Kannywood

Har abada ba zan sake yiwa mata kwalliya a yayin ɗaukar fim ba – Mansur Make-up

Mai sana’ar ƙwalliya a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Mansur Make-up, ya ce ba zai sake yiwa Mata ƙwalliya a yayin ɗaukar fim ba, domin ya gane cewa hakan kuskure a Addinin musulunci da kuma al’ada, wanda a baya Mutane da dama sun nusar dashi hakan, amma yana ganin kamar ba masu ƙaunarsa bane, sai yanzu ya fahimci gaskiya.

Mansur ya bayyana haka ne ranar Laraba cikin wani fefen bidiyo, wanda yayi tsokaci akan kalaman jarumi Abdallah Amdaz bisa yadda yake fuskantar ƙalubale daga abokan sana’arsa, bayan wasu kalamai da ya furta a ranar Litinin din da ta gabata a hukumar Hisbah.

Har abada ba zan sake yiwa mata kwalliya a yayin ɗaukar fim ba - Mansur Make-up
Har abada ba zan sake yiwa mata kwalliya a yayin ɗaukar fim ba – Mansur Make-up Hoto/Mansur make up/Instagram

“Naga wasu suna cewa bai dace malam Aminu Ibrahim daurawa yayi kiransu a hakan ba, amma malam ya ƙara cijewa ya fito yace ya aika takardar a hukumar tace fina finai wanda inda nine bazan fito nayi hakan ba domin naga, akwai wasu ƙasƙantatu da basu kai darajar malam ba , idan sunyi kira daga nan zuwa kaduna ko abuja da tafiyar zata iya kai awa biyar zuwa shidda, amma mutum mai daraja irin Aminu Ibrahim daurawa ya kamata a girmama shi a karba kiran da yayi.

“Malam ya fadi ƙudirorin wannan kira inda yace zakaga mace tazo kana da niyar fim amma ba haka ba.

Abu na biyu zaka ga ana jan aya ko hadisi ko mutum ya fito liman yana bada fatawa ba daidai ba”

Mansur make up ya kara kawo misali akan cewa.

“Yanzu zakaji mace tace a lokacin da zatayi fim sai da tayi tayi kafin ta sha kan iyayenta su aminta tayi fim kaga tun daga nan akwai gyara,amma wasu wallahi karya suke basu shawo kansu ba.

Yanzu cikin masu harka fim din nan akwai masu ‘ya’ya mata duk sun balaga amma babu wanda ke yarda ya kawo yarsa,kanwarsa ko antyinsa kaga kenan akwai matsala.

Yanzu misali kai Malami ne ana so yarka ta zamo Malama da gudu zaka barta , zakaji dadi ma, amma duk wanda yake fim yarsa balagaga tace zatayi fim zai ce a’a , akwai matsala kenan ko? “- inji mansur make up.

Ku saurari sauran bayyani a cikin wannan faifan bidiyo.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button