Kannywood

Abdallah Amdaz ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan sana’arsa yana zubda hawaye

Fitaccen jarumin nan kuma mawakin Afrika abdallah Amdaz wanda yayi fice a cikin shirin mai dogon zango na labarina excellency inda bayan taron su da hisbah yayi maganganu wanda abokan sana’ar suke nuna matsa yatsa da ƙyama saboda ya fadi gaskiya.

Premier radio sun zamu zantawa da shi akan miyasa yayi irin wannan maganganu wanda yake wanke kansa da zarginda suke masa yana zubda hawaye.Abdallah Amdaz ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan sana'arsa yana zubda hawaye

Jarumi kuma mawaƙi a masana’antar Kannywood, Abdallah Amdaz, ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan sana’arsa, inda wasu ke ikirarin cewa ya bata musu suna, don haka zasu daina saka shi a fim, harma wasu na barazanar gurfanar dashi a gaban Shari’a.

A ranar Litinin ne Abdallah Amdaz ya bayyana wasu dabi’u marasa kyau da wasu yan masana’antar ke aikatawa, a wajen taron da hukumar Hisbah karkashin jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta shirya da yan Kannywood.

Sai dai jarumin yace ya bayyana abubuwan da ya fada ne saboda yadda Daurawa yace su fadi tsakaninsu da Allah akan matsalolin da suke so a gyara, wanda yace shi kuma yana ganin yan fim yan uwansa ne, bai kamata su je lahira su na la’antar junansu ba, gwara tun a Duniya ya bayyana gaskiya, tunda dai Abincinsa da ɗaukakarsa na hannun Allah.

“Abinda nasani duk wani dan adam Allah ya halicce akan abubuwa guda ukku ne ɗabi’arsa,mu’amilarsa da addinsa, duk wani dan fim da yasani duk tsawon lokacin da babu wanda na taɓa bara shi ko kayimin nakan dannewa.”- inji amdaz

Ga bidiyon nan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button