Labarai

Labarin Ellie da ake tsokana da ɗan birin Africa akwai ban tausayi da mamaki

Labarin wannan ellie da mutanen gari suke tsokana da irin hallitar da Allah yayi masa wanda har suke masa lakabi da ɗan birin afrika.

Mutanen gari suna cewa masa dan biri dan biri wanda har takai wannan abun ya shafi ƙwaƙwalwarsa duba da yana yaro ya dauki cewa tabbas shi ba mutum bane daban ne.fitaccen mai amfani da kafar manjaha abis fulani ya kawo rahoton bidiyo shafinsa inda yake cewa:

Labarin Ellie da ake tsokana da ɗan birin Africa akwai ban tausayi da mamaki
Labarin Ellie da ake tsokana da ɗan birin Africa akwai ban tausayi da mamaki

“Har takai mutane suke tura shi bisa icce idan sunka gansa suna dan biri dan biri, wani lokacin su kan kama yi masa ihu da jifarsa suna wani lokacin har sai mahaifiyarsa ta je ta kamo shi, wanda ya san wannan tsangwama da tsokaci da mutane suke masa ya fara ƙyamar ganin mutane yana ganin su zai fara arar na kare ya gudu.

Wani abun ban mamaki a garin ba iya kadai yara yan uwansa ba harda manya manyan mutane tsokanarsa suke shine daga nan yaga bari kawai ya bar musu garin su ya tare a daji , Allah yayiwa yaron baiwa dan banzar gudu mahaifinsa sai tayi da wayo take kamasa ta mayar da shi gida.

Abun ban takaici ba’a bar mahaifiyar Ellie hakan nan ba wasu har munanan kalamai suke jefa da cewa taje ta kwanta da wani dan birin ne shiyasa ta haifi mai kama da biri, wanda ta sanya mahaifiyar ellie abun ya dame ta ta fito duniya ta gayawa mutane cewa:

“Ellie shine ɗan ta na shidda duk ‘ya’yanda ta haifa mutuwa suke dan haka ellie shine kadai abinda Allah ya bar mata wanda ta dauke shi kyauta ne daga Allah tana son abin ta “-inji mahaifiyar ellie.

Masana binciken harka cututtuka ta gano cewa ellie yana dauke da cuta wanda ake kira da suna. “microcephaly” da take damun ƙwaƙwalwar sa.

Allahu Akbar, Allah yana son bayinsa fiye da tunanin kowa bayan irin ganin labarin sa ya karade duniya sai ga ellie ya zamo mutum an fitar da iyayen sa daga cikin talauci ya zamo dan gaye, yana zuwa makaranta yanzu haka.

Ga bidiyon nan ku kalli irin yadda ya fara rayuwa har Allah ya canza abunsa.

@abis_fulani Labarin Ellie me abin tausayi da mamaki wanda mutan gari ke tsokanarsa da dan birin Africa😢 #abis_fulani #hausa #kano #africa ♬ original sound – Abubakar sadauki👑👑Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button