Labarai

Tutsun na’ura muka samu, bamu yafewa kowa bashi ba – MTN

Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewar kuskuren na’ura ya sanya mutane suke ganin cewar kamar an yafe musu bashin da ake binsu na kati ko kuma Data da suka ranto daga kamfanin.

Da safiyar yau dai masu amfani da kamfanin sadarwa na MTN suka tashi da mamakin ganin cewar duk wani bashi da kamfanin sadarwar ke binsu yayi batan dabo,wato kamar dai an yafe masu bashin kenan.

Kamfanin dai ya bayyana cewar kwastomominsu waɗanda suka yi imanin kamfanin sadarwar ya soke basussukan su da gangan, sun je shafukan sada zumunta don murna tare da godiya ga kamfanin sadarwa.

Misali, wata mai biyan kuɗi mai suna Ada, ta rubuta a shafinta na WhatsApp, tana cewa an biya bashi. Masu bin bashin MTN Check your account, MTN don clear una gbese.Tutsun na'ura muka samu, bamu yafewa bashi ba - MTN

A halin da ake ciki kuma, wani martani daga wani jami’in MTN, ya bayyana cewa masu amfani da layin za su ci gaba da biyan basussukan da ake bin su, inda ya kara da cewa masu amfani za su dauki nauyin biyan kudaden da ake binsu ko da bayan MTN sun gyara matsalar da ta sa basussukan suka bace. daga asusun su.

Ya bayyana cewa bacewar basussukan da aka samu a asusun masu biyan kudi wata matsala ce, wanda hakan ke nufin masu biyan bashin za su rika biyan basukan da ake cewa an cire da zarar MTN ta gyara kuskuren.

Kuma babu wani wanda aka yafe wa bashin da kamfanin MTN yake binsa kamar yada suke fadi a shafukan sada zumunta da sauran wurare.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button