Labarai

Gwamnan Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya kaddamar da dakarun samar da tsaro mutum 1,500

Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD ya kaddamar da dakarun samar da tsaro na musamman na Jihar Katsina wato (Katsina Community Watch Corps) tare da muhimman kayan aiki domin dawo ta martabar tsaro a fadin jihar.

Kamar yadda Katsina Post na ruwaito an gudanar da bikin karramawar ne a babban filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin birnin Katsina ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, 2023.

Haka zalika bayan kaddamar da dakarun su 1,500, Gwamnan jihar ya kuma kaddamar da motoci masu sulke (Armored Personnel Carriers), motoci kirar Hilux guda 70 da kuma babura 700 domin yaki da ta’addanci a lungu da sako na jihar Katsina. Gwamnan Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya kaddamar da kadarun samar da tsaro mutum 1,500

Bikin kaddamarwar dai ya samu halartar fitattun mutane da shugabannin al’umma daga kowane bangare na Najeriya musamman ma a arewacin Najeriya.

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da Gwamnonin Arewa maso yammacin Najeriya dai suka hada da Kano, Kaduna, Jigawa, Zamfara, Sokoto da Kebbi duka sun halarci taron da kan su wasu kuma sun tura wakilci.Gwamnan Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya kaddamar da kadarun samar da tsaro mutum 1,500

Haka zalika sarakunan gargajiya na jihar Katsina da tsaffin Gwamnonin jihar duk sun halarci taron.

A jawabin sa, Gwamna Dikko Umar Radda ya hori matasan dakarun da su sa kwarewa da jarumta wajen gudanar da aikin su a garuruwan su domin ganin dawwamammen tsaro ya samu.

Dikko Radda ya kuma sha alwashin cewa daga bangaren gwamnati, za su cigaba da ba shirin dukkan goyon baya kamar yadda suka yi alkawari tun lokacin yakin neman zabe.Gwamnan Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya kaddamar da kadarun samar da tsaro mutum 1,500

Faretin ban girma da nuna jarumta daga bangaren dakarun na cikin abubuwan da suka wakana a wurin taron.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button