Labarai

Sanarwa gayyatar yan Kannywood daga Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta nemi Jarumai da Masu Shiryawa da Ba da Umarnin Fina-finan Hausa su kai kansu gabanta ranar Litinin 13-11-2023 da karfe 2 na rana.

Hisbah ta ce zaman da za ta yi da Yan Kannywood na cikin jerin hanyoyin da take bi don wayar da kai da nasiha domin samar da gyara a jihar Kano.

Sanarwa yan gayyatar yan Kannywood daga Hisbah
Sanarwa yan gayyatar yan Kannywood daga Hisbah Hoto/facebook: Malam Aminu Ibrahim Daurawa

A farkon makon nan ma dai Hisbah ta yi makamancin wannan zama da Taurarin TikTok.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Kano Dr. Mujahid Aminuddeen ya yiwa Freedom Radio karin bayani kan gayyatar da suka yiwa yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Babban kwamandan hisbah na kano ya sake bada sanarwa a wancan sati alhamdulillahi wancan satin mun kira yan titkok mun zauna da su alhamdulillahi , zaman ya haifi da mai ido an zauna anji tsare tsaren su ,mun basu dokoki wanda in sha Allah akwai karatu ga mai so, akwai sana’a ga mai so, akwai jari ga mai so.

Kai har ma ga aure kamar yadda baban kwamandan yake cewa za’ayi auren yan titkok to a yanzu shine yanzu kau da badala zamuyi kira mun kira ‘ya’yan yanzu muna so mu kira manya, wannan sati kannywood muke so kwanta da kwarkwatarsu.

“Furodusa ne kai na kannywood babban kwamandan hisbah yana kiranka, darakta ne kai na kannywood babban kwaman hisbah yana kiranka,hafiz ne kai celebrity ne na kannywood babban kwamandan hisbah yana kiranka.

Wanda kawai munka jingine bazamu kira su ba yanzu sune mawaka, amma yanzu amma wadanda guda ukku da wanda yake fitowa shiri , da mai shirya dirama din da mai design din dirama duk wadannan muna neman su da izinin Ubangiji ranar Litinin da karfe 2 muna neman su.- inji mataimakin babban kwamanda.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button