Labarai

Mu fa ba ‘yan ta’adda bane – Fulanin daji

Jaridar Dclhausa ta samu tattaunawa da wani fulani inda yake bayyana cewa bai dace ana yiwa fulani jam’i da yan ta’adda ba domin ba su kadai ne keyimin ta’addanci a cikin daji ba.

Ga abinda wnanan mutumin yake fadi:

“Sunana abdullahi Muhammad matsalolin da nake so in bayyana a jahohin mu na arewa bafulatani da bahaushe ƙabila daya ne kowa musulmi ne ya yadda da kalma shahada amma kowa ya buɗe baki sai yace fulani yan ta’adda ne, shin tana yiyuwa ace fulani kawai yake ta’addancin a jahohin mu na arewa.

Mu fa ba 'yan ta'adda bane - Fulanin daji
Mu fa ba ‘yan ta’adda bane – Fulanin daji

Ya dace idan za’ayi magana ace duk inda naka ga dan ta’adda na daji da cikin gari amma sai ace daji shidai adda yan ta’adda”.-inji abdullahi Muhammad

Minene damuwar ka na alakan tasu da wannan aika-aikar ?

“Abinda a damuwa ta yanzu idan ace a tafi maganin yan ta’adda ,waɗannan da ba yan ta’adda ba sune ake ta kashewa tsakanina da Allah yan ta’addan ba’a kashe su don miyasa ake mana haka nan.

Shin mu ba mutane bane , bamu da hakki da gwamnati ne , shin bamu da hakki ga talakawa ko yan uwan mu musulmai miyasa ake muna haka ne, ni abinda nake so na tambaya miyasa ake kashe mu kamar diyan awaki – inji Abdullahi

Abdullahi ya kara da cewa ya kamata gwamnati tayi bincike da ware wanda a na kwarai da wanda a mugu sai ayi musu wurin zama ace duk wanda yake na kwarai yaje can ya zauna, tunda duk yare akwai na kwarai akwai miyagu miyasa gwamnati bazatayi haka ba

Yanzu Abdullahi me kike so ka fadi abinda ya Dace?

” Ni yanzu abinda nake so gwamnati tayi mana gwamnati tace duk fulanin da a na kwarai ga wajen da ta keɓe ya nan y zauna dan Allah , koda gwamnati ta kama Fulani ta tsaya ta tantance shin wannan mai laifi ne ko marar laifi.

Idan anka tabbatar mai laifi ne laifinsa ya ja masa, idan bamai laifi bane a sake shi ya tafiyarsa yayi lalurar sa.- inji Abdullahi Muhammad.

Ga sautin murya tattaunawar su nan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button