Kannywood

Babu adalci a zargin Buhari da lalata Nijeriya -inji Mai Wakar “Nijeriya Sai Mai Gaskiya“

A yanzu mun zo muku da labarin mai bakandamiyar wakar Muhammadu Buhari wanda ya tallata shi ya fito da martaba shi duniya ta sanshi tabbas Ibrahim yala hayin banki mutum ne wanda ya taka rawar gani da bada gudunmawa wadda tafi duk ta wani wani da yake ji ya tallata buhari a kyauta.

Har jiya wa yau an samu tattaunawa ne da Ibrahim yala da jaridar Dclhausa ta gayyato shi domin shima yace wani abu akan kalaman da mawaki rarara yayiwa buhari hausawa kance anci moriyar ganga kenan ga yadda tattaunawar ta kasance da Ibrahim yala hayin banki ta kasance.

Babu adalci a zargin Buhari da lalata Nijeriya -inji  Mai Wakar “Nijeriya Sai Mai Gaskiya“
Babu adalci a zargin Buhari da lalata Nijeriya -inji Mai Wakar “Nijeriya Sai Mai Gaskiya“

“Sunana Ibrahim yala hayin banki wanda ankafi sani da mai bakandamiyar wakar buhari ‘yau najeriya riko sai mai gaskiya’ da kuma ‘mai alkalamin da bai rubuta karya’ cpc anyi shekara takwas na gwamnatin buhari ba’a yi ta dani ba kuma babu abinda zan iya fadi akan gwamnatin muhammadu buhari alhamdulillahi ina rayuwa cikin wadatar zuci da godiyar Ubangiji yanzu idan ka ganin ba’a gayamaka ba zakace nayi minista a gwamnatin.-inji yala

A lokacin da kaji ance tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yaci zabe a matsayinka na mawakinsa me kayi tunanin zaka samu?.

“Eh to tsakani da Allah wani masoyina ko na kusa dani ko na kusa ga masoyina bai taɓa zaton za’a yi gwamnatin shekara ban iya yiwa wani alfarma ba, ba’a cewa ni banda alfarma ba wani da yake tare dani baida wata alfarma mutane basu taɓa tsamnanin haka ba.

Magana ta gaskiya har buhari yayi gwamnatinsa bani da kowa a cikin gwamnatin nima bana ciki amma alhamdulillahi har yanzu da buhari ya sauka daga mulki ina masa fatan alkhairi.

Bazan manta sau daya buhari yana kan mulki yaji labarin zan aurar da diyata ya aikomin da naira miliyan 2 na kira shi nayi godiya, bayan nan babu wani abu da na samu a gwamnatin buhari amma tun a lokacin nake masa fatan alkhairi har yanzu da ya sauka kan ka ragar mulki.- inji Ibrahim yala.

Ga bidiyon nan ku saurari cikin bayyani daga bakin mawakin.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button