Tsananin talauci: wata uwar marayu saboda babu, kurar ruwa ta ke turawa


Tabbas a rayuwarnu ta yau da kullum idan kaji ko kagani yadda wani yake rayuwa a wannan lokaci kai idan kana da na ci ka godewa Allah , yanzu ka duba irin kima da martaba da a ga matar malam bahaushe ko in ce a Addini musulunci.
Amma kaga uwa mai ya’ya shidda wadda karfinta ya tafi wajen haihuwa amma itace ke jan kura domin ta samu na abinci tabbas muna cikin matsi da kuncin rayuwa wannan labarin daga shugaban kungiyar jinkai da tallafawa gajiyayyu da marayu, kuma mai baiwa Gwamna Shawara ta musamman a bangaren Fauziyya D Suleman ce ta wallafa wannan labarin a shafin ta na sada zumunta facebook .


Ga abinda take cewa.
“Lokacin da wani ya kirani ya ce mun akwai wata mata a unguwarsu kurar ruwa ta ke turawa ta samowa yaranta abunda za su ci abinci, ban yadda ba don haka na ce idan ya kara ganinta ya mun vedio ya turo mun, ai kuwa washegari ya ganota ya turo mun vedio dinnan.
Allah ya sani hankalina ya yi matukar tashi, Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, a cikin garin Kano ace mace na garuwa, gidan haya an tasheta a rakabe ra ke a wani guri, ba su da abinci yaranta marayu guda shida babu arabi balle boko, gashi ba ta da halin yin sana’a don babu jari don haka ta nemi kurar ruwa ta ke turawa su samu abunda za su ci abinci da yaranta.
Tabbas wannan tashin hankaline mai sosa zuciya, kuma wai a cikin garin Kano ba kauye ba, al’umma ku taimakawa baiwar Allah nan mu sake mata sanaa, mu kama mata haya mu saka yaranta a makaranta don Allah, babu kadan babu yawa ko dari ce da kai ka taimaka mata, kai koda tayamu yadawa ne har matar nan ta samu taimako shima sadaka ne.
Ga wanda za su taimakawa baiwar Allah nan da yaranta za su iya tura taimakonsu ta account dinmu.
Account no; 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Bank name: Access.
Ko
Account name: 6032459122
Account name; Fauziyya Danladi Sulaiman.
Bank name: Keystone.
Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya. 09128901099
Allah ya baku ikon taimakawa Amin.”.
Zaku iya kallon bidiyon matar tana turin kura a Nan.