Kannywood

‘Tawali’u ne ya hana rarara bayyana cewa ya yi karatun digiri a jami’a – mai kare martabar Rarara

Bayan hirar da dauda kahutu rarara yayi da yan jarida ana cewa yakamata a bashi minista biyu idan ma daraktoci ne idan aka raba ya kamata a bashi sha biyar idan an baiwa wasu goma.

Maganar kowa yana dubin ta da rashin sanya tunani da hankali a wannan furuci domin kuwa ko Abdulmajeed almustapha kwamanda wanda anka fi sani da dan balki kwamanda yace taya rarara zaka fadi yakamata ayi shawara da kai duk mutanen da sunka baiwa wannan tafiya gudumuwa mafiyoyi ne amma ba’a yi shawara da su sai dai mawaki.

'Tawali'u ne ya hana rarara bayyana cewa ya yi karatun digiri a jami'a
‘Tawali’u ne ya hana rarara bayyana cewa ya yi karatun digiri a jami’a

To shind Jaridar Dclhausa inda wakilin du zaharadeen dutse kura ya samu zantawa da wani masoyi dauda Kahutu rarara mai suna jamilu dan kuda mai kare martabar rarara inda yake cewa rarara fa yayi digiri.

Ga abinda yake cewa a zantawar tasu.
“Rarara yayi digiri muna da cikakkiyar sheda tabbas yayi digiri shiyasa munka fito mu gayawa mutane su gautar da wannan jita jita da zancen banza bai isa yayi kaza ba.

Kuma ni abinda yake damu na yau rarara cewa yayi ya cancanta a bashi minista, ba cewa yayi a bashi minista ya rike ba, yau din nan ka bawa rarara minista dauka zaiyi ya bawa wani kuma dan arewa zai bawa”- inji dan kuda.

Mai tambaya: shin kace abinda kowa yake tin ƙaho da yayi karatu rarara ma yayi digiri wane fani ya karanta kenan?

” Ai na riga na fada “mass communication ” ya karanta ma’ana ya karanci fanin aikin jarida a makarantar “open university a online”kuma na fada duniya ta sani, kuma ina gayamu ku cewa nan gaba zamu bayyana takarda shaidar karatun dauda kahutu rarara wato satifiken dinsa duniya ta gani ta shaida.
Rarara sai da ya kwashe shekara hudu yana karatunsa ba maganar sayen satifiket ankayi ba – inji dan kuda.

A nasa ra’ayi yace wai da anyi magana sai ace mutum bai iya turanci ba shi yanzu idan ya samu ya zama shugaban kasa najeriya ka ma isa kayi magana da turanci wani yanayin taro ko da manema labarai.

Zakayi maganar ka da hausa yadda irin wasu ƙasashen duniya suke magana da yaren su iyan saudiyya kayi da labarci, china suke yi da ya rensu amma mu, mun ci baya a siyasance wai dole sai kayi turanci -inji dan kuda.

Ga bidiyon nan domin sauraren cikakken firar.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button