Kannywood

Hukumar tace fina finai ta dakatar da Malam Ali na kwana casa’in daga fim na shekaru biyu

Fitaccen jarumin nan Abdul saheer da anka fi sani da malam Ali na kwana casa’in wanda ake ganin wasu bidiyo dinsa na yada badala a kafafen sada zumunta.

Shine hukumar ta kira shi domin tattaunawa da shi akan wannan bidiyo da ake zargin sa, majiyar mu ta Freedom Radio kano ta wallafa wannan sanarwa a shafinta na sada zumunta a facebook inda take Cewa:

Hukumar tace fina finai ta dakatar da Malam Ali na kwana casa'in daga fim na shekaru biyu
Hukumar tace fina finai ta dakatar da Malam Ali na kwana casa’in daga fim na shekaru biyu Hoto/Bbchausa

“Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta dakatar da Jarumi Abdul Saheer da aka fi sani da Malam Ali Kwana Casa’in daga Fina-finan Hausa har tsahon Shekaru biyu.

Hukumar tace hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka yi a kansa na cewa yana yada bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.

Hukumar ta ce ta gayyace shi amma ya bijirewa amsa gayyatar ta.”

Ga bidiyon nan ku saurara daga bakin abba elmustapha

 

Martanin mutane akan wannan magana.

 

@Barista Ibrahim Yusuf yana cewa :

Allah yasa nan gaba a dakaar da Ali Nuhu.

@Dahiru darancy zarewa ga abinda yake cewa :

Yayi daidai saidai Matsalar Majority na Jagororin Firlms Sunayin Waɗannan Baɗalar shi Tasace Tafito Fili Kawai.

@Mus’ab Abdul ga abinda yake cewa:

Wannan hukuncin yayi dai-dai. Duk wanda taka doka.doka ta takashi.kowaye shi.koda Ali nuhu ne da adam a zango da suke koyawa yaran mutane yadda ake raye-raye.Allah yasa mudace.

@Muhammad Auwal Dz ga abinda yake cewa :

Masha Allah, wlh dama wannan mutumin barin irinsu a wannan masana’anta ba karamin illa ba ne, hakan yayi daidai, insha Allah idan Gawuna yazo zai dora akan wannan kyakkyawan aiki.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button