Labarai

Kare ma ya fi maroƙi amana : Barr. Bulama Bukarti yayiwa Rarara martani mai zafi

Fitaccen lauyan nan kuma mai sharhi akan harka tsaro da bincike lauya Audu Bulama Bukarti yayi tsokaci mai zafi akan maganar rarara da yayi jiya.

Inda yake cewa wannan ba abin mamaki bane ga maroki domin kuwa duk da ka yarda da shi sai yaci amanarka ga abinda yake cewa a shafinsa na sada zumunta.

Kare ma ya fi maroƙi amana : Barr. Bulama Bukarti yayiwa Rarara martani mai zafi
Kare ma ya fi maroƙi amana : Barr. Bulama Bukarti yayiwa Rarara martani mai zafi

Wai menene abin mamaki don maroƙi ya juya wa wanda ludayinsa ya bar kan dawo baya? Su fa dama ba don al-umma ko ma ƙaunar ƴan siyasa suke yi ba. A’a, don aljihunsa kaɗai suke yi. Iya kuɗinka, iya sha’aninka.

Da zarar zamaninka ya shuɗe, sai su tattare nasu ya nasu, su arce gurin na gaba. Dama can ya san cewa duk matsalolin da muka yi ta faɗa a kan Buhari gaskiya ne amma ya ƙi Allah saboda yana samu.

Duk kyawawa abubuwan da ya faɗa a kan Tinubu yanzu, ya faɗe su a baya a kan Buhari, kuma haka zai yiwa Tinubun ma idan ya dena samu. Kare ma ya fi maroƙi amana.”

Mutane sunyi martani sosai akan wannan magana.

@Musa hassan ibn Jaks cewa yake :

Tabbas hakan zai iya faruwa a kan Tinubu da sauran su…Amma inaga kaman soyayyar Rarara a zuciyan talakawa yazo karshe ne..wata kila talakawa zasu fara zeben mutane na gari ba wanda maroka suka musu talla ba.

@Yusuf Alhaji modu Babangida yana mai cewa :

Gaskiya ne barrister da yawayawan al umma ba kowabane ake gane haka sai abin yaru sai kaji ko ina yadauka, allah ya kyauta.

@moh’d Ghazali H Danja cewa yake :

Abin takaicin ma shine ko yanzu din ma bawai ya fusata akan halin da talaka ke ciki ba ne, dukkan alamu sun nuna takaicin sa akan rashin muqami ne da rashin damar ganin Tinubu kai tsaye

Naga ya koka akan yadda masu muqami ko ganeshi basayi sai-dai wani yayi musu describe dinsa yace… Na him sing dat song wey be Jagaba shine gaba.

@sani musa kademi cewa yake :

Ai duk abidda yaci Doma la shakka bai barin Awe, a baya in yana zagin wasu har lumshe Ido ake anajin dadin abidda yake, to ga shawara, yadda sauran Jagororin Siyasa da magoya bayan su sukayi hakuri suka jure cin mutuncin da yake musu, sabida Mulki ya kubuce musu ko kuma basa ra’ayin abidda yakeyi, suma mutanan Buhari sai subi wancan sahun da sauran magoya baya sukabi, a karshe Ina yiwa Buhari da magoya bayansa jajen sanya su da Rarara yai a shafinsa na rashin mutunci, kamar yadda ya saka sauran Jagorori da magoya bayan wasu Yan Siyasar.

@Bashir lamido Grz cewa yake :
Babu Butulu, Azzalumi,mugu Irin buhari har Kudi muka hadamashi Amma sbd Azzalumi ne ,yazo ya Rufe Muna border sbd border uwar Sace.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button