Labarai

Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Kulla Auren Bogi Tsakanin Surukarsa da Buhari

Jihar Neja – Wata kotun majistare da ke zama a Minna, jihar Neja, ta yanke wa wani mutum mai suna Gambo Adamu hukuncin watanni 12 a gidan yari kan kulla auren bogi tsakanin surukarsa, Sa’adatu Aliyu da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wacce ke karar, wacce ta kasance bazawara, ta tunkari kotun cewa surukinta ya karbi kudade daga hannunta wanda ya kai naira miliyan 5 bisa alkawarin hada ta aure da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.

Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Kulla Auren Bogi Tsakanin Surukarsa da Buhari
Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Kulla Auren Bogi Tsakanin Surukarsa da Buhari

Yadda wani mutum ya gabatarwa surukarsa sadakin aurenta da Buhari
Ta fada ma kotun cewa surukinta ya gabatar mata da N100,000 a matsayin sadaki, da kwandon goro da soyayyiyar kaza a cikin wata jaka a matsayin kyauta daga Shugaban kasa Buhari a yayin daurin auren.

Majiyarmu ta samu daga legit ta bayyana cewa bayan zaman jiran ganin tsohon shugaban kasar ya zo daukarta a matsayin sabuwar amaryarsa, sai ta yanke shawarar tunkarar kotu domin ta shiga lamarin.

Matar ta kara da cewar mai laifin ya kuma bukace ta da ta kafa wata kungiya mai zaman kanta da ita a matsayin shugaba, yayin da shi surukin nata zai zamo kakakin kungiyar, inda ya yi mata alkawarin cewa za ta samu alfanu daga wajen gwamnatocin tarayya da na jiha.

Bugu da kari, ya sanar da ita cewar za ta samu kujerun aikin hajji.

Daily Trust ta kuma rahoto cewa alkalin kotun, Ibrahim Musa Zago, ya yankewa wanda ake karan hukuncin watanni 12 a gidan yari kan samunsa da laifin zamba wanda ya sabawa sashi na 322 na kundin laifuffuka, tare da zabin biyan tarar N100,000.

Ya kuma umarci wanda ake kara da ya biya mai karar kudi naira miliyan 2 a matsayin diyya.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button