Labarai

Tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi – Solomon Dalung

Tsohon ministan matasa da wasanni a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, Barr Solomon Dalung ya yi ikirarin cewa yanzu haka halin da ake ciki, tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi a zamanin da ke shugaban kasa.

Solomon Dalung ya ce dalilin da na sanin da Buhari ke yo, shi ne na yadda wasu makusantansa suka ingiza shi ya aikata abin da ya aikata da yanzu ba ya jin dadin abin.

Tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi - Solomon Dalung
Tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi – Solomon Dalung

Barr Dalung da ya yi minista a wa’adin farko na gwamnatin Buhari daga 2015-2019, ya ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na 2015.

A lokacin da ya ke tattaunawa da gidan rediyon Trust Radio, ya ce dole ya fadi gaskiya a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka yanke wa APC cibi.

Sai dai Solomon Dalung ya ce tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, da ya aminta da mutanen da ke kewaye da shi dari bisa dari. Sai dai yanzu haka Buhari na nadamar amincewa wadannan mutane da ya yi.

Kotu ta umurci sojoji su saki Salim Bazoum, da ga hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum

A wani Labarin na Daban : Kotu ta umurci sojoji su saki Salim Bazoum, da ga hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum

 

 

Kotun birnin Yamai (Tribunal de grande instance hors de Niamey) ta bada umarnin a saki Saleem Bazoum, da ga hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da sojojin da suka yi juyin mulkin ke cigaba da tsarewa tare da iyayen sa a cikin fadar shugaban kasa tun bayan juyin mulki

A kwanakin baya dai tsohon shugaban Najeriya Abubakar Abdusalami a wata zantawa da manema labarai bayan ganawa da hambararren shugaban na Nijar, ya ce Bazoum din ya nemi alfarmar sojojin na su bar dan nasa ya koma makaranta suka kiMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button