Rarara ya sake zunguro sama da kara a wata sabuwar hirarsa


Gidan rediyo rfi hausa sun samu tattaunawa da dauda kahutu rarara akan kalamansa da na tayar da kura a kafaffen sada zumunta na arewacin najeriya akan gwamnatin ta da shude da caccakar tsohon shugaban kasa muhammadu buhari.
Mutane wasu suna Allah wadai da irin butulcinsa wasu kuma suna nuna cewa ae wannan dabi’a ce ta makori kamar karuwa ne, amma mawaka basa son ana kiransu da wannan kalma ana alakanta su da kare,ga yadda zantawar ta kasance tsakanin rarara da rfi hausa.


“Na fada na kara fada ita gwamnatin tasan abinda ake ciki amma ta kasa fitowa ta fadawa mutane da an yarda na kaiwa gwamnati wannan bayyani asiri da shikenan”
Wai Miyasa tun wancan lokaci baka fito ka fadi hakan ba sai yanzu?
” A wancan lokacin muna igiyar zato ne idan za’a zagi buhari sau dubu dari takwas da hamsin ni ake zagi nafi kowa zaƙalƙalewa duk wanda yayi gwamnatin buhari nafi shi bada gudunmawa har shi buharin na fishi bada gudunmawa”
Shawararin da ka bada ne ba’a karba ba ko dai baka samu damar kaiwa bane?
“Ai a gwamnatin buhari ba wanda zai saurare ka balantana ka bada shawara duk ministocin da anka naɗa kana fara magana da shi zai ce maka shi ba ɗan siyasa bane balantana su maku santan shi indai ba kudi zaka basu ba, ba za su magana da kai ba, kullum in zagi ne ,mu za’a zaga.
Miyasa zaka iya samun ganin shi a wancan lokaci?
” Waye zai iya samun ganin shugaban kasa ba ma ni kadai bane shiyasa na fito nayi magana , duk wanda yake gani na samu wani abu a gwamnatin buhari ko dani ake shawara ya tabbatar da badani ake ba.”
Miysa tunda ka saba aika sakonka a wakance bakayi ba tsoro ne kaji kayi wata waka mai alamar hannunka mai sanda?
“Yanzu waka nazo nayi, ai ba waka nayi ba ae cewa nayi ministan kudi, ministan noma , ministan tsaro, ministan mai, ministan ilimi, hukumar NSA, ministan kudi su fito suyiwa al’umma bayyani kasar nan a jagwalgwale take, buhari ya ja gwal gwala ta babu wani parastasal da yake mosti sai wanda anka motsa , wannan shawara nake bayarwa su fito su fadi gaskiya – inji Rarara.
Ga bidiyon nan.