Kannywood

Hisbah ba ta biyo hanyar neman ganawa da Yan Kannywood ba – Umar UK

Hukumar hisbah ta jihar Kano karkashin kwamandan hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya fitar da sanarwa ganawa da jaruman yan fim kamar yadda sanarwa ta fito ta mataimakin babban hukuma hisbah.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Kano Dr. Mujahid Aminuddeen ya yiwa Freedom Radio yayi bayani kan gayyatar da suka yiwa yan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Hisbah ba ta biyo hanyar neman ganawa da Yan Kannywood ba -  Umar UK
Hisbah ba ta biyo hanyar neman ganawa da Yan Kannywood ba – Umar UK Hoto/fimmagazine

Shine daya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkat kannywood umar uk mai shirya fim yayi martani akan wannan sam ba’a biyo hanyar da ya dace ayi zama da su ba kamar yadda tattaunawar su da freedom Radio ta kasance inda yake cewa:

“Ni bani da jarumar kamar yadda ka fada kuma ni bani da wani labari na gayyata, na ga dai abu ga rediyo ko soshiyal midiya ko jarida ance ana gayyatar yan fim jarumai da masu shirya fina finai da daraktoci a inda na shigo masu shirya fina finai , inda ance ana gayyatar jarumai babu ni a ciki kuma bazan saurari ma abun ba.

Amma nasan masu shirya fina finai nasan irina babu wani wanda zai saurari wannan abun saboda Wallahi babu wani mutum ko gwamna ne shi da zaya gayyace mu a titi, kamfani ne da ni, wai ya kira mu babu abinda ya dame ko hisbah ne shi, kamfani ne da ni ina biyan hajari ina da ma’aikata ina biyan komai nawa dai dai.

“Babu wani yace wai yana gayyata ta a titi bazai yiyu ba wallahi babu shi, ban sani ba ko suna da wasu yan fim amma bari muga ranar tazo Allah yasa abun a haka babu wani dan fim da yasan kansa da zai je.- inji umar uk

Ga bidiyon nan ku saurara.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button