Labarai

Malam ya cire tsoro : malam Murtala Assada yayiwa gwamnatin Sokoto wankin babban bargo akan matsalar tsaro a cikin bidiyo

Malam Murtala Bello Assada da ke jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya yayi maganganun sosai akan matsalar tsaro idan baku mance ba malam Murtala Bello Assada tun gwamnatin da ta shude yake caccakarta akan matsalar tsaro Sokoto.

A yanzu ma malam yace duk da sun goyawa jami’ar Apc baya taci zabe bazasu daina magana akan matsalar tsaro jihar Sokoto ba, inda yayi tsokaci ne akan kwamitin da anka nada na harka tsaron jihar Sokoto irin duba da yadda gwamnan katsina yayi Dr. Dikko radda yayi na daukar mutum 1,500 domin fafatawa da yan bindiga.

Inda anka basu horo tare da motoci da mashin da bindigogi shine shima gwamnan jihar Sokoto yayi koyi domin daukar irin wannan mutane domin a basu horo.

Amma sai dai a nan Sokoto abinda hausawa kance ja ya fado ja ya dauke ne domin tsohon Kwamishinan tsaro na jihar Sokoto lokaci gwamnatin da ta shude yana cikin wanda ake zargi wajen hada baki da yan bindiga inda har takai wasu fusatattun mutane a garinsu na isa ƙaramar hukumar isa sunka kone gidansa.

To shine yau mai girman gwamnan Jihar Sokoto kuma ya nada shugaban kwamitin daukar wadanda za’a baiwa horo da yakar yan bindiga, malam Murtala assada yayi maganganu da sakin bidiyon tonon sili akan wannan tsohon Kwamishina kanal moyi wanda kuma yanzu shine shugaban kwamitin gwamnati mai ci yanzu.

Shafin sheikh musa ayuba lukuwa  Sokoto na wallafa bidiyon a shafinsu na facebook

Ga bidiyon nan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button