Labarai

Na tuba ina neman afuwar kashim shettima,Ganduje da Gawuna- inji Firdausi Yar Tiktok

Fiddausi yar Tiktok tayi wani faifan bidiyo ne inda take ikirarin zatayi jigidar bama-bamai inda take lissafo mutane da zata iya kunar bakin wake tun daga kan alkaliyar yar zuwa ga mai girma mataimakin shugaban kasar Kashim shettima da shugaban jam’iyyar Apc na kasa Dr. Abdullahi umar Ganduje da dan takarar gwamna jihar kano Dr.nasiru Yusuf gawuna wanda kotun sauraren kara ta tabbatar a matsayin wanda ya lashe zaben kano.

Na tuba ina neman afuwar kashim shettima,Ganduje da Gawuna- inji Firdausi Yar Tiktok
Na tuba ina neman afuwar kashim shettima,Ganduje da Gawuna- inji Firdausi Yar Tiktok

Firdausi yar tiktok yar kwankwasiyya ce abinda ya ja mata shine akan hukuncin kotu inda tayi bidiyo tana dura ashariya wanda nan take hukamar farin kaya Dss sunkayi dirar mikiya a gidansu amma dai ba’a samu bom ko daya ba, shine bana kiran mahaifiyar ta da yan uwanta an sako Firdausi.

Fidan rediyon Freedom Radio kano ya samu tattaunawa da Firdausi ga abinda take cewa:

Ni gaskiya kawai na fada ne amma banida alaka da bom rai nane ya ɓace dukan abunda na fada ina rokon tun daga mai girma mataimakin shugaban kasa da Dr. Abdullahi umar Ganduje da Dr. Nasiru Yusuf gawuna da dai duk wanda na taɓa a bidiyon Dan Allah yayi hakuri ya yafemin in sha allahu bazan kara ba.

Sa’a nan hukuma ma ina rokonta da tayi hakuri ta yafemin insha Allah wannan zai zamanto izina a gare ni.- inji Firdausi Yar Tiktok.

Itama mahaifiyar ta da yar uwarta da suka je karba ta sun bayyana godiya baza’a kara jin tace zata daura bam ba.

In sha Allahu zan sa ido sosai in gani bazata kara yi ba kuma na gode da jami’an tsaro Allah ya saka da musu da Alkhairi -inji mahaifiyarta.

“In sha Allahu bazata kara ba zamu tsaya sosai tsayin daka a kanta in Allah ya yarda wannan ya zamo izina a gareta Allah kuma ya karemu baki daya.”-inji yar uwartaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button