Kannywood

Ba mu ji dadin hanyar da hisbah ta bi don gayyatar mu ba – Alhassan kwalle

Kungiyar Jaruman Masana’antar Kannywood ta ce ba ta ji dadin gayyatar da Hisbah ta yi mata ba.

Kungiyar ta ce bai cancani a yi mata irin gayyatar da aka yiwa Yan TikTok ba.

Shugaban Kungiyar Alasan Kwalle na ya bayyana hakan ga Freedom Radio ga abinda yake cewa

Ba mu ji dadin hanyar  da hisbah  ta bi don gayyatar mu ba, irin yan tiktok - Alhassan kwalle
Ba mu ji dadin hanyar da hisbah ta bi don gayyatar mu ba, irin yan tiktok – Alhassan kwalle

“Da farko muna yiwa Allah godiya da kuma hukumar hisbah ta gayyace mu wannan zama domin muna da muhimmanci , amma magana ta gaskiya bai dace ana mana kallon irin na yan tiktok ko wasu mutane daban ba, mu kamfanonin ne da mu, kuma muna da shuwagabanni kungiyoyi na kasa zuwa ga na jahohi.

Kuma muna da uwayen gida masu ruwa da hatsi a wannan masananta ,abin da yakamata ko a wancan lokacin baya da yana kan wannan kujera shi malam Aminu Ibrahim Daurawa mu da kanmu munka nemi mu kawo kanmu .

A taikace dai ko dai a rubuto mana takarda ga hukumar tace finafinai, saboda ita take ruwa da tsaki ga duk wannan kungiyoyin,domin musan waɗanda mutane zamu gayyato ayi wannan zama, amma ace ba’a turo mana takarda ba, ko ace an turo kuma aje gidan rediyo ace ana neman mu a tunanin mu ana neman mune ruwa a jallo “wanted” wannan shi muke tunani a wajen mu – inji alhassan kwalle.

Alhassan kwalle ya kara da cewa kamar mutum ne yayi laifi ana neman shi, magana ta gaskiya muna godiya da wannan gayyata ,amma hukumar hisbah da ta gyara wannan kuskure ta dawo baya wanda zai tabbatar da cewa mu ‘ya’ya ne kuma abokan tafiya ne a wannan ƙungiya tamu inji – alhassan kwalle.

Yanzu zakuji hukumar hisbah a ranar Litinin din ne?

” A’a ai wai ba’a ce kawai a kira ka ta kafar watsa labarai bane ace ana nemanka , kuma ba wani laifi kayi ba, a matsayin ka na mai sana’a, wanda muna da kungiyoyin aƙala kungiyoyin sunkai guda bakwai , wanda kuma muna da kungiya ta kasa da ta jaha , wanda ya kamata ace ta nan aka bi aka turomuna takarda gayyata.

Ta yadda zamu bada lokaci ko idan an bamu lokaci sai mu sasaita lokacin mu,amma a shiga kafar rediyo kawai ace ana nemanka kaga laifi kayi kenan.” -inji alhassan

Alhassan kwalle yayi maganganu na nuna rashin jin dadin su na daukar su kamar yan tiktok ku saurari sauran jawabinsa a nan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button