Labarai

Duk wanda ya san ba zai yi aikin da muka bashi ba to ya ajiye mukaminsa, Tinubu ya gargaɗi ministoci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce duk wani minista da masu rike da muƙamai da su ka san ba za su iya aiki ba to su ajiye mukamansu, in da ya bayyana cewa dole ne ya yi nasara ta kowace hanya don cimma burin ƴan Najeriya da suka kawo shi kan karagar mulki.

'Duk wanda ya san ba zai yi aikin da muka bashi ba to ya ajiye mukaminsa, Tinubu ya gargaɗi ministoci
Duk wanda ya san ba zai yi aikin da muka bashi ba to ya ajiye mukaminsa, Tinubu ya gargaɗi ministoci

Ya bayyana hakan ne a yau Larabar a wajen bude wani taro na kwanaki uku mai taken “Sadar da Ajandar Sabuwar Nijeriya,” wanda aka shirya wa ministoci, mataimakan shugaban kasa, sakatarorin dindindin, da manyan jami’an gwamnati a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana cewa a karshen taron, ya ce za a rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin mahalarta taron da shi kansa, ya ce: “Idan ku ka yi kokari, to babu abin tsoro. Idan ba ku yi ba, za mu duba kuma idan ba za ku iya ba, ku ajiye mana aiki. ”

Shugaban, wanda ya ba su tabbacin samun ƴancin gudanar da ayyukansu, ya kuma shawarce su da su rika yin tambayoyi kan yadda za su gudanar da ayyukansu da kuma lokacin da za su yi.

Don haka ya bukaci ministocinsa da sauran jami’an gwamnati da su taimaka masa wajen samun nasara.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button