Kannywood

Mijina ne ya karfafin gwiwa na shiga harka fim -inji amina umar jaruma fataken dare

Jaruma Amina Umar wadda aka fi sani da Fatima a cikin wani sabon shiri mai dogon zango Fatake ta bayyana cewa ita matar aure ce har ma tana da yara.

Amina wadda ta bada takaitaccen tarihinta a yayin hira da tashar Freedom Radio Kano, ta ce ita haifaffiyar kasar Ghana ce amma iyayenta ‘yan asalin kasar Nijar ne kamar yadda hausa daily times ta fara majiyo mana

Mijina ne ya karfafin gwiwa na shiga harka fim -inji amina umar jaruma fataken dare
Jaruma amina tare da iyalanta

Ta ce tun a shekarar 2011 ta yi aure kuma Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu.

Mijina ne ya karfafin gwiwa na shiga harka fim -inji amina umar jaruma fataken dare
Iyalan jaruma amina

Kasancewa abu ne mai matukar wuya samun mace mai aure a masana’antar Kannywood ta Najeriya, Amina, ta ce da izinin mijinta take wannan sana’a hasali ma, shi ya rinka bata kwarin gwiwa tun kafin sana’ar ta shiga jikinta.

Da aka tambayeta yanda ta tsinci kanta cikin harkar fim, jarumar ta ce an je daukan shirin Fatake a kasar Ghana ne ta samu damar neman shiga cikin shirin bayan yin gwaji kuma sai Allah ya bata nasara.

A yanzu dai, ta ce karfin aikin ya dawo Najeriya, hakan ke sa lokaci zuwa lokaci takan bar iyalinta a Ghana zuwa Kano ko duk inda aiki a Najeriya kuma hakan bai canza komai tsakaninta da mijinta ba.

Wannan dai abu ne mai wahala samun mace jaruma wadde take da aure a masana’antar shirya fina-finan Hausa, wasu ma na ganin baya ga haramci a addini hakan ya saba al’adun Malam Bahaushe a Arewa.

Ga bidiyon nan.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button