Labarai

Yanzu -yanzu: Majalisar dokokin kano ta karama direban adaidaita sahu da kudi naira miliyan 1.5M

Auwal salisu dan adaidaita sahu (keke napep) da ya tsinci kuɗi a kimamin  kudin Najeriya naira miliyan 15 wanda ya nemi mai su a inda ya kai shi amma bai samu ba yazo ya aje kudin a gida.

Bayan yan kwanaki yaji sanarwa a Arewa Radio kano suna cigiya ya dauki lambar waya ya kira domin mayarwa mai kuɗin kayansa, wanda sunka bashi naira duba dari hudu ladan tsintuwa.

Auwal ya samu Alkhairi sosai ta sanadiyar hakan wanda har sabuwar napep wani bayan Allah ya saya masa, to a yau din nan majiyarmu ta samu labarin kamar yadda shafin gidan Jaridar Dimokuraɗiyya na wallafa a shafin ta na facebook cewa.

” Majalisar dokokin Kano ta karrama direban adaidaita sahun da ya tsinci kudi ya mayar da kyautar naira miliyan daya da dubu dari biyar 1.5

Majalisar dokokin Kano ta karrama matashin nan Auwal Salisu Danbaba daya tsinci kudi a baburin adaidaita sahunsa fiye da naira miliyan 15 tare da mayarwa mamallakansu.

Majalisar ta karrama shine a zamanta na Litinin din nan, yayin da Mambobin majalisar suka hadawa matashin naira dubu ashirin da biyar biyar yayin da majalisar akaran kanta ta bashi naira dubu 500.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button