Labarai

Sheikh Dahiru Bauchi ya baiwa Falsɗinawa Kyautar Naira Miliyan 100

Sheikh Dahiru Bauchi ya bada wannan gudummawa ne lokacin da aka karanta
masa wasikar da babban dan Shehu Ibrahim Nyass Khalifa Sheikh
Muhammadul Mahiy Inyass ya rubuto wa dukkan Almajiran shehu Ibrahim
cewa su taimaka a tara dala miliyan guda da ya yi alkawari cewa za’a
baiwa Falasdinawa da yaki ya tagayyara.

Babban Malamin Addinin Musuluncin kuma jagoran Darikar Tijjaniya,
Maulana Sheik Tahir Usman Bauchi. Ya shaida bada gudumawar naira
Miliyan dari daya (#1000,000 Million) wanda ya yi daidai da dalar Amurka dubu dari na kashin kansa, majiyarmu ta voa hausa na ruwaito.

Ga abinda wasikar ta kunsa daga bakin mai Magana da yawun Shehu Mahiy
a Najeriya.

Wakilin sheihin malamin ya ce, a cikin wasikar da ya rubuto, Khalifa Sheikh Muhammadu-l-Mahy Inyass, ya ari bakin almajiran shehu Ibrahin Inyass ya ci albasa inda ya yi alkawarin baiwa Falasdinu gudunmawar dalar Amurka miliyan guda sannan ko wani muridi, ko ma ba muridi ba ko dan Tijaniyya, in dai mutum Musulmi ne domin wannan batun ya shafi musulmi ne. Ya ce Shehu Ibrahim yana ta kokari da Filadinu tun yana raye, gashi kuma yanzu ana kashe su; dole mu musulmi ne zamu taimaka musu.

Bayan karanta wannan wasikar, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce shi zai ba da naira miliyan dari, sannan kowa ya fadi gwargwadon nawa zai iya bayarwa a duk fadin Najeriya. Kuma duk wanda ya ce shi almajirin Sheikh maulana ne kuma almajirin shehu Tijjani ne, wannan ya zama wajibi tunda umarni ne daga khalifan mu. Amma sauran Musulmi da ba ‘yan Tijjaniyya ba, bai zama musu dole ba, a cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi .Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button