Labarai

Matar gwamnan Abia ta raba sanduna 100 ga makafi a jihar

Uwargidan gwamnan jihar Abia, Priscilla Otti, a jiya Talata, ta bayar da gudummawar fararen sanduna guda ɗari ga makafi a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rawaito cewa, an raba sandunan ne a yayin wani biki da aka shirya don tunawa da ranar wayar da kan jama’a kan amfani da sanda da kuma kare lafiyar nakasassu ta duniya a jihar.

Matar gwamnan Abia ta raba sanduna 100 ga makafi a jihar
Matar gwamnan Abia ta raba sanduna 100 ga makafi a jihar

Majiyarmu ta daily Nigerian Hausa na ruwaito.Ana dai gudanar da bikin ranar a duk fadin duniya a ranar 15 ga watan Oktoba, domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin sanda a matsayin wata hanya ta tallafa wa makafi, amma a bana sai gwamnatin ta maida bikin ranar 31 ga Oktoba.

Taron, wanda kungiyar makafi ta kasa reshen jihar ta shirya tare da hadin gwiwar ofishin uwargidan gwamnan da ma’aikatar mata, an fara shi ne da tattaki, inda bayan nan aka gudanar da taron karawa juna sani a sakatariyar ma’aikatar.

A cikin jawabinta, uwargidan gwamnan ta gaya wa wadanda suka ci gajiyar sandunan cewa farar sanda “na nuna ‘yancin kai kuma yana nuna juriya da jajircewa a garesu su kewaya duniyar da sau da yawa ta ke a ɓoye a gare su”.

Otti, wacce mataimakiya ta musamman kan harkokin mata ga gwamna Chinwe Onyeukwu ta wakilta, ta ce gwamnati ta himmatu wajen aiwatar da dokar nakasassu ta jihar.

Ta ce nan ba da dadewa ba za a kafa hukumar kula da nakasassu a jihar.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button