Kannywood

Sai nayi da gaske nake samun yin sallah saboda korafe korafen mutane – Abba elmustapha

Shugaban Hukumar Tace Fina-finai na Jihar Kano, Abba El Mustapha yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARTB ya bayyana cewa, tun bayan zamansa shugaban wannan hukuma ta dab’i da adabi ta jihar Kano, akwai korafe-korafe da dama da yake samu daga mutane.

El Mustapha ya kara da cewar a wani lokacin hatta sallah sai ya yi da gaske yake samu ya yi domin mutane da yawa ne ke zuwa suna kawo korafe-korafensu a kan abubuwa daban-daban

Tun lokacin da na zama shugaban wannan hukuma, na dauki matakai da dama domin saita al’amura,hakan ya sa na kirkiro wasu dokoki da suka hada da sabunta rajista ga kowane dan fim a masana’antar Kannywood. jaridar Leadership hausa na ruwaito.

Na kuma bullo da shirin hana tallace-tallace marasa ma’ana da ke bata tarbiyar yaranmu, sannan na bullo da maganar cewar duka masu sana’ar downloading su tabbatar da sun sayi foster kafin su tura wa kwastomominsu fina-finai.

Wannan matakai da na dauka yasa mutane suka gane cewar da gaske muke yi a kan alkawarin da muka dauka wajen gyaran wannan hukuma ta ‘Kano Censorship Board’ da mai girma gwamna ya damka muna amanarta.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button