Labarai

Yau Litinin 6/11/2023 Kotu Za Ta Fara Zama Akan Shari’ar Abba Da Gawuna

Akwai fargaba a jihar Kano yayin da kotunan daukaka kara ke shirin sauraron karar da Abba Yusuf ya shigar yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta tube shi daga mukamin gwamna.

Kotun, a sanarwar da Sunday Vanguard ta gani, ta nuna cewa za a saurari karar mai lamba CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 a gobe a kotun daukaka kara da ke Abuja.

Yau Litinin 6/11/2023 Kotu Za Ta Fara Zama Akan Shari’ar Abba Da Gawuna
Yau Litinin 6/11/2023 Kotu Za Ta Fara Zama Akan Shari’ar Abba Da Gawuna

Jam’iyyun da ke cikin karar sun hada da Yusuf, jam’iyyarsa, New Nigeria Peoples Party, NNPP, All Progressives Congress, APC, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.

Ku tuna cewa kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Kotun ta soke zaben Abba inda ta bayyana cewa kuri’u 165,663 na sa ba su da inganci, inda ta ce ba INEC ta sanya wa hannu ko tambari ba.

INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.

Sai dai bayan da kotun ta cire kuri’u 165,663 daga maki Yusuf, an rage masa kuri’u zuwa 853, 939, wanda ya haura kuri’u 30,000 kasa da kuri’u 890,705 da Gawuna ya samu.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button