Labarai

Tsadar rayuwa: ‘Yan Nijeriya Na Sayar Da Motocinsu Don Sayawa Iyali Abinci – Rahoto

Rahotanni sun nuna cewar wasu ‘yan Nijeriya da matsin tattalin arziki ya shafe su.
Mallakar mota na daga cikin jerin nasarorin da mafi yawan ‘yan Nijeriya ke ganin sun samu,yayinda ake biki a gidaje idan wani ya sayi mota a wasu yankunan.

Iyaye da ’yan uwa da abokan arziki su taru wajen yin addu’o’i ga Allah daban-daban domin ceto ran mai motar da ita kanta motar.

Tsadar rayuwa: 'Yan Nijeriya Na Sayar Da Motocinsu Don Sayawa Iyali Abinci - Rahoto
Tsadar rayuwa: ‘Yan Nijeriya Na Sayar Da Motocinsu Don Sayawa Iyali Abinci – Rahoto

Sai dai kuma halin da kasar ke ciki a yanzu ya sanya wasu masu motoci su sayar da motocinsu, a kalla, don ciyar da iyalansu yadda ya kamata, jaridar dimokuraɗiyya na ruwaito.

Economy & Lifestyle ta gano cewa hatta masu son mota a yanzu suna sayen na Najeriya da aka yi amfani da su, maimakon wadanda ake shigo da su cikin kasar, wadanda aka fi sani da motocin Tokunbo.

A yau, mallakar mota an daina kidaya shi a matsayin nasara sakamakon yada sayen motar ya zama larura ga wasu.

Wadanda ke siyan motocin da aka yi amfani da su a Najeriya, bincike ya nuna, ba su taba yin hakan don jin dadi ba amma galibi don safarar kasuwanci kamar Uber, Bolt da inDrive, da sauransu.

Mista Salami Shotunde, wani ma’aikaci, ya ce sai da ya sayar da motarsa bayan ya ajiye ta na kwanaki a gidansa, saboda gazawar da ya yi mata a wannan karin farashin man fetur.

Na yi bakin ciki sosai a halin yanzu da yawancin ‘yan Najeriya ke rayuwa cikin matsi kamar dai ni,domin sai da na siyar da motata sannan na samu na sayi abinci.

Dole ne in sayar da samfurin Toyota Camry dina, 2006, bayan ajiye shi a gida na tsawon watanni.

Sayen mai yana da tsada kuma kasuwanci ba ya tafiya ko kadan. Abu mafi mahimmanci a yanzu shine kasancewa cikin koshin lafiya, kuma ciyarwa shine babban sashi a ciki.

Don ciyar da iyalina, dole ne in sayar da motata inji shi.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button