Minista tace dandalin Rijistar Asusun Tallafi akan Talauci na karya ne – Dr. betta Edu


Dakta Betta Edu, ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, ta ja kunnen ‘yan Najeriya kan wani shafin yanar gizo da wasu bata gari suka kirkiro don damfarar ‘yan Najeriya.
Ta fadi hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Abuja cewa “shafin yanar gizo na bada wani asusun bada tallafi na gwamnatin tarayya na karya ne”, kuma bai fito daga ma’aikatar ko wata hukumar gwamnati ba.
“shafin da aka ce na bogi ne, wasu batagari ne suka kirkiro su da nufin damfarar jama’a da ba su ji ba gani.
“Ba za a taba samun wata kafa daga ma’aikatar ko ma’aikatu da hukumomin gwamnati ko kuma abokan huldar ta da za su nemi a samu kudade daga asusun tallafawa ayyukan jin kai da rage fatara ba.
Saboda haka, ake shawartar jama’a da su guji shiga irin wadannan shafuka.
A wani labari na daban: Dakarun Soji sun kama mutum 2 masu safarar makamai a Kaduna.
Dakarun rundunar sojin kasar nan na runduna ta daya 1 dake Kaduna sun samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargin masu safarar makamai ne ga ‘yan taadda tare da kwato babura 16 a Kaduna.
Mukaddashin daraktan sashen sadarwa na rundunar, Laftanar Kanar Musa Yahaya, shi ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa daya fitar a Kaduna, ranar Laraba.
Yayaha, ya bayyana an samu nasarar hakan ne bisa bayanan sirri da rundunar ta samu a ranar 24 ga watan Oktoba wanda ya kai ga kama ‘mutum biyu masu taimakawa ‘yan ta’adda da makamai’ a yankin Awon dake karamar hukumar Kachia ta jihar kaduna.
Ya bayyana cewa an kama mutanen a gidaje daban-daban a yankin na Awon kuma tuni suna hannun rundunar sojin domin bincike.