Labarai

Jama’a ku kawo min agaji, likitoci sun ce a datse min ƙafafu’ – Fitaccen ɗan fim, ‘Mista Ibu’

Fitaccen ɗan fim ɗin Nollywood, ko kuma finafinan kudu, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, a yanzu haka ya na kwance kan gadon asibiti, sai an kwantar, sai an tayar.

Ibu ko John Okafor ya fito ya roƙi duk mai hali kuma mai niyya ya taimaka masa da kuɗi kuma da addu’a.

A cikin wani saƙo mai cike da ban-tausayi da aka wallafa a shafin sa na Instagram, ya ce ce makonni biyu kenan da kwantar da shi a asibiti, “saboda wani ciwo mai hatsari da al’ajabi da ya same shi.”

Jama’a ku kawo min agaji, likitoci sun ce a datse min ƙafafu’ – Fitaccen ɗan fim, ‘Mista Ibu’
Jama’a ku kawo min agaji, likitoci sun ce a datse min ƙafafu’ – Fitaccen ɗan fim, ‘Mista Ibu’ Hoto/Facebook

Okafor mai shekaru 62 a duniya, ya ce likitocin sa sun bayar da shawara a datse masa ƙafafuwan sa biyu.

A cikin bidiyon da aka nuno shi a shafin Instagram, tare da matar sa da ‘yar sa, ya ce, “A yanzu ɗin nan da na ke magana da ku, abin da ya fi dacewa kawai idan har ba a samu wata hanya ba, to a datse ƙafafu na.

“Jama’a ku dube ni, idan aka datse min ƙafa daga nan ina zan tafi. Don Allah ku taya ni addu’a, ba na so a datse min ƙafafu na. Na gode, Allah ya saka maku da alheri.”

‘Yar da mai suna Jasmine Okafor ta tabbatar da rashin lafiyar mahaifin na ta, kuma ta nemi taimakon kuɗi domin su ɗauke shi zuwa asibiti a ƙasar waje.premium times hausa na ruwaito.

Ta ce yanzu haka su na wani asibiti ne a Legas, amma an ce za a maida shi wani asibiti, domin ba ya samun sauƙi.

Sun bada lambar Asusun Ajiyar Okafor, inda duk mai niyya zai tura masa taimako kamar haka:

“1685687982
John Ikechukwu Okafor
Access bankMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button