Kannywood

Iyayenmu na cikin masifa ba kadan ba – Adam a zango

Fitaccen jarumi kuka mawaki adam a zango yayi wani magana wanda ya karade shafukan sada zumunta inda tabbas ta dauki hankalin mutane.

Adam a zango ya fitar da wani rubutu wanda yake cewa yayi mafarki wanda akan masu amfani a kafar sada zumunta na tiktok inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a Instagram.

Ga abinda yake cewa :

Wallahi yau nayi mafarki akan tiktok ba zan fadi details ba.amma dai iyayenmu na cikin masifa ba kadan ba.

Nayi tsammanin ganin masu yin tiktok ta hanyar da bai dace ba a cikin azaba.

Adam a zango ya kara da cewa :

Iyayenmu na cikin masifa ba kadan ba  - Adam a zango
Iyayenmu na cikin masifa ba kadan ba – Adam a zango Hoto/Instagram: Adam a zango

“Sai naga iyayenmu ne a ciki ,ban san me Allah yake nufi da nuna min hakan ba.

Allah ya yafe mana ya bamu hanyar samun zallar halastacciyar arziki.” -inji adam a zango

Mutane sun yi martani akan wanan maganar sa a karkashin sashen martani.

@aytaheer yake cewa:

Inde har iyaye sunyi iya bakin qoqarinsu wajen bada tarbiyya toh laifin yayansu bazai shafe su ba dan laifi wani baya shafar wani a lahira sede anan dunia…Allah ya shiryemu ya kuma kyauta.

@ummu dufail gyran yana cewa :

Hhhhh to ai ko Ina ana iya sabo, har a cikin masallaci, kuma iyaye sunada commission na alkhairi ko akasinsa, Allah yasa mu dace.

@designaliy shots cewa suke :

@ummu_dufail_gyaran_jiki Trying to justify it or what? Wane sabo akeyi a masallaci? They are totally two different things. Tiktok platform ne dake kan internet. Abu na farko dake baki sani ba shine “the internet never forgets”. Once kika yi abu kika saka shi a internet wannan abun yana nan har abadah kuma zaici gaba da yaduwa. Ko da kinje kin goge, a copy of it it still there. Kuma idan abun da zai kawo miki zunubi ne, that means har abada zai cigaba da yin haka. Abu na biyu kuma shine, in kayi abu akan platform kamar Tiktok, kayi sharing, kana influencing duk wanda ya kallah ne. Haka yasa masu followers dayawa akan irin wadannan applications din ake kiran su da ” influencers”. Duk wanda post dinki yayi influencing, yaje yayi makamancin ko abunda yafi wannan, kina da commission na har abada. Iyaye da basu kare ‘ya’yansu ba (wanda kids are vulnerable), suma zasu samu kaso na abunda suka shuka. A masallaci kuwa duk Sabon da akayi, if yama kai girman na tiktok, yaduwar sa bazai kai na internet ba, tunda internet means “international Network”, world wide interconnection of people all around the world. Allah yasa mu dace.

@miss azeezah cewa take :

Ta wace hanya iyaye suke masifa Adamu? Idan har iyaye sun bada tarbiya yanda ya dace har yaro yakai munzalin hankali saiya zaba TikTok to babu ruwan iyayenshi a lamarin tsakanin shime da Allah zayayi bayani. Allah ya shirya masu yasa su gane gaskia, muda bamuyi Kuma ubangiji Allah ya qara tsare mana imanin mu.

@a_abubakarsuleiman cewa yake :

Mafarki Mai harcen damo ??? Mun Gane Inda Inda aka dosa, shi rayuwa mahakurci mawa daci, Allah ya shiryemu gaba dayammu, da “Yan TikTok da “Yan film, da makada, duk uwansu Daya ubansu Daya, Kai dai mu yaweta istigfari Allah ya sa mudace.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button