Kannywood

Kanwata tana cikin tsananin rashin lafiya a hannun yan bindiga – Bilkisu shema

Fitacciyar Jarumar Kannywood dake arewacin Najeriya, Bilkisu Shema, ta bayyana takaicinta bisa halin da kanwarta da sauran wasu dalibai ke ciki a hannun yan bindiga a jihar Zamfara , jarumar ta samu zantawa ne da shafin gidan jarida Dnn hausa.

Ta kara da cewa tun daga lokacin da wasu yan bindiga suka saxe kanwartata maisuna Hafsat Shema a makaranta dake garin Gusau a jihar Zamfara suka shiga tashin hankali.

Kanwata tana cikin tsananin rashin lafiya a hannun yan bindiga - Bilkisu shema
Kanwata tana cikin tsananin rashin lafiya a hannun yan bindiga – Bilkisu shema Hoto/Instagram: Bilkisu shema

Acewarta a ranar larabar nan Hafsat ta kira gida inda take sanar da cewa tana kwance babu lafiya a cikin daji a hannun yan bindigar.

“Kanwata hafsat shema tana wajen yan bindiga wajen wata daya kenan wanda suna bata dama ta kira, inda ta kira yan gidan mu su ukku take fada musu cewa tana cikin tsananin rashin lafiya yanzu haka a kwance take bata da lafiya”-inji bilkisu shema.

Saboda haka ne Bilkisu ke kara rokon gwamnatin Najeriya, ta kara ko kari domin kubutar da mutanan da ‘yan bindigar ke rike dasu a hannun su.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button