Labarai

Tinubu ya dakatar da buɗe jami’o’i 37 da Buhari ya amince da kafa su

Gwamnatin Tarayya ta ce za a jinkirta buɗe sabbin jami’o’in da gwamnatin da ta shude ta amince da kafa su.

Ministan Ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a yau Laraba a Abuja.

Ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da bukatar samar da ingantattun shirye-shirye na ilimi ga wadannan jami’o’in.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da ba da lasisi ga sabbin jami’o’in 37 daf da karshen mulkinsa.

“Da yawa daga cikin sabbin jami’o’in da gwamnatin da ta shude ta amince da kafa su ne a ƙarshen mulki. Bayan an yi nazari da yawa, Shugaba Tinubu ya ga ya kamata a dakatar da bude su tukunna.

“Hakan ba wai na nufin za a soke jami’o’in ba ne, sai dai a duba su ta fuskar karfinsu da fa’idar da daliban za su samu.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button