Labarai

Wasu Maza Sun Yi Ma Yan Gudun Hijira Ciki A Katsina

Hukumar bada agajin kaukawa ta jihar Katsina SEMA, ta amshi wasu mata hudu da wata kungiya ta ceto daga hannun bata garin maza a cikin birnin jihar, kamar yadda Katsina Post ta samu daga majiyar ta taJakadiya

Matan hudu da aka sakaya sunansu saboda wasu dalilai sun kasance biyu a cikinsu yan gudun hijira ne sai biyu kuma sun samu sabani ne da iyayensu maza.

A yayin da ta ke yi mana bayani jim kadan bayan amsar matan hudu, Shugabar hukumar ta SEMA, Hajiya Binta Hussaini Dangani, ta bayyana takaicinta dangane da irin wannan rashin i’mani da wasu mazan ke yi.

Wasu Maza Sun Yi Ma Yan Gudun Hijira Ciki A Katsina
Wasu Maza Sun Yi Ma Yan Gudun Hijira Ciki A Katsina Hoto/RFI

Ta ce a cikin yan matan an samu uku masu ciki sai dai daya ta riga ta zubar da nata ta hanyar shan ganyen bidi, yayin da sauran daya cikin ya kai wata takwas dayar kuma ya kai watanni kimanin biyar.katsina post na ruwaito.

Dangani ta ce, a cikin yaran akwai daya da ta san wanda ya yi mata cikin inda ta ce ya dauke ta ne ya kai ta wani gida ya aje ya rinka lalata da ita safe da dare har ta kai ga samun

cikin.
Hakazalika, ta ce su kuma sauran biyun da ke da ciki ba yan gudun hijira ba ne sune suka samu matsala da iyayensu maza sakamakon matayen mahaifansu, suma a cikinsu wani mutum ya dauke daya ya kai wani gida shima ya rinka lalata da ita har ta kai ga samun ciki itama, ya yin da dayar kuma ta ce bata san wanda ya yi mata cikin ba, sai dayar ta hudun ita ba ta da ciki amma dai ta bayyana yadda maza ke daukarta suna zuwa daji suna amfani da ita.

A karshe dai shugabar hukumar ta SEMA, ta ce yanzu haka sun sanar da gwamnan jihar Dr. Dikko Radda sannan kuma su a matakin hukumar sun ba yan matan kayayyakin sawa da sabulan wanka tare da yi masu gwaje-gwaje a Assibiti domin tabbatar da lafuyarsu, kuma daga nan zasu kai su wani gida da za a rinka kula da su tun daga cinsu da sha da kuma basu ilimi na addini da na zamani.

Ta kuma ce, su yan matan da suka samu matsala da iyayensu zasu yi kokarin ganawa da iyayensu domin sasanta su.

Sannan ta jaddada cewa lallai zasu yi bincike domin kamo wadanda suka yi wannan aika-aikar don fuskantar hukuncin da ya dace







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button