Labarai

Mata na neman kotu ta raba auren ta da mijinta saboda zai ƙara aure

Wata matar aure mai suna Sadiya Bashir ta nemi a raba aurenta a wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa Kaduna, kan shirin mijinta na sayar da gidansu da kuma auren wata matar.

Mai shigar da karar ta shaida wa kotu cewa mijinta, Abdullahi Haruna ba ya ciyar da ita da ƴaƴansu goma jaridar daily Nigerian hausa na ruwaito.

Sai dai Haruna ya tabbatar da cewa yana son ya auri wata mata amma ba shi da niyyar siyar da gidan.

Ya ce ya kasance yana ciyar da iyalinsa daidai karfinsa, inda ya bayyana cewa yana zaune lafiya da matarsa, har sai da shirinsa na auren wata ya taso.

Alkalin kotun, Muhktar Mu’azu ya umarci ma’auratan da su gabatar da shaidunsu a gaban kotu a ranar 14 ga watan Nuwamba.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button