Kisan gillar budurwar da aka sace a Zaria ya ɗimauta al’umma


Labarin sace budurwa da mata fyade bayan karba kudin fansa ya kashe ta abun ya tada hankalin mutane sosai irin yadda wannan mutum yayi rashin imani wanda Majiyarmu ta samu wannan rahoto daga shafin editan Liberty tv Ahmed Tijjani Ramalan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ga yadda ta tattara labarin.
Mutane a birnin Zariya sun auka cikin alhini da kaɗuwa kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wata budurwa ‘yar shekara 20, bayan an sace ta, sannan aka yi mata fyaɗe.


Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wani matashi ɗan shekara 27, lokacin da ya je karɓar cikon kuɗin fansa na marigayiya Fatima Adamu.
Suna zargin matashin ne da sace Fatima, sannan ya yi garkuwa da ita tsawon kwanaki, tare da karɓar kuɗin fansa, kafin ya halaka ta bayan ya yi mata fyade.
Tun farko, wani bidiyo ne da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna wani matashi tare da wasu mutane, lokacin da yake tonon wani abu da aka binne.
Bidiyon ya nuna matashin yana haƙar wani abu mai kama da kabari a cikin ɗaki kuma aka ji inda yake nuna wani sashe na ramin, yana cewa ga alamar hannu nan.
A cikin wani bidiyon kuma, an ji muryar wani mutum lokacin da yake umartar matashin, ya fito da marigayiyar daga cikin kabarin. Daga nan sai ya kamo sashen hannunta ya tashi gawar zaune. Har a lokacin hannunta na bankare ta baya, ga alama ɗaure da igiya.
Al’amari ne mai matukar tayar da hankali da dugunzuma zuciya.
‘Yan sanda sun yi zargin cewa matashin ya kashe Fatima Adamu ne ta hanyar amfani da muciya, lokacin da yake tunanin yadda zai yi da ita, kafin dawowar iyalinsa, da suka yi tafiya.
Ga bidiyon nan.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce tun da farko, matashin da ake zargi ya karɓi kuɗin fansa naira 120,000 daga hannun mahaifan Fatima.
Kuma daga bisani ya nemi su cika kuɗin da ya nema kafin ya sake ta.
Jama’a da yawa har a shafukan sada zumunta, na ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan irin tashin hankalin da suka shiga, sanadin wannan mugun labari.
Pharm Musa A. Bello a shafin Facebook ya ce hankalinsa ya tashi, zuciyarsa ta sosu, sannan yana cike da ɓacin rai.
A cewarsa, irin wadannan munanan ayyuka kaɗai sun isa jefa al’umma cikin halin ha’ula’i.
Allah ya kare mu da dukkan zuri’armu daga munanan ayyuka da sharrin mutane da aljanu, ya yi addu’a.