Monday, 24 September 2018

Hadarin zama Da Mace Daya -  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hadarin zama Da Mace Daya - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.

ILLOLI GA MAGIDANCI.
1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida.
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.

ILLOLI GA SU MATAN.
1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida,  yaran gida da ita ma kanta.
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya.
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa.
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.

ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu.
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma.
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.
WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA,
DA FATAN MAGIDANTA ZASU GANE,
SU KUMA MATA ZA SU TAIMAKAWA JUNANSU WAJEN TUNAWA MAI GIDA YA QARA AURE.

Sunday, 23 September 2018

ALBUM : Classiq - New North (EP)

ALBUM : Classiq - New North (EP)New North (EP) is a studio album by Nigerian recording artist ClassiQ which was released through Arewa Mafia on September 21, 2018.
The Album houses 8 complete track with feature appearances from Ckay , Ice Prince ,
Yung L, M.I Abaga , and other talented artists.
The production list was also released with talents such as TUC, Supersonic , G-Plus Chang , Reinhard Tega , and others.
ClassiQ New North Album Tracklist Below;Bad Man (Karya Su Ke)Download Music Now


2. Gargajiya


Download Music Now


3. Sai GodiyaDownload Music Now
4. Manager feat. Ckay


Download Music Now


5. Up & Away feat. Ice Prince


Download Music Now6. Sharp Sharp

Download Music Now


7. Binta

Download Music Now8. Wonder Me feat. Yung L

Download Music Now


Sources:arewarulers.comSharhin Fina Finai : Sharhin Fim Din Matar Mamman

Sharhin Fina Finai : Sharhin Fim Din Matar Mamman

Suna: Matar Mamman
Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo
Kamfani: Asnanic Mobie Tone
Shiryawa: Usman Mu’azu
Umarni: Aminu Saira
Jarumai: Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Hafsat Idris, Asiya Barde, da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din me kallo ya ga Uwale (Asiya Barde) ta na bacci wanda a cikin barcin ta tayi mafarkin wata gawa wadda jama’a suka dauke ta suka kai ta makabarta, bayan Uwale ta farka daga bacci a firgice sai mijinta Magaji (Isa A. Isa) yake tuhumar ta akan don me zata dinga mugun mafarki don kawai yace zai karo mata kishiya? Daga baya Magaji ya soma kokarin kwantar was da Uwale hankali a bisa dalilin sa na son kara aure amma bata saurare sa ba saboda mafarkin da tayi na gawar wata mace shi yafi tsaya mata a zuciya, hakan yasa ta tafi wajen malami ta fada masa mafarkin da tayi gami da son sanin fassarar mafarkin ta, amma sai malamin ya nuna mata cewar bazai fassara mata mafarkin ba har sai taje ta nemo bayani akan gawar matar da ta gani a mafarkin tunda ta nuna alamun cewar tasan wani makusancin gawar da ta gani. Haka kuwa Uwale ta tafi wajen Asiya (Hafsat Idris) don son sanin wacece matar da taga gawar ta a mafarki? A nan Asiya ta fara bawa Uwale labarin Mariya wadda itace Uwale ta gani a mafarkin ta, kuma Mariya (Hadiza Gabon)kawar Asiya ce wadda suka taso tare domin Asiya ce tayi mata siyan baki a lokacin auren Mariyar da mijinta Mamman (Ali Nuhu) bayan auren Mariya da Mamman sai Asiya ta cigaba da zuwa gidan Mariya a duk sanda take da lokacin hakan, kuma akwai mutunta juna a tsakanin Asiya da Mamman saboda akwai lokutan da idan tazo gidan Mariya yakan bukaci Asiya da cewar ta jira shi ya dawo daga aiki don ya sauke ta a gidan iyayen ta, akwai lokacin da Mamman ya dauko Asiya a motar sa don mayar da ita gida sai yake tambayar ta shin bata da masu son auren ta ne? Sai Asiya ta nuna masa cewar har a sannan bata samu wanda suka daidai ta ba shi yasa ma ta koma makaranta don cigaba da karatu, jin hakan ne ya bawa Mamman dama bayan ya koma gida sai ya fara turo mata sakonnin soyayya a shafin zumunta na ‘Whats’App’ bayan Asiya taga an turo mata sakonnin kulawa a wayar ta kuma da lambar da bata sani ba sai tayi mamaki gami da son sanin wanda ya turo mata sakon na kalaman soyayya, amma a cikin hirar sai Mamman ya nuna mata cewar zasu hadu da ita don ta gane wanda yake son ta, hakan kuwa akayi Asiya tana makarantar su sai taga Mamman yazo wajen ta a lokacin da tayi zaton ganin wanda yake turo mata kalaman soyayya, hakan yasa ta kasa yarda da cewar shine me turo mata sakonnin soyayya a waya sai ta fara zaton ko abokin Mamman din ne yake son ta, amma a nan take a wajen sai Mamman ya nuna mata cewar shi yake turo mata sako kuma yana son ta da aure, hakan ya bawa Asiya mamaki saboda ganin cewa ita kawar matar sa Mariya ce. Don haka sai Asiya ra roki Mamman akan ya canja shawara don bazai samu abinda yake nema a wajen ta ba.

 Da daddare kuwa Mamman ya shirya cikin kaya masu kyau ya fesa turare zai fita, amma da Mariya taga yayi wannan shirin sai ta tambaye sa inda zai je amma sai Mamman ya nuna wajen mahaifin sa zai je, jin hakan sai bai gamsar da Mariya ba sai ta fara zargin ko ya shirya yi mata kanwa ne saboda tun kafin ya aure ta yasha fada mata cewar bashi da ra’ayin zama da mace daya, amma sai Mamman ya nuna mata sam ba haka bane shi ziyara zai je. Bayan Mamman yaje wajen Asiya sai ta fito ta gargade sa akan kada ta sake ganin yazo gidan iyayen ta saboda bazata iya auren sa ba domin tana ganin yin hakan kamar zataci amanar kawar ta Mariya ne. Bayan Mamman ya koma gida sai ya cigaba da kiran wayar Asiya yana yi mata magiya akan ta so shi amma sai ta nuna sam bata amince ba. Cikin dare Mamman yana bacci sai Mariya taji shigowar sako a wayar sa, bayan ta duba ne sai ta fahimci cewa yana son ya auri kawarta Asiya, bayan ta fuskanci hakan ne sai ta soma bijiro masa da maganar tana so ya kara aure, amma sai Mamman ya nuna sam shi baya ra’ayin hakan. Asiya kuwa sai ta daina zuwa gidan Mariya sai bayan an dau tsawon wani lokaci sannan tazo, hakan ya kara saka Mariya zargi akan cewar tabbas akwai alakar dake tsakanin ita Asiya da Mamman, hakan yasa Mariya ta roki Mamman akan tana so ya auri Asiya, amma sai yayi fushi ya nuna cewar tana zargin sa da kawar ta ne, Asiya da Maryam suna cin abinci sai Mariya taji Asiya tana yabon halayen Mamman gami da nuna bai kamata ta dinga samun sa6ani dashi ba, hakan yasa Mariya ta yi amfani da wannan damar wajen bijirowa Asiya da batun tana so ta auri mijinta Mamman, amma sai Asiya taki amincewa da hakan har ma ta soma fushi da Mariya ta daina zuwa gidan, hakan yasa Mariya taje gidan iyayen Asiya ta cigaba da rokon ta akan ta auri mijinta Mamman, amma Asiya duk da hakan bata amince ba, sai dai kuma abin ya dame ta don ta rasa yadda zatayi, musamman da taga Mariya tana bibiyar ta a ko ina har a cikin makaranta don ta auri mijinta Mamman. Mariya ta yi nasarar shawo kan Mamman ya amince zai auri Asiya saboda dama can yana son ta kuma akwai lokacin da wani abokin sa ya taba bashi shawara akan tunda matar sa Mariya ta amince masa da ya karo auren wadda yake so ya dace ya amince, amma a sannan din ma dai Mamman yana nunawa abokin nasa cewar yasan kawaici ne matar sa take masa domin tana son duk abin da yake so koda kuwa ita bata son abin. Bayan Mamman ya amice da bukatar Mariya ta son ya auri kawarta amma sai ya nuna ai ba lallai Asiya ta amince da auren ba, nan ma dai Mariya ta nuna kada ya damu zata shawo kan matsalar. Haka kuwa aka yi, Mariya ta matsawa Asiya akan lallai tana so ta auri mijinta Mamman domin ko bai aure ta ba zai auro wata macen tunda yana da ra’ayin zama da mata biyu, hujjojin da Mariya ta dinga kawowa Asiya ne yasa har Asiya ta amince zata auri Mamman. Cikin dan lokaci kadan aka fara shirye shiryen aure har ma dangin Mamman suna mamakin halayyar Mariya saboda ganin da ita ake ta shagulgulan bikin auren mijinta da Asiya, a wannan lokacin ne kannen Mariya suka rutsa Asiya a makaranta suka ci mata mutunci har da marin ta saboda zata auri mijin yayar su Mariya. Wannan dalilin ne yasa mahaifiyar Asiya da kuma ita Asiyar suka janye maganar hada auren Mamman da Asiya, amma sai Mariya ta kai karar kannen nata wajen iyayen su wanda kuma su ma iyayen basu goyi bayan abinda yaran suka yi ba, har ma mahaifin su Mariya ya nuna bazai yafewa kannen Mariyar ba har sai sun je sun roki gafarar Asiya, haka kuwa aka yi sai da suka nemi yafiyar Asiya kuma Mariya ta sa baki har abin ya wuce kuma Asiya ta amince da zata auri Mamman.


Bayan auren Asiya da Mamman Mariya ce ta karbi kudin siyan baki a wajen mijin su Mamman sannan ta yi musu nasiha gaba daya na zama lafiya. Bayan gama hakan ne ta shiga daki tana kuka saboda kishin mijinta da ya dame ta amma son abinda yake so ne da bin umarnin Allah hakan ya hana ta bayyana kishin ta a sarari. Ba’a jima da yin auren Asiya da Mamman ba sai abubuwa suka soma dagule masa, ya fara yin asara, kayan sa da aka turo daga wani garin ma’aikata suka rike, ba shi ya fara hawa kan sa. Nan fa dangin Mamman suka fara kananan maganganu akan ya auro mace me kashin tsiya ga komai nasa ya fara karewa, jin hakan bai sa Mamman ya gamsu da cewar matsalar daga wajen matar sa bane, haka itama Mariya ta kara nuna masa muhimmancin yarda da kaddara. Ana cikin wannan matsalar ne Asiya ta samu juna biyu wanda hakan yasa duk sukayi ta farin ciki, musamman Mariya tafi kowa farin ciki saboda tana ganin Asiya zata haifawa Mamman dan da ita bata haifa masa ba, Asiya tana mamakin saukin kai irin na Mariya gami da rashin nuna kishi akan juna biyun da ita Asiyar ta samu, ana cikin murnar ne aka gane cewa itama Mariya tana dauke da juna biyu, nan fa murnar su ta karu saboda suna ganin sun samu abinda kudi bazai basu ba, wato haihuwa. Bayan dan wani lokaci Mariya da Asiya su ka haifi ‘ya’ya mata wadanda duk aka saka musu sunan Mariya.

Lokacin da Asiya fa gama bawa Uwale labarin Matar Mamman wato Mariya, sai Uwale taji tana nadamar abinda take shirin yi na hana mijin ta kara aure, hakan yasa bayan ta koma gida ta roki gafarar mijinta gami da nuna cewar ta amince ya kara aure, amma sai mijinta ya nuna dama zai kara aure ne saboda munanan halayen ta, amma yanzu ya fuskanci tayi nadamar sa zata iya gyara halin ta don haka shima ya fasa kara wani auren.

Abubuwan Birgewa:

1- Marubucin yayi kokari matuka wajen gina labarin, domin labarin fim din ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba.

2- (Matar Mamman) Sunan fim din ya dace sosai da labarin.

3- Labarin ya fadakar domin yana dauke da mafita kan hujjoji masu karfi wadanda suke damun al’ummar mu, musamman ma ga mata.

3- Fim din ya rike me kallo wajen son ganin abinda zai faru a gaba, sannan kuma fim din ya ta6a zuciyar me kallo kuma mutum zai ga kamar rayuwar zahiri ta wadansu mutanen yake kallo.

4- Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin, haka kuma me daukar Camera tayi kokari ta hanyar nuna salon daukar hoto me kyau. Daga hoto har sauti sun fita radau.

5- Kalaman jaruman wato (Dialogue) sun yi dadi gami da gamsar wa.

6- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin. Wato (Location)

7- Jaruman sun yi kokari matuka wajen samar da yanayin da ya dace.

Kurakurai:

1- Shin wace alaka ce a tsakanin Asiya da Uwale? Me kallo yaga Uwale taje wajen Asiya an bata labarin Matar Mamman, amma ba’a nuna dangantakar dake tsakanin Asiya da Uwalen ba. Tunda ba’a nuna Uwale a cikin jerin kawayen Asiya ba, ya dace ayi bayanin alakar su ko da ta hanyar ‘yan uwan taka ne.

2- Shin wanene mahaifin Asiya ne? Har fim din ya kare me kallo bai ji ko a baki an ambaci mahaifin ta ba, musamman a sanda maganar auren ta da Mamman ta taso da kuma sanda aka ce an fasa auren, ya dace aji an ambaci ko wani Kawun ta ne, idan ma rasuwa mahaifin nata yayi, ya kamata ko a baki ne a fada.

3- Abin daukar sauti ya leko a lokacin da Mariya da Asiya ke cin abinci a falo, sa’in da Mariya ta fara bijirowa da Mamman batun ya auri Asiya a sanda yayi fushi ya fice daga gidan.

4- An samu discontinuity a lokacin da Mamman ya shirya a karon farko da daddare don soma zuwa hira wajen Asiya, an nuna bakar doguwar riga a jikin Mariya a sanda ta shigo daki take tambayar sa inda zai je, amma bayan ya dawo sai aka ganta sanye da koriyar doguwar rigar atamfa a falo, bayan kuma tabi Mamman cikin daki sai aka sake ganin ta da bakar doguwar rigar farko.

5- Lokacin da yayar Mamman wato Yaya Fati da kanwar ta suka zo gidan Mamman bayan sun dawo daga wajen kai kayan lefe, me kallo yaji sanda Yaya Fati take cewa, tana mamakin ganin yadda Mariya ta zage dantse wajen kai kayan lefe gidan su kishiyar ta. Amma a karshen hirar sai akaji kanwar Mamman tana tambayar cewa yaushe za’a kai kayan lefen? A cikin hirar gaba daya me kallo ya fahimci an kai kayan lefen saboda ko nuna su ma ba’a yi ba, don haka bai dace a karshen hirar a ji kanwar Mamman ta tambayi shin yaushe za’a kai kayan lefen ba.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma yayi ma’ana sosai gami da gamsar da mai kallo, labarin yazo da kyakkyawan salon da zai iya yin tasiri wajen dakile mugun kishi ko mummunan zato daga wajen mata da sauran jama’a. Wallahu a’alamu!

Sources:leadershipayau

Jaruma Maryam Booth Ta Samu  Babban Matsayi A Gidauniyar AtiKu Abubakar

Jaruma Maryam Booth Ta Samu Babban Matsayi A Gidauniyar AtiKu Abubakar

Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake rike da matsayi karkashin wannan gaidauniyar.

Fitacciyar jaruma Maryam Booth ta samu babban matsayi a gidauniyar tsohon mataikin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.

Gidauniyar Atiku Care Foundation wacce take tallafa wa mara sa galihu ta daukaka mukamin ta daga jakadiya zuwa mukamin mataimakin shugaba na yankin arewa.
Gidauniyar ta sanar da hakan ne ta hanyar wani sako da ta wallafa a shafin ta na kafafen sadarwa inda ta bayyana cewa matsayin zai fara aiki daga ranar juma'a 21 ga watan Satumba.


Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake karkashin wannan gaidauniyar.
Wasu daga cikin fitattun jarumai da suka samu matsayi a gidauniyar sun hada da Fati Muhammad, Rashida Adamu da Abdu Boda.

An kafa gidauniyar ne domin taimakawa mara hali tare da nuna aikin tallafawa da Atiku Abubakar keyi ga idon jama'ar Nijeriya har da na kasashen waje.

Har ila yau gidauniyar Atiku Care Foundation ta zama cibiya da tsohon mataimakin shugaban kasa ke samu yana mu'amala da yan kasa a ko wani lungu da sako ta hanyar kafafen sadarwa da gidauniyar ta kafa.

Sources:pulse.ng
Sababbin Kyawawan Hotunan Fati shu'uma da Na Tayar Da Kura

Sababbin Kyawawan Hotunan Fati shu'uma da Na Tayar Da Kura

Sababbin hotunan jaruma fatima abubakar wanda anka fi sani da fati shu'uma akan wanna fim da ta haskaka a cikinsa akan harka shu'umanci wanda kuma fim din yayi kyau da irin rawar da ta ,taka a cikinsa wanda masu kallo sunka fahimci sakon da ke da wannan fim sosai.

Friday, 21 September 2018

Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Anka Daina Ganinta A Fim Yanzu

Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Anka Daina Ganinta A Fim Yanzu

Ta bayyana hakan ne yayin da take bada amsar tambayar da wani masoyin ta yayi a shafin ta na Instagram.

Fitacciyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa ba'a cika ganin ta a cikin fina-finai a kwana-kwanan nan.

Jarumar bayyana hakan ne a yayin da take baiwa wani masoyinta amsar tambayar da yayi mata na cewa, mai yasa bata cika fitowa a fim kwana-kwanan nan?.
Masoyin jarumar ya yayi tambayar bayan ya sanar mata cewa ita ce jarumar wanda fim dinta yafi birge shi kuma yana kewar rashin ganin ta a sabbin fina-finai dake fitowa daga masana'antar kannywood.


Nafisa ta mayar masa da martani inda take cewa ta gode da soyayyar da yake mata kana ya shaida masa cewa tana da wasu ayyuka da take yi bayan fim kuma harkar tana da matukar wahala idan ta hada da fim domin shirya fim tana daukar lokaci kuma tana da wahalar hadawa. Tace idan ta samu labari mai kyau zata iya tsaida matsaya game da batun fitowa a shirin.

Daga karshe jarumar ta wasa masa ruwan sanyi a zuciya inda tace yayi hakuri zuwa cikin watan Disamba zai ganta a cikin shirin fim.

Sources:pulsehausa
Classiq Arewa Mafiya Ya Raya  Ranar Haihuwarsa Da Sabon Album "The New North"

Classiq Arewa Mafiya Ya Raya Ranar Haihuwarsa Da Sabon Album "The New North"

Hazikin mawakin hausa hip-hop Barnabas Buba Luka wanda aka fi sani da Classiq ko Captain sama yana murnar zagayowar ranar haihuwar sa yau 21 ga watan Satumba.
Domin raya wannan rana mai muhimmi a rayuwar shi, mawakin zai fitar da faifan sabbin wakokin shi domin nishadin masoyan sa da masu bibiyan wakokin sa.

Kamar yadda ya sanar a shafin sa na Instagram mawakin wanda aka yi ma lakabi da 'Arewa mafia' zai kaddamar da wakokin ne a wajen taron biki da aka shirya masa musamman domin murnar ranar haihuwa.

Sabon faifan wakokin shine "The New North" kuma wakoki Takwas ne a cikin ta.
Wasu daga cikin mawaka da ya saka a cikin ta sun hada da Ice Prince Zamani, Ckay da Yung L.

Kasancewa yau take ranar haihuwar shi ne ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da shi ;

1. Dan jihar bauchi
Wannan mawakin da aka haifa ranar 21 ga watan Satumba na 1991 haifaffen dan jihar Bauchi ne kuma shine da na karshi cikin yara 3 da iyayen sa suka haifa.

2. Baban shi malami ne
Kwarrai ko kana iya kiran shi da “dan mallam” domin shima na alfahari da haka kasancewa babban shi malami ne a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake nan jihar Bauchi. Baban shi likita ne na boko a fannin ilimin “geography” ita kuma uwar sa malama ce a asibiti.

3. Yayi karatun sa a Arewa
Shidai wannan jarumin waka ya fara karatun sa na firimari garin Bauchi kuma ya kammala karatun digiri dinsa a jami’ar Ado Bayero dake
Kano inda yaa karanta ilimin kwamfuta.

4. Ya yayi wasa a garuruwa da dama kuma jakadan arewa ne
Classiq ko kuma “arewa Mafia” kamar yadda yake ma kansa lakabi yayi wasa a wurare da dama kuma ya yi waka tare shahararrun mawakan Nijeriya .

5. Duk wakar shi akwai dangantaka da Arewa
Ko cikin baitutukar shi ko sunnan wakar ko kuma yanayin shigar shi a bidiyo zai ka ji ko ka gan abun da ya ganganci arewa. Duk da cewa wannan mawakin yana iya basaja ya koma wakokin turanci amma ya amince da ya dabbaka yaren ga idon duniya.
yayi wakoki irin su Zauna, Sama, hoto, barka da sallah, Ana haka da dai sauransu.

MUSIC : Umar M Shareef - Bude Cikin  Zuciya Latest Song

MUSIC : Umar M Shareef - Bude Cikin Zuciya Latest Song

Ga wata waka daga cikin album din 'Ni da ke' wanda duk wakokin da ke cikin wannan album sunyi dadi soaai ba'a cewa komai ga kadan daga cikin baitocin wakar.

==> Bude cikin zuciya ki jefa ni, in na shiga sama karki fiddani


==>  Dan mazari  a kira gwanin rawa ,in ya fito chilas ayo kalla.

==> Dan makaranta nafiso bani shiri da diyar da ke talla.

Bari na barku haka kar ku a hakan hausawa kance waka a bakin mai ita yafi dadi.

Download Music Now

Shawarata Ga Mata Yan Fim suyi Aure -inji  Fati Nayo

Shawarata Ga Mata Yan Fim suyi Aure -inji Fati Nayo

Fati Nayo ‘yar Fulanin asali, hazikar mace mai rike da sana’o’i daban-daban, kuma fitacciyar jaruma cikin shirin fim din Dadin kowa da take fitowa a Dillaliya, ta shawarci matan da suke harkar fim da su yi aure idan sun samu mazaje. Fati Nayo ta ba da wannan shawara ce, cikin tattaunawarsu da wakiliyar
LEADERSHIP AYAU Lahadi , ga yadda hirar ta kasance.

Masu karatu za su so su ji cikaken sunanki da cikaken tarihin rayuwarki
Sunana Fati Nayo fulanin Asali ce. Wadda aka fi sani da Kyauta Dillaliya a cikin shirin Dadin kowa Sabon salo, An haife ni a Kasar Saudi Arabia, a garin Madina, na yi karatu a Gombe, ina aiki a asibitin Murtala. Kuma yanzu Ina wasan kwaikayo a Tashar Arewa 24 bangaren Dadin kowa Sabon salo. Ina yin Dj, da Humra, Dinkin labulaye, Ina kuma yi wa Ma’aurata nasiha, sannan ina yi wa yara tarbiya, ina yin waka – jefi, kazalika Ina yin dinkin kaya. Aikin Asibiti, Soja, waka, Dinki, wasan kwaikwayo, abu 5 suka ginu a zuciyata tun ina karama, har na girma, amma yanzu na samu 4 Soja ne ban samuba, da ma shi ma sojan ba ni zan yi ba, kawai suna birge ni don su Jarumai ne, kuma har yau ina kaunar Soja.

Shin menene ya ja ra’ayinki kika zabi yin wasan kwaikwayo alhalin kina aikin asibiti, kuma Kina da sa na’ar hannu ta dinkin labule?

Film gaskiya tun ina karama nake sha’awar film, na kan tara kannena muna wasan kwaikayo, don haka da shi na tashi. Aikin asibiti kuwa kowa ya san albashi na sai karshen wata, wani watan kafin ya zo ka cinye su. Dinkin Labulaye kuwa wata ran a samu wata ran kuma babu dinkin, sannan kuma ina da masu taya ni dinkin labulen idan ya samu. Aikin asibiti kuwa, wata ran wataran da safe, wata rana da dare wataran kuma hutu, Kinga ina da lokuta.

Mun ji kin ce kina Dj na biki da nasihar ma’aurata da tarbiyar yara, shin ta yaya kike hada dawainiyar aikinki na asibiti da sauran ayyukanki?

DJ yawanci sai da yamma, ko da daddare muke zuwa, kuma an fi yi Juma’a, Asabar, Lahadi. Nasihar ma’aurata kuma idan na dawo daga aikin safe sai su zo su same ni, ai ita nasihar magana ce da baki, haka ma tarbiyar yara ita ma magana ce, don haka duk abinda ka dauka da sauki to zai zamo da saukin, haka ma Idan ka dauki abu da wahala to dole wahalar zai zamo maka. Dalilin yawan sana’ata ita ce Wallahi ina da dangin mahaifiyata da yawa, a Gombe haka ma dangin mahaifina suna da yawa a Tudunwadar dan kade, kuma ina da dangin mahaifina a Rano, suma suna da yawa, don dangin babana ban san yawansu ba.
Kuma kowa so yake na yi masa, shi ne dalilin yawan sana’ata, ga kuma yara da ‘yan ‘uwa da muke ciki daya da ‘yan uba, da abokan arziki, don ni Wallahi ko tafiya nake a kan hanya idan na ga wasu sai kawai na ji ina ma ina da kudi na ba su, ga irin su Wasilan Kaduna suma da da kudin sai a yi wa yaransu kayan sallah. Kuma yanzu haka ma Ina son bude gidan abinci, in Allah ya yarda. Sai da na yi wa Malam Daurawa magana ina son in dinga zuwa Rugagen Fulani don In dinga koya musu Karatun Islamiya, kin san ba su da Islamiyya. Ya ce to, kin san su ma Malamai abubuwa suna musu yawa, Allah ya sa mu dace.

Kin ce kina sha’awar aikin soja don Suna burge ki wace shawara za ki ba wa mata masu aikin soja?

Gaskiya Soja na burge ni, shawarar ita ce, a duk in da suke su rike addininsu, Ina kuma yi musu fatan Alkhairi.

Wace shawara Za ki ba wa mata masu sha’awar shiga harkar Fim?

Shawarar ita ce, su yi aure, amma idan Allah ya kaddara sai sun yi to Shike nan, sai su tsarkake zuciyar su, su kuma rike Sallah, idan kuma suka samu Mijin aure nagari to su yi aurensu, don su sami ‘ya’ya nagari.
Wane kira za ki yi ga mata matasa da matan aure masu shaye-shaye
Allah ya shirye su, kuma su ji tsoron Allah, sannan su kiyaye lafiyarsu, don shi shaye-shaye ba talauci ba ne, ba kuma kudi ba ne, kuma yana rage tunani mai kyau, sannan yana haddasa man tuwa. ‘Ya’yan talakawa suna yi, ‘Ya’yan masu kudi suna yi, ‘yan kauye na yi, Kai a yanzu Fulanin daji ma suna yi, Allah ya shirye mu baki daya.
I
Muhimman Abubuwa Biyar (5)  Da Yakamata Ka Sani Game Da  Ado Gwanja

Muhimman Abubuwa Biyar (5) Da Yakamata Ka Sani Game Da Ado Gwanja

Ado Isa Gwanja wanda aka fi sani da Ado gwanja, jarumin barkwanci ne a dandalin masana'antar Kannywood kuma hazikin mawaki ne.
Jarumin wanda tauraron sa na cigaba da haskawa a fagen nishadantarwa ya samu karbuwa a zukatan masoya masu bibiyan fina-finan hausa.
Hakazalika yana da farin jini a fagen waka musamman daga mata duba da irin wakokin biki da yake rairawa. Bisa ga wannan dalilin aka yi masa lakabi da 'limamin Mata'.
Advertisement
Mawakin yana daya daga cikin fitattun yayyan kamfanin White house Family wanda Adam A.Zango ke jagoranta.
Sanin kowa ne cewa Zango maigidan sa ne hakazalika shima mawakin baya boye ma jama'a dangatakar dake tsakanin su.
Mun kawo maku wasu abubuwa biyar da muke son ku gane dangane da jarumin kamar haka;

1. Shi ruwa biyu ne

Duk da cewa shi dan asalin jihar Kano ne, Mahaifin sa dan garin Warawa ne dake Kano kuma mahaifiyar sa yar kabilar shuwa Arab ce daga jihar Borno.

2. Karatun sa

Ado Gwanja yayi karatun firamaren sa a makarantar Babbangij i dake Karkasara . Sannan yayi karatun sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa .
Bai samu ya cigaba da karatun sa bayan bayan Sakandare. Bayan rasuwar mahaifin sa jarumin ya shiga buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo shi zuwa ga matsayin da yake yanzu.

3. Harkar waka ya fara.

Yawanci ana ganin cewa jarumin ya fara da harkar sai dai a yanda ya bayyana, ya fara aiki a masana'antar nishadi ta fagen waka. Yace sama da shekaru 12 yake waka sai dai kuma a wancan lokacin ba'asan shi kana bai samu kudin shiga situduyo ba don buga waka.

4. Wanene gwanin sa

Hakika dangantakar shi da sauran mawaka mai kyau ce kuma akwai girmamawa tsakanin, mawakin yace babban gwanin sa a wannan harkar shine mawaki Aminu Maidawayya.

5. Dalilin da yasa ya fiye yin wakar mata

Sanin kowa ne cewa hazikin mawakin ya fiye yin wakokin biki wanda ana iya cewa wakokin mata ne sai dai mafi yawanci ba'a san dalilin da yasa ya shahara a wannan fagen ba wanda yasa ma har ake kiran sa da 'limamin mata'.
A cewar shi dalilin da yasa yake yin wakokin mata shine domin mata sune iyayen biki kuma masu iya magana sukan ce inda baki ya karkata ta nan yawu kan zuba.

Thursday, 20 September 2018