Labarai

Labari mai dadi: Kayan da Buhari ya hana shihowa da su, Tinubu yace a shigo da su daga yau

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta Cire takunkumin shinkafa ta aminta ‘yan kasuwa su cigaba da shigo da wasu kayan mu’amullar yau da kullum har guda 43 ciki harda shinkafa wacce yanzu haka ake sayar da ita kan farashi Mai tsada

Babban bankin Nageriya CBN ne ya fitar da sanarwa a yau alhamis

Labari mai dadi: Kayan da Buhari ya hana shihowa da su, Tinubu yace a shigo da su daga yau
Labari mai dadi: Kayan da Buhari ya hana shihowa da su, Tinubu yace a shigo da su daga yau

Ga abubuwan kamar haka:

1. Shinkafa
2. Siminti
3. Magarin – (Botar Biredi)
4. Man Kwantirola
5. Man gyada
6. Man alayyahu da kayan lambu
7. Nama da naman da aka sarrafa
8. Kayan lambu da kayan lambun da aka sarrafa
9. Kaji da kayan kiwon kaji da aka sarrafa
10. Kifin gwangwani wata Geisha ko sardine
11. Shimfidadden karfe watau faleti
12. Dogon kwanon rufi
13. Gajeren kwanon rufi
14. Wilbaro
15. Kwanon sarki
16. Akwatunan ƙarfe da kwantenoni
17. Fadi ka mutu
18. Badujala
19. Fayif na karfe
20. Wayar rodi – lalatacce da wanda bai lalace ba
21. Rodi sitil
22. Rodi Bagobiri
23. Wayar raga
24. Kusa
25. Wayar tsaro da turakuna
26. Fatikus bodi
27. Faibod da faleti
28. Filawud
29. Ƙofofin katako
30. Tsinken sakace
31. Gilashi da kayan da aka yi da gilashi
32. Kayan kicin
33. Kayan hada tebur
34. Tayil
35. Silindar gas
36. Sakakkun yadudduka
37. Tufafi
38. Kayayyakin da akaa yi da roba
39. Kwayoyin roba watau Polypropylene
40. Ledar rufe alewa da jaka
41. Sabulu da kayan kwalliya
42. Tumatur/tumaturin gwangwani
43. Hannun jarin Yurobond/Bond na kudin kasashen waje/ko kuma hannun jarin kasar waje

An ce an hana bayar da canji akan wadannan abubuwa saboda kishin kasa, sai dai dukkansu babu abin da farashinsa bai ninka sau ninkin ba ninkin ba. Kuma babu abin da ingancinsa bai ragu ba sakamakon hana shi da aka yi. Ashe kenan ci gaban mai hakan rijiya aka yi, kuma kishin kasar na wofi ne.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button