Kannywood

Maƙiya ne suka yi wa Rarara Sammu ‘asiri’ – inji Aminin Rarara

Fitaccen mawakin Dauda kahutu rarara ya tayar da kura a lokacin da yayi fira da manama labarai inda yayi kalamai sosai akan gwamnatin da ta shude ta muhammadu inda ya caccaki shugaban kasa Muhammadu buhari.

Wannan kalamai da dauda yayi akan shugaba Muhammadu buhari sun tayar da ƙura sosai shine wani dan jarida mai amfani da kafar sada zumunta Bashir yahuza Malumfashi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda yake cewa.

“Wani aminin shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Taskar Gizago cewa wasu maƙiya ne suka yi wa mawaƙin Sammu, shi ya sanya ya shiga soki burutsu, yana neman susucewa.

“Ba wannan ne karon farko da maƙiyan Rarara ke neman shi ta hanyar matsafa da bokaye ba. Amma wannan karon sun same shi, domin kuwa yadda ya fara sukar Shugaba Buhari, mutumin da a sanadiyyar shi ya samu ɗaukaka a duniya, to lallai ina jin tsoron wataƙila ya tada kabbarar durƙushewa. Sai dai wani ikon Allah.” A cewar aminin nasa.

Mutane sunyi martani sosai a karkashin wannan maganar.

@Abba Rabiu adamu yana cewa :

Wannan ai shaci-faci ne! Sai an yi abu ku nuna ku ƴan Ahlussunnah ne, amma yanzu na ga kamar ka na yarda da tsafi? Don Allah mu cire son zuciya mu dinga kallon abu a tsaye. Rarara ai butulci halinsa ne. Mu na Najeriya ya yi waƙar Zuwan Mai Malafa Kano Gwamnatin Tarayya ta kama shi duk tsatsonsu babu wadda ya isa ya ƙwato shi Kwankwaso su ka yi shige-da-fice su ka karɓo shi amma babu irin cikin mutuncin da Kwankwaso ba ya gani a wajen Rarara ba. Rarara ai na daɗe da kallon masa jahili, mara wayewa wadda tarbiyya ba ta ishe shi ba.

@safiyanu usman sallau dantutture abinda yake cewa :

Wlh babu Wani wanda yayi masa Wani asiri kowani tsafi halin sane na cin mutuncn mutum idan ya bar mulki
shi a tunanin sa buhari irin su kwankwaso ne da shekarau bai San wanene buhari ba da talakawan nageria sai yanzu zai gane daman duk mutumin da bashi da aiki sai cin mutuncn masu mutunci toh wata rana zai taba wanda shine karshen sa
Allah yasa mudace.

@habeeb abdurrahman mainamuni ga abinda yake cewa:

Matsafa da masahirta sune suke saurin cewa anyi musu ko anwa wani sihiri ko tsafi mu bamu da wata alaqa dashi yaje chan ya yanka ko karatun al-qurani yake ko tafsiri yake koyarwa dama wata rana zai tafi ballantana wakokin da ba na ilimi da fusaha ba se bambaɗanci da zambo da maula ya iya babu wani abin burgewa ga wakokin sa inkaga Wanda waƙarsa take burgewa to mutum ne Wanda zuciyarsa tacika da hassada da bakin ciki da kuma mutuwar zuciya..

@Abubakar Alkantamawy nakowa ga abinda ya rubuta :

Lallai masu yi masa sammun nan sun jima kuwa da fara yi masa sammun akramakallahu!

1- Sun raba shi da Shekarau
2- Sun raba shi da Kwankwaso
3- Sun sa ya yi wa duk wasu wadanda ya ci moriyarsu zambo.

Allah ya ba shi lafiya.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button