Labarai
Mai kamfanin facebook mark Zuckerberg ya samu rauni an masa aiki


Mai kamfanin Meta ( Facebook), Mark Zuckerberg, ya hadu da tsaustayi a gwiwar a yayin da yake karbar horo na gasar Takwando wanda takai har sai da aka masa tiyata.
Zuckerberg dai ya hadu da tsautsayin tsagewar kashi (ACL) inda ya bayyana hakan a shafin sa na Instagram ranar Juma’a.
Sakon da ya rubuta kamar haka, “Ina samu lafiya.”
“Na gode wa likitoci da tawagar ma’aikatan jinya da ke kula da ni.
“Na hadu da tsaustayin gocewar kashi ne a lokaci da nake atisaye gasar MMA wanda za a yi a farkon shekara mai zuwa, amma jinya ta sa na sami jinkiri .
”Ina fatan komawa fage bayan na warke.
“Ina mika godiya ga duk wadanda suka nuna min kauna da kulawa.”