Fitattun jaruman masana’antar kannywood da sunkayi nuna alhini da jan kunne rashin tsaro a Najeriya


A Masana’atar Kannywood an samu fitattun jaruman masana’antar kannywood da sunka fito da kira ga Babban murna suna bakin cikin irin yadda ake kashe yan uwansu a arewacin najeriya.
Wannan abun ya faru ne daga jiya daya ga watan Oktoba inda sunka fara nuna bukatar su cikin takarda wanda zamu kawo muku wadanda sunka nuna wannan kira da babba murja.
1. Ali Nuhu shine jarumi na farko da ya fara bayyana irin rashin amincewa da ya nuna wai farin cikin samun yanci bayan ana kashe yan uwansa a arewaci tare da sace daliban jami’ar tarayya ta Gusau ga bainda yake cewa:
“Ya kamata masu alhakin tsaro a kasar nan su agaza wajen karbo yaran makarantar FUGUS. Su ma ya’ ya ne kuma suna cikin matsanancin hali sannan iyayensu da yan’uwa na cikin tashi hankali.”
2. Ado Isa Gwanja shine jarumi na biyu da ya nuna rashin amincewa da yayi murna samun yanci a dai-dai lokacin sata mutane da kashe mutane yayi yawa a arewacin najeriya ga abinda yake cewa:
“A dawo daliban mata da anka sace yan makarantar gwamnati tarayya a kawo karshen garkuwa da mutane da yan bindiga da ta’addanci a arewacin najeriya”.
3. Kabir sani international shine jarumi na ukku da ya nuna rashin amincewa da abubuwan da yake faruwa a arewacin najeriya ga abinda yake cewa.
“Arewa mu farka mu fita kwanmu da kwar-kwatamu domin nuna rashin amincewa da nuna kishin irin abubuwan da ya ke faruwa a arewacin najeriya.
A daina kashin yan uwan mu maza da mata a arewa a kawo karshin garkuwa da mutane.”
4. Nakowa comedy yana cikin jarumi na hudu da sunka nuna kishin arewa a cikin jaruman kannywood ga abinda yake cewa:
“Arewa mu farka musan inda yake muna cewa.,arewa na zuba”.
5. Ali Isa Jita shine na biyar wanda yake nuna rashin amincewa da abubuwan da suke faruwa na kashe mutane da garkuwa da mutane inda yake dauke da takarda har da iyalinsa an rubuta
“Arewa mu farka, A kawo karshen garkuwa da Mutane da a dawo da daliban makarantar Gwamnati tarayya ta gusau.
“Jini yana zuba a arewa, a dawo mana da dalibanmu”.