulmi Da Yawa Suna Shan Giya, Suna Neman Mata, Suna Sata, Suna Karya, Suna Luwadi, Suna Caca, Suna Madigo, Suna Aikata Laifuka Mabanbanta Wanda Aka Sani Da Wanda Ba'a Sani Ba.

Shin Musulunci Ne Ya ce Su yi Hakan? Kowa Zai ce Mun A'a.

To Haka Abin Yake a Wajan Wasu Mutane Masu Kiran Kansu Da 'Yan Hakika a Cikin Tijjaniyya Dukkan Abubuwan Da Kuka Ga Suna yi Ba Tijjaniyya Ne Ta Koya Musu Ba, A'a Su 'Yan Shedaniyya Ne.

Ga Abinda Tijjaniyya Ta Koyar Kamar Haka;
* Istigfari,
* Salatin ANNABI (S.A.w), Da
* Lailha Illallahu,
* Kulawa Da Sallahn Jam'i,
* Girmama Iyaye Da Yimusu Biyayya,
* Yawan Karatun Qur'ani.

Shine Aikin 'Yan Tijjaniyya. Shi ya sa a Nijeriya Babu Wanda Ya Kai 'Yan Tijjaniyya Na Gaskiya, Ba Tijjaniyya Bogi Ba, Yawan Mahaddata Alqur'ani.

Ya Kamata Sauran Jama'a a Dunga Mana Adalci".